10

813 59 2
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 10




Abincin dare suka daura matar limam da aysha basu wani dade ba dan taliya ce da miya suka daura Bayan sun gama matar limam tace bari ta shiga ciki yau ta gaji fitan da sukayi, zainab tunda aka saka mata abincin take ta juyawa ta kasa ci, kana kallonta kasan ta fad'a duniyar tunani, zunguranta aysha tayi tare da fadin tunanin mai kike haka? Sai juya abinci kike?  Tashi tayi tare da fadin na koshi d'aki tayi da ido aysha ta bita,  koda ta shiga d'akin kwanciya tayi tana tunanin yazeed lokacin daya dago mata hannu da sanda ya sakar mata murmushi, ido ta lumshe na wajan minti d'aya sannan ta tashi ta dauko wayar daya bata, ciro wayar tayi a kwali tana kallo tare da jujjuyata jin kaman motsin mutum zai shigo yasa tai saurin boye wayar cikin jakarta, matar limam ce ta shigo dauke da abincin data ki ci, tace haba zainab mai kika ci da zaki ce kin koshi maza amsa kici, amsa tayi dan bazata iya musu da matar limam ba, matar limam tai ta dan janta da fira suna firan tana ci kuma taci da yawa, aysha ita ta shigo suka Dan taba firan matar limam tayi musu saida safe, Bayan fitar matar limam aysha tace uhm nikam zainab naga duk kin canza kodai..... Da sauri zainab tace kodai me? Dariya aysha tayi tace bazan fad'a ba amma zan zuba ido inga ikon Allah, zainab tace Hmmm tare da juyawa ta kwanta, ita da kanta ta rasa mai yake damunta yanda take ji yanzu bata taba jin irin haka ba.



Washe gari tun wajan karfe 8 da wani abu suka gama komai dan da wuri suke son tafiya, limam suke jira ya dawo dan ya fita yace su jirashi, suna zaune suna fira har wajan goma saura saiga limam yayi sallama, amsawa sukayi dukansu suka mishi sannu da zuwa, limam yace kuyi hakuri naje siyo muku gurasa ne, gashi anyi Sa'a gashin yau ne, zainab tace lah aiko an bamu gurasa jiya da muka Fita, yace eh na gani bata da yawa, godiya suka mishi, yace Wlh ban so ku tafi d'an zaman nan da mukayi naji mun Saba Sosai, matar limam ta cafke da fadin Wlh koni zanyi kewarsu, zainab tace inye ashe dai ana son wannan amaren, dariya sukayi su duka, tashi sukayi tare da dauko akwatinsu, limam ya rakasu har tasha suka shiga mota saida motar ta tashi ya bar tashan.



Amina da mama da yasmin ne zaune a falo hindu ta fito tana nuna ma amina wani riga data siya tace amina kalla ki gani tayi kyau kuwa?  Amina tace eh babu laifi, ummi ta fito dauke da meat pie a tray ta ajiye akan center table tare da daukan plate tasa ma mama ta mi'ka mata, mama tace sannu da aiki tare da amsa, hindu ta kalli ummi tace ummi kalla ki gani rigan nan tayi kyau kuwa?  Ummi tace yayi kyau Sosai..... Shigowan su zainab yasa ummi yin shuru da sauri aysha ta fad'a jikin ummi tana fadin kai nayi kewarki ummi na, ummi tayi dariya tare da fadin nima haka ya hanya?  Aysha ta amsa da lafiya zainab itama ta fad'a jikin ummi tare da fadin ummi na, dariya ummi tayi cikin son yaran nata tace Sannunku da zuwa, gaida mutanan falon sukayi hindu tace Ina tsaraba zainab ta mi'ka mata katuwar ledan gurasa, hindu ta amsa tare da budewa tace wow gurasa ta kwadama ma khairat kira wacce ta fito da sauri ita da zarah dan sunji hayaniyar yan uwansu, rungume juna sukayi suna dariya, hindu tace khairat in kun gama murnan ki hadamin wannan gurasan yau shi zanci da daddare khairat tace toh,  faruk ne ya shigo gidan nufan su zainab yayi yana fadin saukar yaushe?  Aysha tace yanzu muka dawo yace Kun dawo lafiya? Suka amsa da lafiya, ya kalli zainab yace sis mai kuka kawo min? Dariya zainab tayi tare da kamo hannunshi ta zaunar dashi, ta nufi inda ledan gurasa yake ta dauko guda biyu ta nufeshi tura mishi tayi a baki yana fadin a'ah Na koshi amma ina tura mai take ganin haka yasa ya tashi ya haura sama da gudu sai dariya suke ta musu, duk wannan drama din akan idon Alh Ibrahim ake yinta dan tare da faruk suka dawo, ummi ce ta Lura dashi tace sannu da zuwa, bayan duka suka waiga ganin mahaifinsune yasa duka suka tamke fuska tare dayi mishi sannu da zuwa ga mamakinsu saiya amsa tare da fadin kun dawo lfya? Kallon mamaki suke mishi saida ummi tace baku ji ana tambaya bane? Aysha tace lfya Abba, sannan sukai ciki suna mamakin nuna kulawanshi a kansu, suna shiga ciki khairat ta matsa kusa da aysha tace anzo neman aureki fah Abba ya kuma amince, ido aysha ta zaro tare da fadin ban San wasa, dariya zarah dake gefe tayi tare da fadin dagaske ne, Abba yace Idan kuka dawo saiku hadu keda shi in kun fahimci juna shikenan, uhm kawai tace ita kam zainab sai dariya take tayi alaman jin dadi yar uwarta zatai aure, aysha ce tayi ajiyan zuciya tare da fadin zarah matso kiji duka suka matso sukai magana, zarah tayi dariya tare da fadin zamu gwada hannunta ta ajiye aysha ta daura nata akai zainab ma ta daura khairat tasa nata tare da fadin zamu nuna ma Abba Muma y'ay'a ne, dariya sukayi tare da rungume junansu.



Da daddare kowa Ya hallara akan dinning wajan cin abinci, ummi kaman kullum saida tasa ma Abba yayin da su zarah suke zubama junansu, suna cikin cin abinci zainab tace Abba, dagowa yayi ya kalleta tace Abba Muma muna son mu fara zuwa office, kallonta yayi da sauri Kafin yayi magana aysha tace Abba Muma munyi karatu sannan duk abu d'aya ake koyawa sai dai Inba course dinku daya da mutum ba, Muma muna son mu tallafa maka, khairat tace Abba akan zaman gidan da mukeyi gwara muje Muma mu bada Tamu gudun mawar, zarah tayi caraf tace Abba ka bamu dama domin Kaga irin Tamu baiwar kowa dake wajan kallonsu yake yana son jin mai Alh Ibrahim zaice........  Hmmm ku biyoni muji ko Alh Ibrahim zai yarda da wannan maganan ta yaran nasa mata......  Yawan comment yawan typing....






    *vote*
*comments nd share*

*maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now