21

569 47 0
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 22




Koda suka isa gidan, kowa yana ta dubawa amma basu gani ba sai bude bude suke amma shuru, duk wani inda takarda take sun duba amma shuru babu shi, zarah tace Kai Wlh na gaji wannan takardan bata gidan nan, zainab dai bata ce komai ba sai dubawa take, komawa falo tayi inda ta Fara duba kujeru Tana d'aga 2seater saiga wata takarda ta fad'o d'auka tayi ta bude ta Fara karantawa kuka ta saki mai karfi wanda yasa yan uwan nata fitowa da sauri Abubakar ne ya amshi takardan ya fara karantawa kaman haka *yazeed rayuwanka Tana cikin hatsari domin naji saleh yana waya zai kashe ka Dan haka ka kula sannan ka tabbatar ka fad'ama Alh Ibrahim abunda suka boye mishi tsawon shekaru masu yawa dan Allah kayi kokari ka fad'a ko na sami salama* khairat tace saleh shine ya kashe yazeed kenan? Sannan mai ake son a fad'ama Abba? Zainab tunanin wayan da sukai da yazeed ta farayi Kafin ya rasu, lallai gaskiya police ne kashe yazeed akayi kuma saleh shine ya kashe mata fita tayi tare da fadin kuzo muje Gida, binta sukai a baya zarah saida ta rufe window din sannan suka nufi Gida.


Koda suka karasa gida motar police suka gani, alamun police sun zo, da sauri suka karasa, dai dai lokacin da police din yake fadin saleh shine ya bige yazeed mun kama mai motar ya shaida mana ya bama saleh hayar motar ne inda ya bige yazeed din sannan yaba mai motar kudi mai yawa, kowa dake wajan Ya girgiza musamman amina domin ita zufa yake ta keto mata, police din yace muna bukatar matarka ta kirashi inda zaifi mana saukin kamashi, tunda y'ar Uwar shice, kallon Amina yayi da idonta ya ciko da kwalla ga kuma tsoro yace Amina kirashi, bata musa ba dan Kar Ayi zargin wani abu kiranshi tayi tasa speaker tace kana Ina inzo? Fad'a mata inda yake yayi tace gani nan tare da fad'in kizo min da kudi dan banda kudi a wajena Sosai tace toh tare da kashe wayan.



Bayan Amina sun had'u da saleh police dasu Alh Ibrahim dake binta a baya suka fito, nan aka kama saleh, kallon Amina yayi yace ni kika cuta kika ci amana ta duk rufa miki asiri da nayi, Nayi kisan Kai saboda in boyema duniya da mijinka cewa faruk ba d'anki bane d'a nane ke mace kika haifa Amina tana ta girgiza mai kai alaman yayi shuru amma shi ina fad'a yake kin cuceni tare da fad'in mace kika haifa faruk d'ana ne, alh Ibrahim da gaba d'aya wutar lantarkin dake kanshi ya dauke duk wata jijiya dake jikinsa ya tsaya dan tsabagen kaduwa, police sukai gaba da saleh Abubakar ya kama Alh Ibrahim suka koma Gida wanda inda za'a gwada jininsa zai Kai d'ari biyar dan Tashin hankali, suna shiga ya zauna a kujeran falo yana fad'ama mama abunda Amina da saleh sukayi faruk kam babu abunda yake sai kuka da ba'kin cikin abunda saleh ya aikata tare da takaicin shine ubanshi Wanda yayi sanadin mutuwar mijin yayarshi, Amina ce ta shigo falon Alh Ibrahim ya tashi cikin zafin nama tare da fad'in Amina kin cuceni Allah ya isa tsakani na dake, dan haka ki fita ki bar min gidana yanzu bana bukatar in sake ganinki sannan ki kawo min y'ata duk inda take, ummi tace babu inda Amina zata kowa waigowa yayi yana kallon ummi cikin mamaki taci gaba da fadin Amina bata da laifi kaine mai laifi kaida mama da kuka nuna kuna son d'a namiji kowa yasan da wannan burin naka, bako wace mace bace zata iya jure ba'kin cikin dani na kunsa ba wajan shekaru ishirin da wani abu ba, saboda na haifi y'ay'a mata, ganin yanda ake min a gidan nan da nuna min dani da babu duk d'aya ne dole yasa Amina ta boye abunda ta haifa tunda inka gani ba zaka amshi kaddara ba , shin MIYE ILLAR Y'AY'A MATA da yasa baka son su? Yanzu gashi Allah ya nuna maka baka isa ba gaba d'aya yaranka mata ne bai baka namiji ko guda d'aya ba, alh Ibrahim yace hakane Allah ya nuna min iyakata lallai na aikata babban laifi kubra ko hakkin ki dana danne na matsayin matata Allah bazai barni ba, ina miki hukunci akan abunda bake kike bama kanki ba sannan ina nuna butulci akan abunda Allah Ya bani, mai makon in gode mishi sai na tsaya zaba, wanda wasu suna nan basu taba haiyuwa ba amma ni Allah ya bani Ina butulci, kubra dan Allah ki yafe min duk da Nasan ba abu bane mai sauki ki yafe min amma.....  Tace ban taba ri'keka ba duk abunda kamin na yafe maka duniya da lahira, godiya yaita mata tare da kallon Amina yace zaki zauna ne saboda kubra yana fadin haka ya haura sama, Amina ta matsa kusa da zainab dan tayi mata magana zainab na ganin ta matso tabar wajan domin babu komai cikin ran zainab sai tsananta, kowa Ya watse a falon, Aneesa da magajiya suna zaune suna tattaunawa akan maganan Aneesa tace yanzu amina itama zata zama Abun tausayi, gidan zai koma hannun ummi, magajiya tace nidai burina mu zauna a nan har abada, aneesa tace uhm karki damu gidan zai zama nawa bada dadewa ba, magajiya tace taya Bayan faruk ba d'ansa bane, aneesa tace zaki gani Kedai kawai ki zuba min ido tunda yanzu Ya gano ba d'ansa bane zai dinga jin tausayin shi Sosai....  Koda yake Kedai magajiya kisa ido kiyi kallo.



Ummi tana d'aki tana taba Alh Ibrahim baki akan yayi hakuri, yace bazai taba samun nutsuwa ba har sai yaga y'arsa, Amina ta shigo hannunta dauke da hoto, yana ganinta yace maiya kawo ta d'akin shi? Tace kayi hakuri na kawo maka hotan yarinyarka ne, da sauri ya amsa tare da fadin tana Ina yanzu Nima ban sani ba amma saleh yace min Tana tafa wajan wata mata yace ana kula da ita Sosai ummi tace yanzu abunda ya kamata sai kaje prison ka sami saleh ya fad'a maka yace hakane yanzu kam zani ma.....  Hmm toh fah shin saleh zai fad'a mishi kuwa? Muje zuwa






     *vote*
*comments nd share*

*maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now