29

532 43 1
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 30




Iyalan Alh Ibrahim ne zaune sunyi jigum domin har yanzu bai dawo gida ba, gashi number dinshi Anata kira anki dauka wasa wasa har dare ya farayi hankalin kowa ya tashi domin baya Kai irin wannan lokacin a zaune, Abubakar ne yace bari yaje ya Sanar da police yanda ake ciki, hakan ko akayi suka tafi harda zarah da khairat,koda ya Sanar ma police sunce za suyi bincike duk yanda ake ciki zasu jisu, hakan koh akayi, suka dawo gida, wasa wasa har gari ya Waye shuru babu alh Ibrahim babu labarinshi faruk kam tunda Aneesa taja shi sukai gidanta duk ya tsorata musamman da tace shine ya kashe mahaifinshi, amma daka baya ta Fara kwantar Mai da hankali tare da fad'in ita Tana sonshi zata rufa Mai asiri, sannan tace Mai dad'i ya kamata kaji tunda Alh Ibrahim ya mallaka maka duka dukiyarsa Kaga yanzu komai naka ne tunda Nasan ya dade da tafiya rami yanzu, haka taita fad'a Mai magana wanda yasa yaji d'an sanyi sanyi harya bashi karfin giwan komawa gida, kuma koda yaje har lokacin ba'a ga alh Ibrahim ba.



Washe gari da sassafe police suka zo gidan, da mummunan labari, domin sun tsinci gawan alh Ibrahim a kasan gada, wanda suka tabbata daya fad'o ne akan gadan, gaba d'aya iyalan gidan kowa Ya girgiza da sukaji alh Ibrahim ya rasu, mama fad'i take mutuwa mai yasa zaki min haka ni ya kamata ki d'auka ba d'ana ba haba mutuwa mai yasa kika Fara daukanshi lokaci d'aya kuma ta saki kuka, police sunyi bincike akan gawan alh Ibrahim inda suka mi'ka musu gawan Bayan sun gama aka mishi wanka aka kaishi gidansa na gaskiya, tunda aka Sanar da Labarin mutuwar alh Ibrahim Aneesa da magajiya suka dawo gidan da zama da Sunan sun zo gaisuwa, da yake mutuwar na cinsu babu wanda ya iya magana dan mutuwar mahaifinsu yafi komai d'aga musu hankali, faruk kam kaman yafi kowa shiga damuwa, police sun dawo sunce alh Ibrahim ba fadawa yayi da kansa ba, amma za suyi bincike, faruk yace miye amfanin binciken tunda wanda ya mutu ba dawowa zaiyi ba, mama tace hakane koma Waye ya aikata sun barshi da Allah, haka akaita zaman makoki, ranan da alh Ibrahim yayi kwana bakwai da rasuwa aka tara duka iyalanshi domin barrister dinshi yazo ya fad'a abubuwan daya bayar ga magada, kowa ya hallara a falon ciki harda su Aneesa, inda barrister ya fara magana kaman haka alh Ibrahim ya mallaki dukiya kadarori company da gidanshi da yake ciki, alh Ibrahim yace inya mutu a raba madaran kud'i daya Bari kashi biyar aba hindu kashi d'aya mama kashi d'aya hindu kuka ta Fara Sosai tare dayi ma d'an uwanta addu'a faruk da Aneesa kuma suna zaune suna son jin na faruk din sai murmushi sukeyi, barrister yaci gaba da fad'in sannan aba amina kashi d'aya, kashi d'aya aba ummi itama, kashi d'ayan kuma daya rage a raba shi kashi biyu d'aya yaranshi mata su raba su biyar d'ayan kashin kuma Abubakar mijin zarah ya d'auka, sannan company dinshi da gidansa faruk wani irin murmushi ya sake amma Jin barrister yace ya mallaka ma y'ay'anshi mata Su biyar yasa faruk da Aneesa mamaki, zarah tace barrister Anya ka duba dakyau kuwa? Sunan faruk ya kamata ya zauna a wajan ba namu ba, barrister yace dai dai na duba abunda mahaifinku ya fad'a Shina rubuta, zainab tace bamu yarda da wannan rabon ba dole a bama faruk, barrister yace koda Kun yarda koda baku yarda ba babu abunda zaku iya domin koda kunce kuna son a muku rabon gado faruk bashi da gado dan haka gwara Kubar abunda mahaifinku ya baku zaifi, shuru sukai su duka barrister yayi musu sallama ya tafi, faruk tashi yayi ya nufi d'aki, yana shiga ya saki kuka, dama na sani karya kake min baka sona ka tsaneni baka kaunata alh Ibrahim Ka nuna niba d'anka bane kuka yake Sosai kaman ranshi zai fita Amina da tun Tashin shi ta biyoshi duk taji abunda yake fad'a hakuri ta Fara bashi akan alh yana sonshi ya dauka kaman shike da dukiyar nan tunda su zarah sun daukeshi matsayin d'an uwa, haka taita bashi baki amma shi ina bama jinta yake ba.



Yau akai kwana arba'in din alh Ibrahim, faruk ne ya fito cikin riga da wando, zarah ta kalleshi tace office dinfa? Yace zarah daka yau Na daina zuwa office, Ummi tace akan wani dalili? Yace Ummi Abba ya barma su zarah company din nan, yana son su kula dashi da kansu sai yasa ya basu, naga gwara in bar musu, zainab tace faruk dan Abba ya bar mana company din nan bawai yana nufin mu zamu dinga zuwa ba, faruk yace tunda har Abba ya baku yana son kuje tunda yanzu baya nan Waye zai zauna matsayin shi kunga dole sai ku, zarah tayi murmushi tace shikenan munji zamu amma harda Kai dan haka sai kaje ka shirya domin kasan bamu San komai ba dole sai an tayamu zaiyi magana zarah tace Ashhhhh ya isa haka maza Jeka shirya, badan yaso ba Ya shirya suka tafi su duka matan dashi da Abubakar, suna zuwa company din ma'aikatan wajan suka taso cikin girmamawa suna taya su murnan Fara zuwa office, koda suka shiga office din mahaifinsu jikinsu yayi sanyi musamman da suka ga tankamemen hotan mahaifinsu, zainab ta Fara hawaye tare da fad'in Abba zamu ri'ke wannan company din da kyau ta yanda koda kana Raye za kayi alfahari, faruk yace Indai suna son ya dinga zuwa shima zai shiga cikin Sahun ma'aikata dai dai da kwalinsa hakan ko akayi aka bashi office din da bai Kai nashi ba, wata rana faruk yana ma wani ma'aikaci magana akan Mai yasa kullum yake zuwa lati nan ya fara gayama faruk magana ina ruwanka in nazo late kaima fa yanzu yanda nake haka kaima kake dan haka ka fita cikin hanyata, zarah na jinsu, sai taji faruk din ya bata tausayi, gashi ran nan da tazo wucewa taji wasu ma'aikata na gulma akan yanzu mata ne ke shugabantan company din ba lallai bane su iya abunda namiji zaiyi ba, wanda tasan gaskiya suka fad'a dan aysha ta kusa komawa gidanta kuma sauran kannen nata aure za suyi bata san ko wani gari za'a kaisu ba lallai ya kamata a matsayinta na babba ta kula da company din dakyau.




Faruk yanzu Ya rage magana in suna falo baya zama, Amina abun na damunta Sosai, dan haka ta yanke wani hukunci ba tare da shawaran kowa ba, su zarah na zaune cikin d'akin khairat suna fira Amina ta shigo ta samesu, zama tayi itama tace firan Mai akeyi haka? Aysha tace muna firan Abba ne rayuwa kenan, Amina tace nikam da zaku yarda da kunba faruk komai ya dinga kula dashi inaga hakan zaifi, zarah tace na fad'a mishi haka amma yaki yarda, Amina tace gaskiya ne bazai yarda ba inda zakuyi signing ku dawo mishi da komai ya zama nashi inaga zai yarda sannan zaku sami kulawa kaman mahaifinku na Raye, rahma tace mum gaskiya hKan bamai yihuwa bane, Amina tace saboda me? Faruk yaja jikinshi daku da kuma kowa saboda yaga mahaifinku bai Bashi  komai ba, Kuma ana gobe alh Ibrahim zai rasu yace yaba faruk duka dukiyarsa kunga inda bashi da niya bazai fad'a ba, zarah tace hakane zamu bashi komai ya kula dashi tashi tayi Jim kad'an sai gata da takarda da Biro tace ni nayi signing ko wacce tayi na amince da abunda Anty Amina ta fad'a, ta mi'ka ma kannen nata ko wacce tayi signing wanda dakyar rahma tayi........  Ku biyoni yanzu Wasan ya fara ga dai dukiya ta dawo hannun faruk koya za'a kaya?







     *vote*
*comment nd share*

*Maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt