20

597 42 2
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 21




Haka aka Kai yazeed gidanshi na gaskiya, mutane nata zuwa musu gaisuwa, zainab ta koma Abun tausayi lokaci kad'an, Dr din data amshi haiyuwar faruk da saleh ya kama wasu yara suna buga kwallo suka jefa gidan saman wani yaro yaje daukowa yaga tsohuwar daka shiganshi ta kirashi tare da bashi takarda tace yakai mata gidan su yazeed tare da kwatantamai, yaron Ya tafi a lokacin su zainab duk sun koma gidan mum din yazeed ana amsar gaisuwa, koda yaron yaje gidan ya rasa wa zaiba takardan can ya hango ummi ya bata yace gashi Wai a bama yazeed, ummi ta amsa Tana hawaye zama tayi zata bude dai dai lokacin Alh Ibrahim ya kirata ajiye takardan tayi ta tafi wajan mijin nata koda taje yace zainab ta samu taci wani abu kuwa? Tace a'a babu yanda Banyi ba amma taki ci, alh Ibrahim cikin jin tausayin y'ar tashi yace ki kara gwadawa Kar a barta da yunwa ummi tace toh Bari inje in sameta.


Koda saleh ya koma gidan da yake yaje da nufin kashe tsohuwar shake mata wuya yayi ta Fara fadin ka kashe ni babu komai domin ko yanzu na mutu zanyi farin ciki domin nasan yazeed zai fad'a Dan na tura mishi message akan kana son kashe shi dan haka babu damuwa kuma yaji komai zai fadama Alh Ibrahim, saleh najin haka Ya saketa tare da wanka mata Mari yace bazan kasheki ba sai na nemo letter din zan kashe ki Shegiyar tsohuwa Yana fadin haka Ya fita, kiran Amina yayi ta tashi ta fita da sauri ta dauka yace amina wannan Shegiyar Dr din ta rubuta letter tasa a kawo ma yazeed bata san Ya mutu ba, dan haka kisan yanda letter din yake Kar wani ya gani domin ta rubuta komai a ciki, amina tace ka gani koh saleh yanzu miye Abun yi? Yace ki nutsu ki duba abunda nace kawai tace toh, koda su alh Ibrahim zasu tafi ummi tace zata zauna da mum din yazeed da zainab a gidan, Amina tayi caraf tace a'a ita zata zauna dasu ummi ta koma Gida, ummi taji dadin karan da amina tayi dan haka suka tafi, cikin dare Bayan kowa Ya kwanta, amina ta fito falo tana haskawa da waya ko zata ga letter din, kunna wutan falon akayi cikin tsoro ta waiga taga zainab ce, amina ta Fara in ina tare da fadin nazo insha ruwa ne, muje nama sha, komawa sukai ciki, Amina kasa bacci tayi sai juyi take tayi, kwanan su uku a gidan amina na neman letter din amma bata gani ba, zainab na zaune rungume da hotan yazeed tana kallo tare da kuka, mum din yazeed ta shigo cikin tausayin zainab din ta zauna kusa da ita tare da janyota jikinta tana fadin kiyi hakuri zainab addu'a  za muyi ta mishi domin shi yafi bukata sannan addu'a itace babban gata da zamu nuna masa kiyi hakuri Kinji? Kai ta d'aga alaman eh cikin kuka tace mum Kafin yazeed ya rasu akwai abunda yake son fad'a min, mum dinshi tayi caraf tace Nima ya kirani ranan da yayi hatsari yake fadamin akwai matsala a gidanku muna cikin maganan wayan ya yanke naita nemanshi ban samu ba kuma yanda naji yana maganan a tsorace yake, toh ban dai San miye matsalan ba na Fad'a miki hakan ne dan nasan Kema kiran da yake ta miki kenan, yana son fad'a miki,mum ta canza maganan da fadin ki shirya kayanki yau zaki koma gidanku, da sauri zainab ta kalli mum din tare da fadin mum bazan koma ba tare zamu zauna ni dake.....  Maganan ummi suka ji wacce take fadin zainab hakuri za kiyi kizo mu taf zainab tace ummi bazan iya tafiya inbar mum ta zauna ita d'aya ba a wannan gidan, mum tace zainab Nima yau zan tafi kano wajan yan uwana bazan Zauna ba dama saboda yazeed nake zaman kaduna yanzu baya nan zaman mai zanyi? Zainab Kuka take akan Kar mum ta tafi amma mum tace bazata iya zaman gidan ba domin zai dinga tuna mata yazeed Sosai, haka suka shirya gaba daya suka tafi, Amina taji dadin hakan domin tasan babu Mai ganin letter din yanzu tunda an rufe gidan, saleh ta doka ma kira yana dauka yace Anga letter din? Tace a'a amma an rufe gidan kowa yabar gidan, ajiyan zuciya yayi tare da fadin yanzu hankali na ya kwanta yau zan koma in kashe wannan tsohuwar likitan, yana fadin haka ya kashe wayan, gidan ya nufa direct Wanda rabon shi da gidan kwana biyu kenan, yana shiga yaga baiga tsohuwar ba duba wajan yayi duka bai ganta ba, fita yayi yaje gidanta Wanda Ya satota shekara ishirin da wani abu, koda yaje ya Tarar da gidan a kulle wata mata ya gani kusa da gidan tana wanki yace dan Allah mai wannan gidan fah? Tace an saceta jiya ta dawo kuma a jiyan Allah yayi mata rasuwa, yace Innalillahi'wa inna'ilaihira jiun,  tare da goge hawaye yace Kai rayuwa kenan Allah yaji qanta matar ta amsa da Ameen sannan ta tashi tayi ciki, matar na barin wajan yayi wata Shegiyar murmushi tare da fadin kin hutar sheni daukan zunubi ban kashe kiba kin mutu da kanki, yanzu babu wani mai tauna asiri kuma tunda wanda suka San Abun sun mutu yanzu daka ni sai Amina.


Koda zainab ta koma Gida tunanin maganan da mum din yazeed ta mata take tayi, itama in bata manta ba sanda suke waya taji kaman a tsorace yake yanda yake magana 'kasa 'kasa, khairat ce ta kirata akan tazo police din da suke bincike akan mutuwar yazeed sunzo domin suna son sanin Wanda ya bigeshi mai yasa ya gudu, koda tazo falo police din yana fadama Alh Ibrahim sun gano number din motar amma basu San inda zasu ga mai motar ba suna dai kan bincike ne sannan hatsarin daya faru bigeshi akayi da gangan, zainab ta girgiza Sosai, dan haka ta shige d'aki ta dauko hotan yazeed, d'akin zarah ta nufa akan suzo su rakata wajan da yazeed yayi hatsari zarah bata musa ba dan a halin yanzu suna matukar tausayinta fita sukayi su duka matan, harda Abubakar mijin zarah shine yake tuka su, koda suka je wajan nuna ma mutane hotan yazeed zainab take tayi wai ko sun sanshi amma kowa sai yace a'a har zasu wuce taje wajan yaran da suke buga kwallo ta kamo hannun wani yaro tace ka taba ganin wannan? Yace a'a yaron yace Anty yana da kyau Ya sunanshi koda na ganshi d'an murmushin takaici tayi tace yazeed tare da barin wajan yaron shuru yayi yana tunani yazeed kaman na taba jin Sunan har zata shiga mota yaron yace Anty zainab ta waigo yazo wajanta da gudu yace kwana uku da suka wuce wata tsohuwa ta bani letter in Kai ma yazeed naje gidansu nakai naga mutane da yawa, zainab tace letter? Ina tsohuwar data baka? Yaron yace ta rasu, zainab tace ngd, mota ta shiga tace zarah muje gidan su yazeed mu duba letter din Abubakar yace kina tunanin zamu gani? Tace eh zamu iya gani, zarah tace toh amma gidan ai a rufe yake, zainab tace zamu iya shiga ta window baya muje kawai.....  Hmm toh muje zuwa muga ko za suga letter din sannan miye tsohuwar nan ta rubuta a ciki  duk ku biyo ni......






     *vote*
*comments nd share*

*Maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now