FORTY NINE

1.5K 171 4
                                    


🏵🏵🌸🏵🏵
       _RAYUWARMU A YAU!_
                      *FORTY NINE*
🏵🏵🌸🏵🏵

✍🏻AMMIN SU'AD
  
Shatuuu095@wattpad.....shower me with your votes and comments I'll love that, show me some love and spoil me a little..... ILYSM!

Washegari da asuba da muka tashi, Baki daya kunyar kallon Farouq din nake, inajin Yana tashi na amma naki tashi se kawai ya fice Don har an shiga sallah, Inajin ya fita na Mike zuwa toilet, komai very neat sannan nayi wanka nayi Alwala na dawo na tada sallah se gashi, yana shigowa ya cire jallabiyar jikinshi ya rage daga shi se singlet da short ya zauna gefen sallaya ta a haka na Idar da sallah na gama lazumi na sanann na dubeshi Naga gaba daya idonsa, bakinsa da hancinsa baki daya yana kallona, kuma kallon with lot of adoration. Baki na turo nace

Ina Kwana?

Murmushi yayi min ya amsa mini sannan yace

Zazzabin ya tafi..... Iyeee Yarinya me son mijinta ko nan da can bazata iya rabuwa dashi ba.

Rufe fuskata Nayi ina dariya a hankali, shima dariyar yayi ya maida rigarshi sannan ya dakko qura'ani daga cikin wani shelf sannan ya dawo gurina ya zauna, ya janyoni jikinshi ya bude mana suratul Anfal muka Fara tilawa, God! Kira'arshi can make someone sleep, shi Yana admiring tawa nima ina yin tashi. Haka muka kammalla na Mike na nade praying mat din sannna na maida qura'ani inda yake na hada mishi ruwan wanka nace

Creamy Kaje kayi wanka.

Wani kallo ya buga min full of daggers yace

I'm not.

Dariya nayi nace

Creamy ya zama kazami

Tashi tsaye yayi ya cire jallabiyar ya rage daga shi se short yace

Ni kika cewa kazami right?

Tahowa yake gadangadan yayo kaina hakan yasa nace

Creamy I'm sorry wasa nake fa!

Bata fuska yayi but I can glimpse at wani kwantaccen murmushi a Fuskarshi har yasa yayi wani Irin kyau ga lips dinshi yayi curving

Yau ni da ke ne a dakin nan, shebi you called me kazami right? Xakiga abinda zan miki

Bata fuska nayi ina Diddira kafata nace

Allah kayimim abu I'll cry fa.

Ina gama fada ya iso inda nake banyi aune ba naji ya dagani yasa a kafada aikuwa na Fara ihu ina fadin

Creamy ni ce fa

Ko kallona baiyi ba haka ya danna ni cikin ruwa, tare mukai wanka kusan rabi wasan ruwa ne Don naji ana cewa wasan ruwa na masoya ne tabbas hakane Don kuwa naji nutsuwa da nishadi wanda na dade banji Irinshi ba, seda muka fito naga ya saka kaya na tuna ni banida kaya suna dakin Yadikko gashi kunya komawa nake, kallona yayi yace

Chocolaty ya akayi

Kayana

I don't see anything funny amma kawai ya fara dariya wai naje da kaina, na manta kukan da nayi jiya ni me miji, seda ya gama bata min Lokaci sannan yaje ya kawo min wata Abaya pink plain babu komai jikinta amma tayi min kyau kuma abinda na fahimta da Farouq Yafi son ina saka abaya don ko lefe na abaya tafi yawa. Seda mukai breakfast kafin muka je dakin Yadikko bata Ko yimin maganar jiya ba hakan yasa na dan saki jiki, daga baya muka kara Kwana biu kafin wani cousin dinsa ya kaimu kano.

A gidan Abba muka Fara sauka, gaba daya ya tsufa mutumin kamar ba ubana dan gayu ba grey hair ya cika masa fuska, kana kallonshi ma he doesn't looks healthy amma yaji dadi babu karya I can tell from fuskar shi ya kuma yaba da Farouq, da Zamu tafi Farouq ya bashi 100k Nikam Dama 50k na kawo mishi aikuwa yayi tayi mana godiya har naji kunya saboda a ganina he deserves more. Mun fito su Rahama sun dawo Daga wani guri da Mamansu, Baki daya suka yo kaina ana ta ihu, nima murna kwance saman fuskata muka gaisa suka rakoni har mota kowa Yana complain dinshi, Allah yasa nabar 10k saura don haka na cire duka na basu tareda fadin

RAYUWARMU A YAU!Where stories live. Discover now