TWENTY FIVE

1.3K 192 8
                                    


🏵🏵🌸🏵🏵
       _RAYUWARMU A YAU!_
                      *TWENTY FIVE*
🏵🏵🌸🏵🏵

✍🏻AMMIN SU'AD
  
Shatuuu095@wattpad.....shower me with your votes and comments I'll love that, show me some love and spoil me a little..... ILYSM

Bari mu leka dakunan Amare masu tuwo da dadi!

Hafiz & Zainab

Sati biyu kenan da Kai kowacce Amarya dakinta, gidansu Zainab da farko anyi soyayyar da ake kira ta marmari babu Abinda Zainaba ta iya dangane da kitchen, hatta gyaran gidanma akwai saura sede inda Allah ya ragewa aya zakinta batada son jiki kuma Bata son kazanta hakan yasa Hafiz bai samu matsala da ita a Wannan bangaren ba. Satin farko soyayya ce zalla me tsayawa a rai wadda dukkan wanda ya gansu a Wannan lokacin zai tabbatar da irin son da sukeyiwa junansu. Baki daya satin Ummiey ce ta dauki nauyin kaiwa amaren abincin hakan yasa Bata taba kunna gas ba da sunan girki, seda sukai Kwana bakwai kafin ta daina kawowa, kuma a Wannan lokacin zai koma gurin aiki, Tunda suka Idar da sallar asuba ya dinga zuba idon ganin ta Fara shirin shiryashi amma se ta Mike a gado tare da jan Duvet cover ta koma bacci, baice komai ba ya wuce ya hada ruwan wanka sanda ya fito ya ciro kayanshi da kanshi Yana yi yana kallonta tana ta baccinta hani'an, daga nan kitchen ya nufa ya hada tea yasha sannan ya dawo daki lokacin har 7:30 tayi Don haka ya zauna gefen gadon tareda yaye Duvet din, sanyin AC ne ya bugeta hakan yasa ta bude idonta tareda turo Baki Tace

Dear

Murmushi yayi Yana shafa hancinta yace

Zan wuce office.

Gyara kwanciyarta tayi tareda kamo hannunshi ta manna mishi kiss tace

Take care.

Daga haka ta juya mishi baya, bashi ya dawo gida ba se bayan laasar lis, a gajiye ga tarin yunwa da ta addabeshi ya shigo, Tana zaune ta kame kan sofa parlon Dama Zainab badai kwaliyya ba Tasha gayu iya gayu wanda kallonta kawai se da yasa duka gajiyar shi tafiya, yasha tarairaya seda ya nutsu yace

Beb yunwa fa

Ya fada Cikeda shagwaba, murmushi tayi tace

Jiranka nake yanxu zan daura.

Yayi mamaki amma se ya danne ya cigaba da shan Fantan dake gabanshi, itakuwa taje kitchen ta dafo indomie, Tunda ya dubi plate din Baki daya ranshi ya baci, Hafiz akwai ci babu karya, baice mata komai ba yaci da daddare ta dakko diblan, nakia dasu alkaki tace shi ne abincin dare, nanma haka ya hakura, wasa wasa kullum abinda Ke faruwa kenan girki daya take shima ba na arziki ba, kafin wani Lokaci gaba daya Hafiz ya fara raina kanshi idanunsa kadai zaka kalla kasan yana cikin matsala.

Yammancin yau da ya dawo Dama tuntuni a office ya tsara yadda zai shawo kan matsalar, yana shiga ta tarbe shi kamar kullum tana ta fara'a da nuna tsantsar kulawa, seda ta tashi zata nufi kitchen kafin yasa hannunshi ya ruko waist dinta, hakan yasa ta fada jikinsa gaba daya, gyara zamanshi yayi hade da Nata yace

Zainab

In a very serious tone hakan yasa ta maida dukkan hankalinta kanshi sannan ta amsa shi kuma ya cigaba da fadin

Yaushe ne aurenmu zai rabu.... I mean expiry date dinsa

Wanne expiry date kuma? Is it not a long life thing

Ta fada fuskarta dauke da mamaki da tsoro, kanta ya shafa yace

Then indai kin yadda hakane bazan iya cigaba da zama dake a yadda kike.......

Me Nayi maka?

Katse ta shima yayi yace

Allow me, kwatakwata ba abinda nayi tunanin zan kawo gidana kenan ba? Baki iya girki ba, Baki iya kula Dani ba the only thing kike expert akai shine sex I guess Abinda akai miki huduba akai kenan...... Ki sani cikina shi ne Abinda nafi valuing akan komai everything comes after if I'm filled. Don haka ki san duk yadda zaki gyara mistakes dinki before a month if not Wallahi kinji na rantse se na maida Ke gida idan kika san Meye aure then Seki dawo..... Kwatakwata you are not wife material.

RAYUWARMU A YAU!Where stories live. Discover now