NINETEEN

1.2K 163 3
                                    


🏵🏵🌸🏵🏵
       _RAYUWARMU A YAU!_
                      *TWELVE*
🏵🏵🌸🏵🏵

✍🏻AMMIN SU'AD
  
Shatuuu095@wattpad.....shower me with your votes and comments I'll love that, show me some love and spoil me a little..... ILYSM

This page goes to Anty Fauza..... 'yar amanar kainuwa...... All thanks to you.

Cikin kankanin lokaci muka Fara end of term exams, makarantar baki daya kowa karatu yake su juniors 3 papers suke a rana muka kuma muyi 2 papers a rana. Sati daya muka gama sannan muka Fara satin zaman banza, Baki daya satin bamu zuwa class muna hostel Sede muci abinci, muyi games da wakoki da kidekide, se kuma sallah, ranar naje block A Naje dakinsu Najeeey na tarar suna karatun Hausa novel wannan shi ne first time a rayuwata da naji inason ji, gefen Najeey na zauna ana karanto mana fuska biyu, God littafin yayi min Daga Nan na fanjama na zama Ogar kaina har a class ana lesson ina karatu na zama expert a Wannan gurin, karatun da nayi ma bazasu irgu ba.

Wata ranar Wednesday ana wani programme akan child spacing da Muslim corpers association of Nigeria jigawa chapter suka hada a dutse polytechnic aka zaba class dinmu mu biyar ni, S bukar, Nadia na manta sauran biyun gaskiya mukaje, lectures din is Mashaaa Allah kawae Amma muna gurin wata malama da Niqab fuskarta Tace mu 'yan secondary ne bai kamata amana child spacing ba bayan bamu San me aure yake fada ba, wannan yasa speakers din da organizers akace zaayi organising wani akan marriage. Da aka gama aka bamu su hisnul Muslim muka taho school.

Ranar Friday shi ne ranar Hutu, kowa ka kalla murna yake idan ka dauke ni, bacci ma nake abuna saboda banga dalilin da zaisa na kafa murna ba hasalima haushin hutun nake ji don banki muyi ta zama a school ba, se wajen 7 house captain tazo nemana saboda banyi Shara ba, haka na tashi na dauka tsintsiya na share sannan naje zanyi wanka to school din sunada ka'ida ranar Hutu so ake 7 an fita a hostel hakan yasa da naje da kyar metron dinmu Mama Jebu ta barni nayi wanka, ina gama shiryawa ana hura whistle na fita aikuwa babu jira na fice inajin har na Fara missing school.

Yaya Hanif shiyazo daukata hakan ya dada min rai sosae Sede tunda na ganshi na fahimci babu lapiya saboda yadda murmushi ma fake yake bani, ya rame sosae duk wannan kuzarin babu. Hakan bance dashi uffan ba mukaje gurin class teacher aka karba result dina nazo ta 11 out of 37 naji dadi saboda inajin nayi kokari tunda datsarsu nayi babu background bare introductions haka na fara, shima ya nuna min jin dadinshi kafin muka tafi mota Inata sallama da friends dina.

Tunda muka shiga duk surutun Yaya Hanif shiru yayi ni ce ma nake ta bashi labarin school amma idan nayi abin dariya sede naga baiyi ba, ko kuma ya tafi absent minded, hakan yasa nace

Ya Hanif

Da sauri ya juyo yace

Ina jinki Habibty go on

Hararashi nayi nace

Park the car

Saboda me?

Saboda nace

Na fada sounding authoritative, bawan Allah Habiby se yayi parking ya juyo da dukkan hankalinshi kaina, yabani tausayi saboda ina iya hango tsananin tashin hankali akan Fuskarshi amma bana son hakan ya dameni har ya hanani aiwatar da abinda nayi niyya hakan yasa nace

Tell me

Hannunsa ya juyar alamar rashin sani me zai fada tare da kuma kawar da kanshi gefe, hakan da yake yana kara jefa zuciyata cikin tunani, tabbas Yaya Hanif akwai Abinda Ke damunshi.

Me zan fada miki Habibty?

Abinda yake damunka, Habibi akwai Abinda zai dameka ka kasa sharing dinsa Dani, Inace we're team mun yarda dukkan abinda ya samu dayanmu mu ya shafa?

RAYUWARMU A YAU!Where stories live. Discover now