THREE

1.6K 185 1
                                    


🏵🏵🌸🏵🏵
_RAYUWARMU A YAU!_
*THREE*
🏵🏵🌸🏵🏵

✍🏻AMMIN SU'AD

Shatuuu095@wattpad

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
_United we stand and succeed our ambition is to entertain and motivate the mind of readers_

*Shout out to all those who were separated by the person they love, cherished most in their life. What will be life will definitely be. The page is yours!*

Binta ta jima tsaye kafin ta shiga dakin saboda ta rasa me yasa tsohon keyi mata wani Irin kwarjini, haka ta shiga inda ta sameshi zaune da kwaryar Zuma Yana diba cikin wani kwanon azurfa, dagowa yayi ya dubeta kafin ya nuna mata gefe tareda bata ixinin zama, zama tayi a takure tana bin dakin da kallo, katifa ce katuwa an shimfide ta da bedsheet se akwatina wanda babu tantama kayanshi ne a ciki, Daga gefe shelf ne me littatafan addini a ciki Se carpet dake malale a tsakar dakin, murya ya gyara wanda yasa Binta sake nutsuwa tare da maida kanta kasa gabanta na doubling bugun da yake.

Inason inji asalin ki har yadda kuka hadu da Adamu

Ko ance kayi karya gaban Alhaji Bana tunanin zaka iya yi, saboda xakaji discomfort itakadai will make you spit out the truth. Babu shiri ta fada masa komai ba tareda tayi karya ba , shiru ya ratsa dakin na kusan Mintina goma kafin yace

Zaki iya karbar musulinci?

Maganar tazo mata a bazata, hakan yasa tayi shiru Tana tunani sosae kafin tace

Adams yace Yafi son na zauma a faith dina Tunda I've right to religion

Alhaji baiyi mamaki ba Sede ya sake maimaita tambayar

Zaki iya karbar musulinci

Babu wani dogon tunani tace

A'a zan zauna a addini na

Cikin gamsuwa Alhaji yace

Koma dakin da aka kaiki zan saka ayi miki magana

Haka ta Mike ta fice tana jin wani tsoro Yana bin ilahirin jikinta,

Bayan sallar ishai Baki daya Uncles dina su takwas Harda Abba suka nufo cikin gida, Abba Sagir shi ne babba kuma architect ne suna xaune da iyalinshi a zamfara, Baba Nafi'u shi ne na biyu class room teacher ne anan majiya, Baba me sunan marigayi kuma yana Kano sannan shi Accountant ne na government house na kano lokacinda jigawa ta rabu da Kano ya koma Accountant general na jigawa state yafi kowa kudi cikinsu suna xaune a Kano mostly zamansu a dutse yafi yawa, da matarshi da Umman mu uwarsu daya ubansu daya haka yasa muka shaku da gidan dukda se nafi shekara Banje inda suke ba harse sunxo. Shikam Abba kasim yafi Abba rashin mutunci baiyi karatu ba Shiyasa yake wani daban cikin yan uwansa, se Abbanmu, Abba shettima shikam barrister ne the only no nonsense man cikin family gaba daya nafi sonshi saboda shakuwar dake tsakanin mu tafi karfin na rubuta muku anan, he's my second father, my mother and also my brother saboda lokacinda Umma ta bar gidanmu Abba shettima was the only one nake gani Naji dadi har Seda yayi aure ya bar gidanmu Daga shi se uncle Manga karamin uba as we call him, manomi kuma saboda ya yadda da agriculture gidan gona yake da ita katuwa a majiya ana kiwon kaji both layers da browlers, kifi, shanu, zabi, bullet dasu geese karatunshi kaf Kan Agriculture, breeding and rearing. Se auta Kare nono wato Uncle Mamman Dan Boko kenan, wasu halayensa yana Kama Dana Abbana akan gayu da son Boko.

Se kuma mata Don gidan seda aka gama haifar Maza kafin aka haifi mata su goma, Baba hajara Itace babba matar Tana da matsala sosae halayen munafukai sun fito rado rado a jikinta, mukan godewa Allah da Batayi karatu ba, don da ace tayi karatu tabbas da mun shiga uku se Allah yasa ko primary Batayi ba, Baba Zainabu wasu suna fadin I'm her second saboda yadda muke azabar Kama da ita, na tashi bansan uwar da ta haifeni ba hakan yasa nake ganin tamkar Itace uwata se daga baya na fahimci kanwar Abba nace, tana min so da kauna kamar yadda nake mata matsala daya mukan dade bamu hadu ba saboda tana Suleja tana aure, Baba hannatu kam a majiya take ina Yarinya nakan ce Allah ya zabe masu kyan halin ya daukaka su yayinda sauran munafukan ya Barsu a majiya cikin kangin talaucin, itama batada dadin shaani se naje na gama kwanaki na Banje inda take ba amma muka hadu zansha zagi, Baba Batula reserved one kenan tana auren wani dagaci a maje batada hayaniya ba kuma tada son mutane amma ta fiye min sauran, Anty Adama tana aure a hadejia itama matsalarta fuska biyu bazaka taba fuskantar inda tasa gaba ba, daga kan Anty Rahila aka Fara kai mata makaranta hakan yasa suka waye sosae kuma iyaka secondary ne se mijinka yaso ka karasa gidanshi, ita Tana aure a katsina kuma mijinta shima yayan Umma ta ne uwa daya uba daya itama sosae take zumunci damu, Anty Zakiyya kuma tana Abuja tana auren wani mutum me kudi hakan yasa take jinta daban cikin yan uwanta tana ganin tafi karfin wasu a ciki shirinmu da ita kadan ne plus bata son Umma ta kuma dalilinta Umma Tasha wahala, se wanda muka fi shiri Anty Asiya, Anty Lawisa da Anty Mama. Wannan kenan!

A dakin Alhaji suka yada zango Bayan sun gaisa da mutanen gidan, dayake gidan sarauta ba'a rabashi da mutane, Hajiya Azumi da sauran matan biyu duk suna xaune suna mamakin dalilin Wannan taron, seda akai gaishe gaishe kafin Alhaji yace

A cikin ya'ya na Maza takwas Adamu, shettima, Mamman da manga ne kawai basui aure ba, a mata kuma Asiya da Mama ne kawai suka rage, kun kasance shaida akan rabon da Adamu ya Waiwaye mu shekaru uku kenan cikin hukuncin ubangiji yau se gashi yazo da wata Christian wai zai aure ta.

Surutan daya kacame cikin dakin yasa dole Alhaji tsagaita maganarshi, Abba kam se sake kasa da Kai yake yi, yayinda iyayenshi da yan uwan ke nuna alamun rashin goyon bayansu har Abba me sunan marigayi yace

Me zakai da Ahlul kitab, Bayan ga musulmai mata basu Kare ba

Alhaji ne yace

Ku bari na Baku ixinin yin magana kafin kuyi, na samu yarinyar munyi magana akan indai ta amince zata karbi musulinci to Adamu mijinta ne Don ko bbu komai ai jihadi ne amma se tace dani Adamu yace she's free tayi addininta, haka na sake maimaita tambayar amma Tace bazata iya musulinta ba, Wannan dalilin yasa gobe Nafi'u zaka maida ita garinsu babu aure tsakaninsu.

Kowa yayi Na'am da wannan maganar tareda kwantarwa da Alhaji da su hajiya hankali amma Abba tunanin yadda zai bullowa Alhaji yayi hakan yasa yace da Alhaji

Inada magana

Kafin Alhaji yayi magana hajiya Azumi tace

Me zakace Adamu? Kanada bakin kara magana Dama? Arniya zaka kawo mana matsayin suruka? Yaushe rabon da kazo ka gaishe mu?

Alhaji ganin muryar ta na rawa yasa yace

Azumi ya isa haka, Adamu ina jinka

A hankali Abbanmu yace

Nake ganin kamar Allah ya halatta auren Christian, I see nothing bad akan hakan.

Kowa a gurin yayi mamaki kafin Alhaji yace

Tabbas ya hallata ka auri Ahlul kitab, amma ka isa da gidanka, banyi maka Baki ba amma ka guji duniya saboda Allah yace

"Riddallahu fi Riddal walidain, wa sukuddullaha fi sukuddul walidain"

_Yardar Allah yana daga Yardar iyaye haka Fushin Allah yana Daga Fushin Iyaye_

Bazan taba yimaka lamani akan auren wadda ba musulma ba, Yaushe da ka rike naka addinin Balle ka kula da na wani.

Seda Alhaji ya kalla kowa kafin yace

Inason kowa yayi min shaida matsawar inada rai Adamu ya auro waccan to tabbas na cireshi daga ya'yana. Ku tashi na sallami kowa.

Kowa jiki a sanyaye ya fito dayake Baba me sunan marigayi da Abba shettima se Baba Zainabu, Anty Zakiyya da Anty Asiya su kadai suke uwa daya ya'yan hajiya Azumi kenan. Baba me sunan marigayi yace da Abba

Muje dakin hajiya

Tunda suka shiga yake tayi masa nasiha akan ya hakura yayinda bakin ciki ya Hana Hajiya Azumi magana.

Washegari kuwa Abba Nafi'u ya maida Binta Zaria Bayan an hada mata Sha Tara ta arziki kafin Tana kuka suka wuce ba tareda ta sake ganin giftawar Abbanmu ba.

Shatuuu ♥️

RAYUWARMU A YAU!Where stories live. Discover now