TWENTY ONE

1.2K 177 7
                                    


🏵🏵🌸🏵🏵
       _RAYUWARMU A YAU!_
                      *TWENTY ONE*
🏵🏵🌸🏵🏵

✍🏻AMMIN SU'AD
  
Shatuuu095@wattpad.....shower me with your votes and comments I'll love that, show me some love and spoil me a little..... ILYSM

Wayar hannu na aje gefen gado ina sake tariyo hirar mu nida Yaya Hanif, Nikam Tunda nake ban taba rokar miji Bayan Hanif ba ina ganin Allah gave me all I don't have to ask for more. Son Hanif kullum Kara gaba yake yana bin dukkan sassan jikina, komai nake a duniya to Hanif is always in my thoughts har kunya nake ji na daga hannu na roki Allah abu ba tareda na rokawa Hanif ba inajin Hanif is my better half ban ma taba kawo akwai wani abu da zaiyi mana tsaiko cikin rayuwar ba ashe yana kan hanya.

Hutun karshen term na dawo, Tunda na dawo na kasa fahimtar inda Yaya Hanif ya dosa Baki daya ya zame min tamkar wani stranger ko magana muke se inajin muryar shi tamkar yana cikin damua Duk yadda naso ya fada min matsalarshi abin ya faskara, ni kaina nasan inada naci amma duk naci na yaki fadamin komai.

Lokacinda aka fara tafiya hajji muka tafi nida Umma da Buddy, tafiyar ansha bala'i kafin Abba ya amince naje, Dama bai taba Zuwa saudiyya ba Balle kuma matanshi ni bansan kudin da Abba yake nema ina yake kaisu ba Saboda inkika dauke jikinmu da abincinmu babu inda zaki ga wannan kudin, ana gobe zan tafi da safe bayan munyi break kowa Yana parlour Baki dayanmu yaran gidan, Abu ne dake faruwa once in a while hakanan, kuma yanxun babu laifi akwai dan fahimta tsakaninmu ba kamar da muna yara na, kowa fadar abinda yake so dayake Zamu siyo mishi yake Salma tace Abaya takeso, Feey Tace turarruka se yaran wai dolly ta wasa, Big yace jallabiya nace a'a tashi kafiya naci dai, kowa yayi dariya, Alamin yace waya, Zainab ce kawai bata fada ba nace

Kefa?

Murmushi tayi tace

Duk Abinda Kuka kawo min

Har cikin raina Naji dadi Zainab is changing kuma ina jin zuciyata tana karbarta Tana bata wani matsayi na daban, Al dake gefe yace

Ke Feey da gaske tashi zamui daga gidannan?

Baki daya muka zuba mata ido, dama ba wani dariya takeyi ba hakan yasa ta kare daure fuska ita a dole muna neman abu a gurinta,

Haka Anty Binta ke fada min

Dukkanmu munyi mamaki Buddy yace

Ke Nafisa da gaske kike?

Duk iskancin Feey tana tsoron Buddy hakan yasa Harda Rantsuwa wai gidan a Lodge road yake Nikam karaf se nace

Kai meye yake saka Abba kama haya, da hayar isn't it better mu gina gidanmu na kanmi

Big yayi tsaki yace

Wallahi wannan relocation din namu pains me Bakada damar bada address daya.

Zainab ce tace

Gaskiya ne, sarki we need to talk to him Tunda Naga matan gidannan kamar basuda amfani

Dariya duka mukai Buddy yace

No Zeey Karki fadi haka, may be he has his own reason mu jira muga plans dinsa.

Salma da se lokancin tayi magana tace

Wane plan? Shidai yana son gida me kyau bayada kudin ginawa, daidai kudinshi kuma ya raina

Adnan yace

Kan bala'i gaba daya baku gane halin bawan Allah nan ba, tsabar mugunta ke damunshi saboda kada ya mutu muci gadonshi......

Wani kallo Buddy yayi masa Daga nan aka canja topic, ni Duk tunani na ni kadai hayar da muke ke damu ashe kowa haushin abun yakeji, Washegari muka tafi Airport Inata kiran Habibi saboda yayi alkawarin kaini airport Amma baya picking haka nan na hakura muka tafi Big Ya kaimu, Umma dama Kwananta biyu da zuwa don ta kano ta biya mana, babu laifi anyi mana rakiya 'yan uwa sosae sede babu Yaya Hanif ciki, wata paper dake Bayan wayata na cira na karba pen hannun Yaya Hafiz nayiwa Habibi note kamar haka

Habibi I longed to see you amma Bakazo b, ban kuma samu any message Daga gareka ba, na kiraka for several times Bakai picking ba, I hope is not anything amma whatever it's inason ranar da zan dawo kazo ka daukeni...... Your Habibty

Daga haka na nunkke na bawa Amra ta bashi haka muka shiga jirgi, lokacinda jirgin zai fara tafiya kan runway kawai na hango Habibi tsaye idanunshi kir cikin Nawa yana cikin Armani sweat pants black da Top maroon kasancewar shi yanada haske ga kuma Rana data haske shi sai naga yayi min masifar kyau idanunshi Sanye da Prado sunglasses baki Wanda ya fito da dogon hancinsa, Yaya Hanif kam Issa beauty domin Yafi karfin nace dashi handsome, kallonshi nima nayi tayi seda naga jirgin zai taking off se na cira hannuna ina masa waving, shima haka daga baya na dena ganinshi Baki daya mun hau sararin samaniya, jikin Umma na kwantar da kaina ina tunanin Meke faruwa Meke damun Hanif? Me yasa zaiki zuwa ya bayyana kanshi?

Bansan mun iso ba se naji Umma na fastening mini belt, kawai naji muna landing to shi yafi tsoratani akan taking off, ji nayi kamar zan fado ko kuma kayan cikina zasu zubo na kankame Umma aikuwa Yana landing na sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Daga Riyadh muka wuce Madinah garin akwai niimah, Munje ziyara munyi ibada Umma Tana ta jadadda mana especially ni aikuwa addu'a wasu lokutan har rasa abin roka nake, kwanan mu goma muka koma makkah, ina shiga Harami na hango ka'aba real image not a waya ko a TV gata ina gani kawai se naji Tsikar jikina tana tashi, wani rauni from no where ya lullubeni, subhannalllah! Kadai bakina Ke iya ambata, haka mukai ta kutsawa dayake Bbu cikowa sosae ba'a fara aikin hajji ba yasa na taba ka'aba kawai se na fashe da kuka baki daya zuciyata ta bude duk wasu jiyoyi dake jike da jini naji tsananin tsoron Allah na shiga ta.

Kwananmu biyu aka fara Ibada, haka na dage dayake Umma babu wasa komai mukeyi mu uku abinmu a haka har mukaje Muzdalifa akai hawan Arfa, mukai jifan karshe sannan mukai hajjin bankwana ya rage kwanaki hudu mu koma gida, nan Umma tasa mu gaba da siyayya Harda cargo mukai Kai kace kanmu aka fara fita daga kasar.

Nigeria

Ummiey na zaune gefenta Yaya Anisa Sunata duba kayan da Ummiey ta siyo na kitchen da yake lokacin da aka dauka na aurar dasu is almost due, Amra ce ta fito hannunta rikeda wayar Ummiey, karba Ummiey tayi taga Anty Rahila ce, dauka tayi suka gaisa kowa na tambayar familyn kowa

Anty halima wancan satin Baban Amina yazo akan maganar aurensu akan ta fitarda miji amma se tace wai me sunan sarki (Yaya Hanif) take so.

Dammmmm! Ummiey taji gabanta ya fadi Hanif kuma? Ta fada a ranta kafin ta cigaba da sauraron Anty Rahila

......ni duk tunanina Hanif na son Nanayen Kubra ne amma how's that possible?

Nannauyan ajiyar zuciya Ummiey ta sauke tace

Rahila banida masaniyar komai a zancen nan abinda nafi ganin yafi dacewa mu jira Hanif yazo naji daga gurinshi.

To Anty se naji ki.

Yaya Anisa wadda tayi shiru Tunda aka fara wayar tace

Dama lokacinda nake tsoro ne yazo. Baki daya laifin Yaya Hanif ne Wallahi

Cikeda rashin fahimta Ummiey tace

Anisa yimin bayani ban gane ba, Inace Hanif Hassana yake so?

Bude bakinta tayi Don yin bayani sega Yaya Hanif ya shigo........

To fa! Meke shirin faruwa...........

Shatuuu♥️

RAYUWARMU A YAU!Where stories live. Discover now