THIRTY SIX nd SEVEN

1.6K 197 8
                                    


🏵🏵🌸🏵🏵
       _RAYUWARMU A YAU!_
                      *THIRTY SIX & SEVEN*
🏵🏵🌸🏵🏵

✍🏻AMMIN SU'AD
  
Shatuuu095@wattpad.....shower me with your votes and comments I'll love that, show me some love and spoil me a little..... ILYSM

Daren da zan tafi Ringim naje gurin Abba shettima Yana kishingide Kan carpet se pillow a bayanshi, na zauna muka gaisa sannan yace dani

Gobe da safe zaki tafi ko?

Kaina na gyada nace

Inshaaa Allah

Girgixa Kai yayi yace

Gobe will mark a new beginning a rayuwarki, zaki fara aiki da kika rantse zakiyi with every sincerity and strength, ki sani wannan aikin zai iya kaiki Aljannah zai kuma iya kaiki wuta..... You're dealing with human lives, show sympathy and empathy a Aikinki, ki rike gaskiya da amana xakiga zaki ta prospering a rayuwarki.

Kaina na gyada mishi nace

Inshaaa Allahu zan kiyaye.

Se kuma abu na gaba, ki rike mutucinki ki kula da kanki zakije inda babu Wanda kika sani be our ambassador kinji...... Allah ya bada sa'a

Kaina na kara gyadawa Nayi mishi godiya sannan na koma daki, ina zuwa muka Fara waya da Umma bata kasar sunje Russia itada mijinta, itama kusan Abinda Abba shettima ya fada min shi ta kuma maimaita min. Washegari komai na ya kammalla se Big yazo ya tafi dani, 7:50am muna Ringim, inda zan zauna cikin asibitin muka Fara zuwa kafin kuma muka je office din chief nursing officer na asibitin, nan yayi addressing dinmu kafin muka zagaya asibitin, Maternity akai posting dina mu biyu don haka muna gamawa muka wuce can, Metron din tamu Christian ce amma tana da kirki yadda ta karbe mu tana ta bamu Irin motherly advice dinnan, tace mu saki jikinmu muji mu kamar staffs, Abinda bamu iya ba mu tambayi koma waye Za'a koyal mana.

Ranar babu wani aiki muka koma gida, muka gyara dakin komai yayi neat yadda akeso, daga nan sabuwar rayuwa kuma ta Fara.

Watanmu daya akai releasing result dinmu, Alhamdulillah na zama successful and registered nurse, ranar nayi murna duk wanda ke sona ya tayani murna saboda nasan na dakko hanyar nasara cikin rayuwata. Seda nayi watannni biyu kafin na Fara shifting it was tiring amma babu yadda zakayi.

Wata ranar alhamis na dawo daga night duty, ina shiga daki nayi wanka, na nade kan katifa na fara ramuwar bacci da banyi da daddare ba, har wajen 12 sannan na tashi shima wata azabbabiyar yunwa ce ta tashe ni, ina mikewa Naje Nayi brush na kunna wayata sannan na daura abinci, jollof pasta Nayi na fara ci kenan, wayata ta Fara ringing, tsaki nayi na duba se naga Amra ce hakan yasa naji dadi na dauka

Maman biyu!

Tsaki taja tace

Ke yar iska ce Wallahi, a dakin haihuwa kike kin San what it takes to give birth amma har kike min mugun fata

Dariya ta kwace min nace

Kai matanan har na hango ki a labor room...... Wayaga ihu

Gaba daya mukai dariya kafin muka gaisa tace

Tun safe nake kiranki Amma wayanki baya going.

Tea na kurba nace

Wallahi kua, night Nayi shi ne nasa wayar a flight mode

Ayya.... Dama kinga duka Munzo Majiya fa, Kece baki zo ba, shi ne nace Bari na tabo ki naji Yaushe zaki taho

Aje cup din Nayi nace

Me akeyi a majiya din?

Tsaki ta bugan wanda yayi barazanar fasan kunne tace

Bikin Yaya Ma'aruf din Baba Hajara mana

RAYUWARMU A YAU!Where stories live. Discover now