TEN

1.3K 220 14
                                    


🏵🏵🌸🏵🏵
_RAYUWARMU A YAU!_
*TEN*
🏵🏵🌸🏵🏵

✍🏻AMMIN SU'AD

Shatuuu095@wattpad

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
_United we stand and succeed our ambition is to entertain and motivate the mind of readers_

*Shout out to all my cousins out there who add more spices to life making it less boring and making it conducive. This page is yours...... ILYSM*

Da na isa bakin motar Abba na ciki se mummy a gaba da dukkan alamu wani gurin zasu Don kuwa Tasha gayu yadda baka zato sede fuskarnan babu digon annuri a ciki, seat din baya na shige abina Abba yaja muka tafi, Dama a kundila suke mu kuma muna Badawa, Tunda na shiga motar shiru babu Wanda yake magana se can Abba yace

Sakina zan fara visiting lecturer a ABU Zaria, every Mondays.

Da yake ina ciki se ta fadada murmushinta tace

Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi

Amin

Yace da ita kafin kuma suka ware suna hira, can ya shiga filling station da a zuba mana Mai yana fita kuwa mummy ta juyo tace dani

Har murna kike zaki tafi ko? Zaki ci ubanki ina nan zaki dawo ki sameni se na lahira ya fiki jin dadi. Me bakin halin uwarta

Kasa nayi da kaina saboda bansan na dago taga idona me Cikeda tsanar ta, matsawar zata zagi Umma se Naji na tsane ta, take kuma se zancen su Zainab ya dawo min na cewar Abba ya fara wulakanta ni, kuna haka ne he shows less care a kaina kan sauran yaranshi.

Bata Kara magana ba saboda Abba ya dawo Se hira tsakaninsu, muna isa ya sauke ni bai ma shiga ba don kuwa gateman dinsu yace Baba da Ummiey basa nan, baba megadin ne ya dauki kayan Nawa zuwa ciki yayinda Abba yace dani

Be a good girl

Murmushi nayi nace

To Abba.

Mummy Tace

Idan hajiya Halimar ta dawo ki gaishe min da ita.

To mummy Allah ya kiyaye.

Daga haka na shige ciki inajin tamkar am free, gidansu babu laifi Don Yafi namu girma da kyau ko da yake samun ma ai ba daya bane, a parlor na tarar Ya Anisa dasu Amra sun zagaye kayana suna jiran shigowata, wani ihu muka saki na ganin juna kafin su rungume ni Baki daya.

Yaya Hanif shi ne dansu babba sunanshi na gaskiya Ismail, Yaya Ammar shi kuma Habib yake Tun Abba bai auri Umma ta ba aka haife su, Daga nan se Yaya Amima Saar salmar gidanmu ce ita kuma 'yar Anty Rahila ce a gidan take Zaune, se Yaya Anisa, Marzuq kafin Amra se Asim da Adil twins ne. Amra ce sa'ata 3 months na bata Shiyasa muka fi shiri da ita, kayana ta dauka ta Kai dakinta nan Yaya Amina ta zuba mana abinci muka dinga ci muna hira, ina sonsu saboda basuda matsala, indai kazo gidan an dinga nan nan dakai kenan.

Muna ta hira abinmu har La'asar tayi, duka suka Mike se ni daya ina duba story books din da Amra ta bani, har suka Idar Seda Yaya Anisa tace

Hassanah Kinyi sallah ne?

Dagowa nayi nace

Lokacin sallar yamma yayi ne dama?

Yadda nayi maganar Baki daya sukai dariya Yaya Amina Tace Dani

Tashi kije kiyi.

Mu gidanmu se ka gadama kai sallah idan baka gadama ba ruwanka, itama mummy se Lokaci ya xarta take yi.

Da daddare su Ummiey suka dawo murnar gani na ba ga ita ba baga Baba ba Balle kuma Yaya Hanif wanda se lokacin muka hadu. Tare mukai dinner kafin Ummiey ta dinga min tambayoyi akan gidanmu wasu na bata amsa wasu kuma nayi murmushi. A haka muka kwanta ni da Amra abinmu dadi.

RAYUWARMU A YAU!Where stories live. Discover now