FIVE

1.4K 166 3
                                    


🏵🏵🌸🏵🏵
       _RAYUWARMU A YAU!_
                   *FIVE*
🏵🏵🌸🏵🏵

✍🏻AMMIN SU'AD

Shatuuu095@wattpad

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
_United we stand and succeed our ambition is to entertain and motivate the mind of readers_

Baba me sunan marigayi wucewa yayi Dakata inda nan ne gidansu Umma ta shida Abba sagir Don isar da saqon Alhaji, suna isa sukai kicibis da uncle Ridwan wanda da alama Daga gurin daurin Auren yake, Bayan sun gaisa da yake hankalin su Baba a tashe yake yasa ko Bayan daurin auren basu nema mutane ba, aika shi yayi akan ya turo masa Ummiey, ai kuwa seda ya fi fifteen minutes kafin ta fito Tasha ado, fuskarnan dauke da murmushi ganin Abba sagir yasa ta sunkuyar da kanta alamun Anga yayan miji, gefe suka dan kebe bayan sun gaisa kafin Baba yace da ita

Halima Munzo ganin Yaya ne

Dan Jim tayi kafin tace

Shigowarshi kenan Bara amma na muku iso

Daga haka ta shige gida straight parlonsa ta wuce su uku ne kawai shida kanninsa daya se abokinshi daya, seda yayi mata izinin kafin ta shiga ta sanar dashi bakin dake jiranshi, mamanki sosae Yayi Don Baya tunanin sun fi awa da rabuwa amma se yace

Halimatou ina fatan dai ba wani abu ne ya faru ba ko

Itama ta fara jin uneasiness din kawai se tace dashi

Yaya basu fada min ba

To Maza shigo dasu ta kofar gaba, Tunda gidan a cike yake

Hakan kuwa tayi Seda suka shigo kafin ta fita abinta ranta fal tsoro saboda Kwana biu takan ji tamkar bata kyauta ba da tayi sanadin hadin Umma da Abba, ta manta what is meant to be will definitely be no matter what.

Bayan sun gaisa tareda yiwa juna murna Abba sagir ya fara magana

Alhaji ne ya Turomin akan Kada a kawo khadija a barta a gida

Barrister ne yace

Saboda me kenan?

Wannan karan Baba me sunan marigayi ne yayi musu bayani sosae akan abinda Ke faruwa, Wanda hakan ya kara tension din dakin, baki daya shiru ya ratsa dakin kafin Yaya yace

Ina ganin baza'ayi hakan ba, nake ganin babu amfanin an daura aure sannan kuma Kubra ta cigaba da zama gidan nan, Tunda shi ya tafi se akaita dakinta duk lokacinda ya dawo Se ya tarar da ita. Amma ya kuka gani

Kamar wasu me zance suka amince kafin ya aika Hajiya Taxo yayi mata bayani, take tace babu inda Kubra xataje wannan wulakanci Abbana yayi musu Amma se Alhaji ya taka mata burki akan yadda yace haka za'ai, ai kuwa Shiyasa har kwanan gobe Nene bata son Abbanmu.

Da yamma aka kai Amarya gidanta mutane nata santin gidan, kowa se ya tambayi aikin da Abba yake ya mallaki uban gidannan, bisa umarnin Nene aka bar Umma da kawayenta wannan ya kwantar mata da hankali, suna ta shakiyanci ita kuma tana ta tunanin sabuwar rayuwa da zata Fara, tana tariyo tarin nasihun mutane kanta, Duk dai abu daya ake ta repeating tayi biyayya aure ibada ne, tayi hakuri shi ne jigon aure, babu Wanda yace mata girki da iya magana shima na cikin aure.

Washegari har yamma tayi babu alamun ango zaizo gashi har kawayenta sun Fara watsewa Don komawa gidajemsu nan hankalinta ya fara tashi ta dinga kuka ga tsoro daya addabeta, ana cikin haka Sega Ummiey da Anty Rahila sunzo, ganinsu yasa taji tamkar an tsoma ta cikin Aljannah, haka ta rungume Ummiey wadda Zuwa lokacin sun san halinda ake ciki babu Wanda hukuncin yayiwa dadi sede Bakada say a ciki.

Basuyi mata bayanin komai ba suka wuce dakinta aka bude wardrobe suka jide kayanta wajen Rabi cikin akwati sannan Anty Rahila ta kamo hannunta Ummiey ta kulle ko ina Bayan sun kara daukar abin da suka san zata bukata sannan straight suka nufi gidan Baba me sunan marigayi, Tunda sukaje batace Kala ba kamar yadda babu Wanda yace da ita wani abu, dakin dake gefe Ummiey Tace ta shiga, babu musu kuwa ta shige ta hau gado Tana bin dakin da kallo tamkar shi ne Karo na farko da ta Fara shiga, Baki daya ta kasa placing chess dinnan a right place, me ya dawo da ita gidan Anty Halima? Ba aure akai mata ba? To Kodai mijin ya mutu ne? Take ta cire wannan tunanin cikin zuciyarta ta Mike jin kiran sallar ishai, tana idarwa Ummiey ta shigo ganinta kan praying mat yasa tace

Kubra

A hankali ta dago tareda kirkiro murmushi tace

Anty

Gyara zamanta tayi tace

Kina da hakuri Kubra, hakurin ki Yana bani tsoro ina ganin kada hakurin ya cutar dake

Murmushi tayi Wanda yake genuine tace

Haba Anty, hakurin? Indai na rike hakuri a rayuwata na tabbatar nayi babbar riba, kada ki damu hakuri bazai taba zama cuta gareni ba.

Sosae Ummiey taji dadi sannan tace

Abbansu small yana nemanki.

Da sauri ta Mike saboda haka kurum take ganin girma da mutuncin Baba me sunan marigayi, tare suka fito parlour babu kowa se shi kadai, Seda suka gaisa ya dan zolaye ta kafin yace

Kiyi hakuri nasan Kinada tsananin hakuri Amma dan Allah ki Kara hkri

Gaba daya kanta se ya kara daurewa to meye ya faru? Tasan ba mutuwa bace don bazasu zama relaxed haka ba. Kafin ta gama tunanin taji Baba ya fara fayyace mata dukan abinda ya faru ya kara da fadin

Mun yanke hukuncin zaki zauna nan amma Yaya (Alhaji Habibu) yace sede kije majiya ki zauna so zaki huta na sati daya kafin mu kaiki can.

Maganar ta bige ta sosae, miji ya tafi? Karatu? Ya barta? Saboda baya sonta? From that instant Umma tayi developing cewa a gurin Abba ita ba kowa bace face matar hadi, wadda batada wani kwarjini gurin miji, kuma bawai don soyayya zasu zauna ba kawai don iyayensu suna son su kasance tare.

Bayan ta koma daki bacci yace baisan magana ba, baki daya taji ta cikin sabon begen Muzammil tunanin ranar da yaxo Yi mata sallama ta dinga yi bata taba kawowa zai iya hakuri Irin yadda yayi ba Amma se gani tayi ya karfafa mata gwiwa tare da sake bata hakuri. Kawai se ta samu kanta da fashewa da kuka, wani Irin kuka ta dinga Yi tana jin babu wata wulakantawa da xa'ayi maka wadda tafi wannan.

Wannan sati daya da tayi yai mata dadi saboda yadda ake nan nan da ita, har Seda lokacin tafiya majiya yayi, nanma hajiya azumi ta nuna mata zallar soyayya itada Alhaji, dukda kowa Yana tunanin yadda zata iya rayuwa cikin garin Tunda dai daga birni tazo, Sede ta Bawa kowa mamaki Don kuwa bata taba korafi ko jin gajiyawa da zaman garin. guri daya aka ware mata me daki Daya ta zauna sede duk wannan soyayyar bazata taba manta cewa anyi mata aure kafin a kawo ta mijin ya tafi ya barta wannan ya tsaya mata a rai.

Watarana tana zaune bayan sallar maghrib ta jiyo sallama, da kanta ta Mike ta fito Zuwa inda akai sallamar, nan ta hadu da Anty Zakiyya da Baba hajara, Dama tuni ta aje Baba Hajara gefe don kuwa ta fahimci matar bata kaunar ta, amma bata nuna komai ba ta musu iso ciki, Tunda suka zauna suke yada magana ta yaya miji ya tafi ya barka ka nace zaman jiranshi? Bata ko kalli inda suke ba ta cigaba da shirun da take wanda dama al'adarta ce hakan. Seda suka tabbatar maganganunsu sun soke ta kafin suka tafi. Bayan ta dawo se kuka tana jin Wacce Irin rayuwa take ciki? Yaushe zata fitar Daga Wannan kangin.

           
Shatuuu ♥️

RAYUWARMU A YAU!Where stories live. Discover now