TWO

1.9K 187 9
                                    


🏵🏵🌸🏵🏵
       _RAYUWARMU A YAU!_
                      *TWO*
🏵🏵🌸🏵🏵

✍🏻AMMIN SU'AD

Shatuuu095@wattpad

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
_United we stand and succeed our ambition is to entertain and motivate the mind of readers_

Tunda Abba ya bar gurin ya dinga tunanin ta yadda zai dawo ya same ta, don wannan tayi matching da taste dinsa. Seda ya jera kwanaki wajen bakwai Yana Zuwa se a karshe suka hadu inda ta gabatar masa da kanta as Binta kuma asalinta yar Zaria ce iyayenta Baki daya Christians ne yan asalin kujama ne na kaduna amma suna zaune a usasa cikin Zaria. basuda kudi hakan yasa tunda ta gama secondary school dinta bata sake komawa school ba dalilin da yasa tabi Anty dinta take Zuwa Don su samu abinci.

Kuskuren da Abba yayi shi ya jefa rayuwar iyalinshi baki daya cikin gagari wanda yake irreversible damage ne. Haka sukai ta soyayya ta gaske kowa yayi mamaki yadda abun ya kullu. Ranar sun rabu da ita yana tafe a hanya yana ta faman wassafo al'amura da yadda yake son su kasance, wani abokinshi Tajuddeen ya tare shi, Bayan sun gaisa suka cigaba da tafiya suna ta hira abunsu a haka har suka isa hostel da yake basuda lectures.

Adams da gaske kake Binta zaka aura.

Cak Abba ya tsaya da sheka musu black tea din hannunshi yace

Deen da gaske nake Wallahi, kasan nayi yan mata kalakala Amma ban taba hango wife material Irin yadda na gano a gurin Binta ba.

Ya fada Yana cigaba da sheka musu tea din tareda jin wani feelings yana growing akanta. Tajuddeen ya jima yana karantar yanayin sa kafin daga bisani yace

Adams da gaske kake

Wannan Karon Abba aje cups din yayi tareda dafa kafadar Tajuddeen yace

Deen ba yaudararta zanyi ba, Karka damu semester na karewa zan kaita gurin Alhaji.

Wani kallo Tajuddeen ya kara buga masa yace

Amma bakada hankali, Kai yanzu har Kana wannan mafarkin? Christian zaka aura? Am......

Da sauri Abba ya katse shi saboda Zuwa wannan lokacin ya fahimci inda maganar Tajuddeen ta dosa

Is there anything bad about that?

Shiru Tajuddeen yayi, Abba ya kara maimaita masa da karawa da

Banga aibu ba, saboda Allah ya bamu damar aurensu, saboda me kai kuma zaka haramta min.

Tabbas maganar Abbana gaskiya ce Allah ya baka damar aurensu, hakan yasa Tajuddeen fadin

Hakane, amma tunda yarinyar na sonka why not kasa tayi converting.....

Noooo! Me yasa? Karka kuma fada gaskiya kowa Yana da right yayi addinin da yake so, ta zauna addininta nima nayi nawa.

Haka kuwa ce ta faru don kuwa bai taba kawo mata maganar canja faith ba, itama anata bangaren Tana ganin in har ya matsa mata zata iya karyar karbar musulinci daga baya ta koma nata.

Kamar yadda yayi alkawari Yaje gidansu Don Seda ya tausaya musu saboda yadda yake ganin talauci futik a gidan, iyayenta sun ji dadi daya sanar musu basai ta karba musulinci ba, wannan yasa suka sha mamaki amma sunji dadi kuma sun amince idan ya shirya azo ayi aure. yana kammalla wannan semester wadda daga ita se final semester dinshi, kuma Tunda yazo Zaria sau uku kawai yaje Majiya shima ganin suna fushi dashi yasa ya tattara ya watsar dasu.

Cikin mota baki daya Binta is nervous, ta damu sosae saboda bata san yadda mutanen Abba zasu dauki maganar ba, Abba ne ya dinga kwantar mata da hankali yana sake jadadda mata ko da iyayenshi sunki amincewa zai gudu ne kawai a daura musu aure (kunji wani shagali kuma) wannan maganar yasa hankalinta ya dan kwanta. Seda suka Kwana a Kano cikin gida daya Wanda hakan babban Illa ne banda Allah ya kiyaye wani abu definitely zai iya shiga tsakaninsu amma Sede duk yadda Abba yakai ga tara yan mata hakan baisa ya zama womanizer ba.

Washegari kuwa haka suka dauki hanya zuwa Majiya wannan Karon shi kanshi a tsorace yake saboda yasan halin Alhaji ba Irin mutane bane da zaka zauna ka raina ba haka kuwa ya dake yana jadadda wa kanshi victory is his!

Da suka isa Rana Irin ta kwalle dinnan saboda lokacin rani ne, gashi wajen sha daya Zuwa Sha biyu na Rana ne, yana Sanye da suit ga uban Afro wanda Za'a iya kitsa Kan hannunshi dauke da briefcase se luggage din ita Binta wadda ta kokarta sosae ganin ta saka Lace zani da riga Amma babu mayafi, imagine wancan lokacin Kinje gaida surukai babu mayafi (let's all say you're dead) Haka suka isa gidan sarki wato Alhaji Samaila, bawan Allah ya kara tsufa girma ya kara kamashi, Yana zaune ana fadanci suka ji sallamar Abbanmu da Binta, Baki daya wuta ta dauke musu saboda yadda mamaki ke kwance fuskokinsu. Zama sukai aka gaggaisa Binta tana ta rabe rabe Don wannan ba muhallin ta bane, Alhaji wanda Baki daya idanunshi na Kan Binta yace

Adamu wannan fa?

Juya kanshi yayi ya dubi Binta tareda sakar mata murmushin karfin gwiwa yace

Allah ya kara Kwana dama ita ce wadda na kawo zan aura ita......

Bai karaso ba yaji baki daya zauren ya dauki salati wanda yasa shi rufe bakinshi tareda binsu da ido yana tunanin meye Don ya kawo Christian yace zai aura munafukai kawai. Dubanshi ya mayar Kan Alhaji wanda yake binsu da kallo kafin ya kira wani mutum dake tsaye yace

Kai ta dakin Amarya kace a bata abinci.

Haka yasa Binta ta bashi wadda Ke ta rarraba idanu gaba daya a tsorace take ji take inama bata biyoshi ba, aka kaita dakin Amarya wanda su a tunaninsu Irin ma'aikatan asibiti ne aka kawo kafin a Bata gurin zama. Kunsan mutumin kauye da kara haka aka dinga kawo mata abinci babu Wanda ya damu da religion dinta ba.

A fada Alhaji bai kara awa waiwayar Abba ba, ganin haka yasa sauran mutanen guntse bakinsu, shikam Yana zaune jiran gawon shanu har lokancin Azahar tayi kafin aka Mike zuwa massallaci, Yana idarwa ya dawo cikin fada baki daya ya kasa predicting abinda Alhaji zaiyi, shikam Alhaji ya cigaba da sabgoginsa har Seda aka tashi a fada kafin ya kama hanyar cikin gida, hakan yasa Abba take masa baya amma maimakon yayi masa maganar Binta se ya sako masa zancen karatun shi, hakan ya kara dagula masa lissafi.

Itakam Binta Baki daya ta rasa nutsuwarta gashi har lokancin Abba bai leko ta ba Sukuwa matan gidan suna tsakar gida suna hira Don zaman daki ba halinsu bane, a haka suka ji sallamar Alhaji hade da ta Abbanmu wanda ya jefa zukatansu a shakku Don sun manta Yaushe rabon da suji makamanciyar maganar tashi a ciki, hakan yasa Hajiya Azumi Bata rai Don Tana son nuna masa kuskurensa, Sede ko inda suke bai nufa ba Balle ta nuna bacin ranta yabi bayan Alhaji Har daki, seda ya zauna kafin yace

Adamu!

Abba ya dago idonsa ya zube kanta Alhaji kafin kuma ya maida kansa kasa yana ladabin karya

Kaje ka turo min 'yan uwanka Maza ina son ganinku Bayan isha'i

Dammm yaji faduwar gaba amma ya dake yace

Allah ya kara lapiya, wasu basannan ai

Murmushin takaici Alhaji yayi yace

Kai tunanin kowa irinka ne Wanda iyayenshi basu da daraja, to ka sani Baki daya sunxo hutun karshen shekara

Kanshi Abba ya Sosa ya mike Yana tunanin duk ranar da yayi kudi majiya Sede a labari Amma baiga dalilin kawo iyalinshi ya ajesu ba, haka kurum su tashi suna hi da ha , har Yaje bakin kofa Alhaji yace

Ka Turomin Binta da kuka zo tare.

Ficewa yayi Bayan ya amsa da to, seda suka gaisa da matan gidan suna ta tambayarshi Zaria kafin ya bawa Amarya sakon Alhaji sannan ya fice ba tareda ya lura da cewar hajiya Azumi Bata amsa gaisuwar shi ba.

Shatuuu ♥️

RAYUWARMU A YAU!Where stories live. Discover now