Page 71

662 22 0
                                    

SAHR-KHULAYD* written by *Seemby luff* 😘 Page *71* *Wannan shafin naki neh matar Yusleem (Miss Xoxo)* Thank you for everything, I heart you irin sosai d'innan ❤❤❤❤❤ Sai kusan 6pm suka shigo gari, bayan Khulayd yayi parking, a gajiye Mami da Mr Abeed suka shigo parlor, babu wanda ya tsaya neman abinci duk da cewa yunwan suke ji, d'aki kawai kowannensu ya nufa don watsa ruwa. Tunda taji horn daga gate ta daka tsalle daga saman gado ta diro kasa, gashin kanta duk a barbaje bata yi combing ba ta d'auki y'ar karamar gyale kawai ta rufa, da gudu-gudu ta fito daga d'akinta ta nufi stairs har ta kusa bangaje Mami dake zuwa d'akinta a gajiye, "Mamina ahlan, sannu da dawowa" kawai ta fad'a ta cigaba da sauk'owanta, tsayawa tayi a bakin kofan parlor'n inda ta tabbatar in ya shigo zai ganta, rungume hannu a k'irji tayi tana murmushinta mai kyau. Sai da Khulayd ya tsaya locking na motan tukun ya kamo hanyan shigowa, rik'e yake da car key yana wak'a yana spinning car key a iska, zuwa yayi zai shige parlor ya ganta tsaye tana ta faman murmushi, kaman tunda yake bai tab'a ganin mai kama da ita ba haka yayi, shareta yayi kaman ma bai lura da murmushinta bah ya cigaba da tafiyarshi, mamaki sosai Sahr taji, irin wannan shariya haka kaman ba shine ya tura mata da sak'o d'azu bah, da gudu tabi bayanshi tana "Jaan". Kusan sau uku ta k'irashi amma yak'i kulata, banza yayi da ita kaman baisan shi take k'ira da suna Jaan ba, sai spinning car key kawai yake yi yana tafiyarshi har ya kai stairs, shan gabanshi tayi ta rik'e dukka sides na stairs d'in kaman hannunta zai b'alle, tana kallonshi tace "Jaan, da kai fa nake magana tun d'azu, why are you ignoring me all of a sudden?" D'agowa yayi yana kallonta daga sama zuwa kasa, had'e rai yayi sosai, fuskan nan babu annuri kwata-kwata yace "Ki matsar min a hanya na wuce, as you can see na gaji sosai and I need to go freshen up" Sake k'ank'ame karfen stairs d'in tayi tana murgud'a bakinta "Not until ka fad'amin me yasa ka k'i kulani haka nan, nayi maka wani laifi ne?" Wannan karon babu yabo babu fallasa fuskarshi ya dubeta, yace "Haka kawai naga dama fah y'an mata, ko bani da freedom ne kuma yanzu? Get out of my way please" Narai-narai tayi da idanu, kafin kiftawar ido tuni hawaye sun fara wanke mata fuska, nan ta rushe mishi da kuka kuma tak'i matsa masa a hanya ya wuce, sai zuba hawayen keyi kaman an bud'e famfo, kawar da kanshi yayi gefe don ta bashi tausayi sosai, jin kukanta yake yi can kasan zuciyarshi amma he isn't ready to give up just yet, a hankali ya d'aura hannunshi a saman nata da nufin d'aukewa, daga shi har ita sai da suka feeling wani electrification, basarwa Khulayd yayi kamar bai ji ba ya d'auke hannun nata daga kan karfen stairs d'in, bata wani k'ok'arin hanashi ba saboda wani kasalan da ya sauk'ar mata, janye jiki tayi gefe guda, shi kuma yayi wucewarshi ko kallonta bai sake yi bah, sunkuyawa tayi a nan gurin ta rungume jikin stairs d'in tana kukanta sheshsheka, sai da tayi mai isanta tukun ta mik'e ta wuce d'akinta. Yana shiga d'aki, gaban mirror ya nufa ya ajiye makullin motan dake hannunshi da waya, undressing kanshi yayi daga shi sai gajeren wando da singlet ya zauna bakin gado, ciwo kanshi keyi saboda hanyan sam babu dad'i, gargada yayi yawa kuma shi bai saba bin irin wannan hanyan bah, dafe kanshi yayi da dukka hannayenshi biyu ya lumshe ido, ita yake gani lokacin da ta rushe mishi da kuka, murmushi ne ya sub'uce mishi yana girgiza kai, a fili yace "Crying crying precious, can't wait to have u all for myself" A nan inda yake zaune, idanunshi a lumshe ya fara imagination, wai gashi ga Sahr akan gado d'aya, a farkon daren aurensu, mik'ewa yayi da sauri kamar an mintsileshi ganin zai b'ata lokacinshi akan wani imagination, fad'awa toilet yayi ya sakar wa kanshi shower, still yayi a karkashin shiwer'n yaayin da ruwan ke sauk'a tun daga saman kanshi har tafin kafanshi, ya d'au lokaci a haka tukun ya tsala wanka sannan ya d'auro alwala, fitowa yayi d'aure da towel a k'ugunshi, yana towel drying suman kanshi da d'an k'aramin towel, gaban mirror ya nufa ya shafe kanshi da hair creams d'inshi sannan yayi combing, bai damu da ya shafa mai a jikinshi ba saboda yanayi na zafi da ake ciki, perfumes d'inshi kawai yayi spraying all over sai dad'ad'an kamshi ke tafi na turaruka daban-daban, wardrobe ya nufa ya ciro jallabiya mara nauyi ya zura sannan ya d'auko darduma a saman side drawer ya shimfid'a, ya tada kabbaran sallah. Asr da yayi missing saboda suna kan hanya ya fara gabatarwa, sannan ya mik'e ya gabatar da Magrib, ya d'auki tsawon lokaci zaune kan darduman kafin daga bisani ya mik'e, gaban mirror ya nufa ya d'au wayanshi ya fito. Hayaniyansu daya ji a dinning area ne ya tabbatar mishi cewa duk suna wurin, kai tsaye shima dinning area ya nufa ya gansu duk a zazzaune, kujeran dake kusa da na Mami ya ja ya zauna yana ta shan k'amshi, fuskarshi sam babu annuri, shafa gefen fuskarshi Mami tayi tace "Yaya dai son naga duk baka walwala? Duk gajyan ne or is something bothering you?" Murmushi yayi, kamar baison magana yace "Babu komai fa aunt, kaina ke ciwo but nasha magani, I'll soon be okay." Sahr ce tayi serving abinci yau, a hankali take bin plate na kowa tana zuba abinci, plate na Khulayd shine k'arshen wanda ta zuba abinci, tana zubawa tana kallonshi da tausayinshi fal zuciyarta tunda yace kanshi na ciwo, gaba d'aya hankalinta baya kan abunda take yi, batayi aune bah sai ji tayi serving spoon dake hannunta ya sub'uce ya fad'i kasa, da sauri taje kasa itama da nufin d'aukowa, ta kai hannunta kenan shima Khulayd ya kai nashi da nufin d'ago mata dashi, karaf ya rik'e hannunta instead of serving spoon d'in, kusan a tare suka d'ago suna kallon juna with so much love ne passion, sun dad'e a haka kuma yak'i sake mata hannu, hawaye ya gani suna zubowa daga idanunta suna gangarowa kan kumatunta, bai san lokacin da ya saki hannunta ba, sai ji tayi yana share mata hawayen shima kamar zaiyi k'walla, yana share hawayen wasu suna zubowa, d'ago hab'arta yayi yana kallonta, idonta da hawayen itama take kallonshi, tab'e baki yayi ya turoshi kamar yadda yara sukeyi idan suna son yin kuka, girgiza mata kai ya shiga yi alamar ta daina, a hankali yayi whispering mata "Am sorry precious" Murmushi neh ya sub'uce mata bata san lokacin bah, da kanta ta shiga share hawayen tana jan hanci tace "Am sorry too Jaan" "Ki share hawayenki, kinsan I hate to see your tears... Am always here for you okay?" G'yad'a mishi kai ta shiga yi tana jin dad'i sosai, basuyi aune bah sai jin muryan Mami sukayi tana cewa "Wai ni me kukeyi neh tun d'azu haka? Wani serving spoon d'in kuke k'erawa ne? don naga kamar d'ago wannan na baku matsala" Da sauri Sahr ta d'auki serving spoon d'in ta mik'e, wani ta d'auko ta cigaba da zuba mishi abincin dashi. Koda suka kammala dinner'n, Mami, Mr Abeed, Neenah da Nailah duk suka d'unguma zuwa parlor, Khulayd da Sahr kam suna nan zaune wai da sunan suna cin abinci, sai juya cokali kawai suke yi suna cakud'a abincin, kusan a tare suka ture plates d'insu, tura kujera Khulayd yayi zuwa baya ya mik'e da nufin komawa parlor shima, da sauri ta kamo hannunshi ya juyo yana kallonta, girgiza kanta take yi tace "Kar ka tafi please Jaan, stay for my sake, ban gaji da kallonka ba" Bai ce da ita komai bah, ya koma ya zauna kawai, tagumi tayi da both hannayenta tana kallonshi, tsawon mintuna biyu tayi tukun tace "Jaan, ka dad'e baka ce kana sona bah, its been long, ka fad'a inji don Allah" "Precious wallahi ak'waiki da son rigima, kin san fa koda ban fad'a bah you know I do, with the whole of my heart" Mik'ewa tayi ta fara bubbuga kafafunta a kasa, tana "Umm umm, nikam banason wayo, I just want to hear u say it, please Jaan" Ta karashe maganan kamar zatayi kuka, ganin da gaske take fa kukan zatayi don ya santa sarai, akan k'ank'anin abu yanzu sai ta fashe mishi da kuka, bai san lokacin da yace "Ina sonki precious, I love you irin sosai d'innan" bah Kawai sai gani yayi ta fashe da dariya, har da y'ar tsallenta, kallonta kawai yake yi baki bud'e babu ko kiftawa, shi dai duk abunda tayi yana burgeshi, jin sonta yake yi yana ratsa jini da b'argonshi, a fili kuwa yace "Drama Queen." © *SEEMBY LUFF* 😘

Sahr-Khulayd Where stories live. Discover now