Page 59

671 42 1
                                    

Page *59*⚜

    A fusace Mami ta karaso gaban Neenah without uttering a word da iya karfinta ta wanke fuskanta da wani mari mai rud'a mutum, a rud'e Neenah ta dafe kuncinta tana ji kamar tsinke namañ fuskanta akayi don zafi ta d'ago kai tana kallon Mami tace "Mami me nayi kuma kika....." Bata karasa abunda takeson fad'a bah ta sakejin saukan wani marin a d'ayan b'angaren fuskanta, dafe kuncin ta sakeyi nan take hawaye ya fara wanke mata fuska, cikin tsiwa tace "wai ni Mami me nayi ne kam kiketa marina continuously without asking me or even allowing me to explain? Ni a iya rayuwata da girmana you've never raised your hands on me talk more of hitting me mom, kamata yayi ki tambayeni meke faruwa ko kuma meya kawoni d'akin Mr Omair, koda ma baku zo nan yanzu bah I was going to tell u abunda ke faruwa da kudirin Mr Omair a kaina" nan take ta fara kokarin juya maganar zuwa wani direction. Sahr ce tayi interrupting d'inta cikin b'acin rai tace "meye Mr Omair yayi kuma this time Adda Neenah? Yau d'in ma yayi forcing d'inki zuwa d'akinshi and he's trying to rape u again right? Gashi u look very sexy in this dress, did he also forced u to wear it? C'mon ki fad'a mana Adda Neenah". Hard'e hannu Sahr tayi kan kirjinta itama tana jira taji me Neenah zata fad'a kuma yau, kuka Neenah ta hau yi babu kakkautawa tace "he he he threatened to fire me from work idan ban bashi had'in kai bah, kuma yace dama tun farko he never loved kid sister ni yake so, ni kuma I so much love my job bazan iya barin OGC bah dats y I agreed" ta matso gaban Mami dake tsaye tun d'azu speechless ta rike hannayenta dukka biyu tace "believe me mother, Wallahi am saying d truth, threatening d'ina yayi" fuske hannu Mami tayi daga rikon da tayi mata ta sake sauke mata wani marin a karo na uku, idanunta sun kad'a sunyi jajur zuciyarta na tafasa ta kalli Neenah a cikin ido tace "this is for lying to my face Neenah, am very disappointed in you, d'abi'arki is very disgusting Wallahi. Yau d'innan kin tabbatarmin da cewa nayi hasarar tarbiyyan dana sha wahala ina baki da 'yan uwanki, all dis years da mahaifinku ya bar duniya nasa effort sosai wajen ganin cewa kun samu ingantacciyar tarbiyya, I raised you girls single handed ba tare da taimakon ko da 'yan uwan mahaifinku bah amma shine sakayyan da zakiyi min?" Hawaye masu zafi neh suka fara zarya a kan kumatunta taci gaba "Wallahi nayi dana sanin haihuwarki Neenah, how I wish da b'arin cikinki nayi mutane su gaisheni bayan wani lokaci in manta da yafi min alkhairi".
     Da sauri Khulayd ya karaso gaban Mami ya d'aura hannu akan bakinta yana girgiza mata kai yace "No aunt, please don't say this, abunda kike cewa bazai kareta da komai bah saidai ya b'ata mata rayuwa, u re a mother aunt u shouldn't be saying this, ni dai nayi haka neh don inyi proving innocence d'ina a gabanki of which I did, bazan tab'a iya jurar ganin zargina cikin kwayan idonki bah amma kamata yayi kiyi mata addu'ar shiriya ba na tab'ara bah" d'aga mishi hannu tayi alamar ya dakata tace "no son, Wallahi nayi dana sanin haihuwarta, she's a disgrace to this family" daga haka bata sake cewa komai bah ta juya tayi ficewarta daga d'akin.
       Taafi Sahr ta farayi tana murmushi tana yiwa Neenah kallon sama da kasa tace "Well done Adda Neenah, well done. Lallai kin iya juyarwa mutum tunaninsa, kinyi nasarar cusamin zargin wanda nakeso a cikin zuciyata, kinsa ina yi mishi kallon macuci kuma mayaudari alhalin sam ba halinshi baneh, abunda kawai kika kasayi shine cire sonshi daga zuciyata saboda the bond is very strong that it cannot be broken this easy, da har ina tunanin sadaukar da soyayyata ga 'yar uwata domin a ganina u love him more than I do but kin san me? U don't deserve this, c'mon Adda Neenah am your blood sister fah, how could u even think of doing this to me, why??" Itama ta kare maganar tana hawaye. Kallon Neenah Khulayd keyi tun d'azu a kyamace yace "well, am so sorry sexy Mrs Mukhtar it was all a setup and am happy it worked, at least yanzu za'a daina zargina kan abunda ban aikata bah kuma ki sani, koda babu riga na ganki bazan tab'a jin sha'awarki bah coz I hate u so damn much". Juyawa Neenah tayi tana hararan Sahr na d'an wani lokaci don ta kasa cewa komai sannan ta juya kan Khulayd shima tana cizan leb'b'e, a sanyaye ta juya ta fita daga d'akin.
*Sahr-Khulayd*
    Neenah na fita Khulayd ya juya da barin kallon Sahr, a zuciyarshi kuma yana jindadi at least yanzu precious d'inshi zata daina fushi dashi and everything will be back to normal between dem again. A hankali Sahr ta tattako ta tsaya dap bayanshi, so takeyi tayi tapping d'inshi a kafad'a amma da zarar ta kai hannunta sai kuma ta sake saukewa, sau uku takeyin haka daga karshe kawai taja dogon numfashi tana murmushi kamar yana ganinta, cikin 'yar siririyar muryanta tace "Jaan" shiru yayi mata kamar baisan dashi takeyi bah, kusan sau 4 take kiranshi amma yayi banza da ita, murmushin ta sakeyi don tasan dalilin kin kulata da yayi laifinta neh tace
"Jaan am sorry, Wallahi situation dinne yai min tsauri and I've never experienced this my whole life, gabad'aya tunanina ya jagule bansan wanda zan yarda dashi a cikinku bah, ban tab'a yarda cewar Adda Neenah zatayi downgrading kanta har zuwa level d'innan bah, ban tab'a zaton zatayi kokarin kwace min farin cikina bah duk da cewa Adda Nailah taso ta ankarar dani, haka kuma kaima ban tab'a yarda zaka iya kwana da blood sister na ba. Try and understand me Jaan wallahi duk da faruwan wannan abun daidai da rana d'aya sonka bai tab'a raguwa a zuciyata bah, am having the best experience of new life with u Jaan and u re the best thing that has ever happened to me, kayi hakuri da rashin yarda dakai da nayi nasan na bata maka rai, I knw I shuld have believed u wen u said u didn't do it saboda banga komai a idanunka bah sai zallar gaskiya, please forgive me Jaan, please" ta kare maganar tayi narai narai da ido kamar zatayi kuka tana son jin abunda zai ce amma duk maganganun data fad'a baisa ya juyo bah haka kuma bai kulata bah, hakan yasa kawai ta fashe mishi da kuka don shine iyakan option da take da.

Vote
Vote
Vote
Seemby luff 😘

Sahr-Khulayd Where stories live. Discover now