Page 62

694 32 0
                                    


© *SEEMBY LUFF* 😘 ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff* 😘 Page *62*⚜ Mik'ewa both Khulayd da Mr Abeed sukayi cikin tsananin mamakin furucinta, "Barrister Zayyad" Khulayd ya maimaita yanajin zuciyarshi yana tafasa, "Yes, barrister Zayyad, and d reason why he didn't asked for ransom is yanason kwana da ni neh kawai" da fashe da tsananin kuka tace "he tried to rape me sau uku" wannan karon har Mami saida ta mik'e tsaye, da karfi Khulayd yace "What? Rape fah kikace" gyad'a kai kawai Sahr tayi batace komai bah hawaye na cigaba da bin kuncinta, da gudu Khulayd ya haura sama jim kad'an ya dawo rike da car key bai ce dasu komai bah ya nufi hanyar waje, Mr Abeed yace "and where do u think u are going in such a hurry?" Khulayd bai ko kulashi bah ya cigaba da tafiya, a karo na biyu Mr Abeed yace "I asked u something" huci Khulayd yakeyi bayajin zai iya cewa komai, da kyar ya iya tattaro 'yar nutsuwa yace "gidan Zayyad zaani" "kayi masa meye" cewar papanshi "bazaka d'auki law a hannunka bah coz if u do kaima zaka zama mai laifi, ka bar masu aiki suyi aikinsu". "But dad how dare he, how dare he to even think of coming close to my woman, she's mine dad, she's mine baxan tab'a kyaleshi ba wallahi, idan na had'u dashi I'll kill him wit my hands aswear" kusa dashi Mami ta matso tare da dafa kafad'anshi tace "calm down son, nasan yadda kakeji amma kamata yayi mubi komai cikin hankali, kana fa jinta tace there is a woman involved, idan ka kashe shi how re we supposed to find out whom she is... Come and sit" Mami ta jawo hannunshi ta dawo dashi cikin parlor'n sannan ta zaunar dashi, wurin fridge ta nufa ta bud'e ta ciro chilled water na faro ta tsiyayo mishi a cup ta kawo, mik'a mishi tayi tana kallonshi batace komai bah yasa hannu ya karba, saida yasha kusan half d cup sannan ta koma ta zaunah duk kowa yayi shiru a cikin parlor'n. Tunda Mami ta zaunar dashi Sahr ta kafeshi da idanu, bata tab'a jin sonshi irin yanda takeji yau bah, gaba d'aya komai ya koma mata kamar sabo, jikinshi neh ya bashi ana kallonshi ya d'ago kai a hankali da jajayen idanunshi ya zuba cikin nata, batayi kokarin sauke kanta bah wannan karon itama tana kallonshi a cikin ido, sun d'auki lokaci a haka kuma tun d'azun basuyi noticing Mami na kallonsu bah, its like sun ma manta akwai Mami da Mr Abeed a parlor'n, Nailah ma kallonsu take tana murmushi kafin daga bisani ta mike taje gaban Sahr tace "kid sis xo muje muyi wata 'yar magana" bata tsaya jin me xatace ba ta ja hannunta suka wuce. Sai a sannan Khulayd ya dawo hankalinshi yana d'ago ido sai a cikin na Mami, gabad'aya kunya ya rufeshi don yasan tabbas ta gansu, mik'ewa yayi shima yana 'yar mik'a da hamma yace "Aunt, papa ni zanje in kwanta, am feeling sleepy sosai" "kodai kana korar kunya da hauka bah" cewar Mami, nunawa yayi kamar baisan inda zancenta ya dosa bah yace "korar kunya da hauka kuma aunt, me nayi neh?" Saida Mami tad'an murmusa tukunna tace "now u re pretending kamar bakasan me nake cewa bah, I saw u two ai" sosa keyanshi yayi da key dake hannunshi yama rasa me xai fad'a, Mr Abeed dake zaune tun d'azu yana kallonsu cike da farin cikin zamantakewarsu yace "I can see my son is so much in love, nayi maka alkawarin muna gama magance wannan matsalar xamu fara shirin aurenku tunda ma abun yaxo da sauki, na gidah neh" Khulayd baisan lokacinda ya karaso gaban Papanshi ya rungumeshi bah, harda pecking d'inshi a kumatu yace "thanks dad, u re d best" itama Mamin zuwa wurinta yayi pecking forehead d'inta yace "nyt aunt" daga haka ya haura sama cike da farin cikin furucin mahaifinsa. A fusace Neenah tabar parlor'n har tana jan tsoki, sam maganar da akayi bai mata bah, bama wannan bah, babban tashin hankalinta shine tasan cewa idan akayi nasaran cafke Barr Zayyad tofah itama asirinta zai tonu, tafiya kawai takeyi tana tunanin mafita. Kasa bacci tayi a daren sai juyi takeyi a saman gado tana sakawa da kuncewa daga karshe ta yanke wani shawarar da tabarwa zuciyanta ita kad'ai har bacci ya d'auketa. Nailah da Sahr suna isa d'aki suka zube nan kan two seated sofa dake gefe, kallonta kawai Nailah keyi batace komai ba bayan ita tace xasuyi wata magana, kallon neh ya ishi Sahr tace "Addah Nailah me nayi kike kallona haka bakya ko kyaftawa, I tot u said zamuyi magana neh, y ain't u talking" Nailah tace "dole in janyeki daga parlor'n mana kid sis, mamaki fah kika bani" cikin rashin fahimta Sahr tace "mamaki kuma Adda Nailah, toh menayi na mamaki kuma" har fuskanta ya fara komawa na tausayi, babu alamar wasa a fuskan Nailah sam tace "wai ma yaushe kika koma marar kunya neh kam, gaba d'aya kin biyewa Ya Khulayd ya cire miki wannan kunyar da kike dashi, I had to take u away saboda irin kallon juna da kukeyi kamar zaku cinye kanku kun ma manta Mami da Uncle suna parlor'n, shin kuwa ko kinsan Mami na kallonku. Wai ma tsaya, yaushe kika koyi kallon cikin idon mutum har na tsawon lokaci haka neh" Nailah ta tambaya tana wondering, "soyayya ce (littafin Maryam Abdulrahman, u guys should try reading it saboda its interesting and educative) ta koyamin Adda Nailah" tana gama fad'in haka ta b'oye fuskarta a cikin hannunta cike da kunya don bata ma san sanda ta fad'i haka bah, "iyye, lallai yarinyar nan kinfa girma, a'a u ain't d kid sister I used to knw wannan kam babba ceh, karki damu burinki yana gab da cika, everything will soon b over Insha Allah" cewar Nailah, daga nan suka d'anyi sisterly hiransu, da hamma Nailah ta mik'e tace "ba naje na kwanta kid sis, Allah bacci nakeji" Sahr tace "aikam kinajin bacci don gashi har idanunki sun k'ankance, tnks 4 ur tym" sunkuyowa Nailah tayi ta sumbaci Sahr a goshi sannan tace "nyt kid sis" tana magana tana tafiya, cikin muryan bacci itama Sahr ta amsa mata da "nyt", bayan fitan Nailah Sahr ta sauya outfit d'inta zuwa nighty ta haye saman gado, addu'ar kwanciya tayi daga bisani ta kashe wutan d'akin ta kwanta. Khulayd na komawa d'aki baiyi tunanin kwanciya bah, bathroom ya nufa ya d'auro alwala ya dawo cikin d'akin, darduma ya shimfid'a yayi nafila raka'a biyu sannan bayan ya idar yayi addu'o'inshi yana mai godiya ga ni'imomin ubangiji, ya dad's zaune kan darduman har saida ya fara jin nauyayyen bacci tukun ya mik'e ya koma kan gado ya kwanta, tunane-tunane yayi tayi kan irin abubuwan da suke faruwa, a take ya zama moody daya tuna maganar precious d'inshi cewa Barr Zayyad yaso ya mata fyad'e, kamar an mintsileshi ya mirgina zuwa d'ayan side na gadon inda landline ke ajiye, d'agowa yayi ya jingina da jikin gadon sannan ya d'auko landline d'in ya ajiye saman cinyarshi ya fara dialing digits din d'akinta. Baccinta har ya fara nisa taji ringing, mirginawa itama tayi zuwa other end na gadon idanunta a rufe ta mika hannu ta d'auko, karawa a kunnenta tayi da wahalalliyar murya tace "Hello" Gabad'aya sai yaji veins d'inshi sunyi weak, nan take muryanta ya saukar mishi kasala da kyar ya iya cewa "precious" a lokacinda muryanshi ya doki kunnenta sai ta nemi baccinta ta rasa, gyara kwanciyanta tayi sosai sannan tace "Jaaaan, bakayi bacci bah" "Precious ya za'ayi in iya bacci when I can't get u off my thoughts" "Nima da tunaninka na kwanta Yayana" ta fad'a a takaice, saida ya d'anyi shiru kafin yace "about dazu, kince Zayyad tried to rape u, did he in anyway....." Bata bari ya karisa fad'in abunda zai ce bah tace "Shhhhh Jaan! Babu abunda ya fara coz nayita addu'an Allah ya kareni idan har ina ajiye kaina wa mijina kuma don shi nakeyi and he did, he protected me from his evil plans, Ya Khulayd ni takace kai kad'ai, I promise". Wani nauyayyen ajiyan zuciya Khulayd ya saki baima san me zaice mata be coz he's overwhelmed, "thank u precious, thank h so much" kawai ya iya fad'a, a hankali tace "now u can sleep don na tabbata abunda ya hanaka bacci kenan" 'yar murmushi yayi yace "not until kin fad'amin abu mai dad'i", rufe idanunta tayi don muryanshi yasa taji wani electrification daga kai zuwa tafin kafa, cikin wani romantic voice tace "I love u Jaan, so much" ta d'anyi shiru, can tace "Muahh, a kumatu fah amma" yadda tayi maganan serious ta bashi dariya sosai, da kyar ya iya controlling dariyan yace "um um, nidai a lips nakeso ayi min, in kuma baza'ayi ba shikenan ko wannan ma bazan karb'a bah" da sauri tace "no way, nyt" tayi hanging up tana dariya, shima dariyan yakeyi a chan, that night dai sun kwanta full of each other's thoughts. Posted on Thursday Date: 05-04-2018 Time: 01:02am Written by: Seemby luff😘

Sahr-Khulayd Where stories live. Discover now