Page 61

677 29 1
                                    


© *SEEMBY LUFF* 😘 ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff* 😘 Page *61* ⚜ Saida sukayi kukan mai isarsu kafin Sahr ta breaking hug d'in tana goge fuskarta ta sauka daga kan gadon tayi waje, tana komawa d'akinta tayi zaman dirshan bakin gado, gabad'aya bata jin dad'in yanda zaman gidan ya koma kamar gaba akeyi, tadai san cewa abu mai kamar wuya neh ta kyale Khulayd ma Neenah after all what happened, zaiyi matukar wuya ta iya rayuwa babu shi, komawa tayi ta kwanta tana tunane-tunane har bacci ya d'auketa. *Monday, 04:20pm* Dai-dai karfe 04:20 na yamma jirgin yayi landing cikin airport d'in, Khualyd da kanshi yazo d'aukan papan shi, tsaye yake a arrivals yana ta dube-dube cikin passengers da suke saukowa bayan kamar minti biyar ya hango Mr Abeed yana saukowa daga matakalan jirgin a hankali cikin takunshi na kasaita kanshi a k'asa har saida ya karasa saukowa tukun ya d'ago kanshi, cikin hanzari Khulayd ya d'an d'aga hannu kamar yana waving, Mr Abeed na ganinshi ya saki murmushi yana kallon d'anshi ciki da soyayya, shima Khulayd d'in murmushin yakeyi ya karasa yayi hugging papanshi, rikeshi Mr Abeed yayi yana d'an shafa bayanshi a hankali kusan seconds goma suka d'auka a haka kafin suka sake juna, "Welcome dad" Khulayd ya fad'a lokacinda suke kokarin karasawa inda ake sauke luggage, " Thanks son" kawai Mr Abeed daga nan suka d'auko luggage d'in suka wuce wurin mota, a baya driver ya b'udewa Mr Abeed ya shige Khulayd kuma yana kokarin bud'e gidan gaba ya zauna, "come and sit next to me" Mr Abeed ya fad'a yana nuna mishi gefenshi, ajiyar zuciya Khulayd ya saki sannan ya mayar da kofan front seat d'in ya rufe ya koma baya ya zauna kusa da mahaifinshi. Shiru neh ya wakana a cikin mota na d'an wani lokaci kafin daga bisani Mr Abeed yace " so, me ake cikine game da maganan abduction din, shin kun zaunah da ita yarinyar ka samo wani information as to who is behind it?", girgiza kai Khulayd yayi alamar a'a yace " na d'an bata tym ta huta neh dad, naga kamar it isn't ryt in fara bincikenta after all what she went through, kaga yanzu ko wanda ya aikata abun zai sakankance coz zaiga kamar we've let go of it sai muzo mishi a bazata... That's wat I thought". "Umm, not a bad idea" cewar Mr Abeed sannan yace " we'll talk about it anjima after isha' prayer" Khulayd yace "hakan ma yayi" haka suka rika hira har suka isa gida. Nailah da sahr tun bayan azahar suke kitchen suna ta faman girke-girke bayan sun gama suka jere komai kan dinning suka koma don kimtsa kitchen din, jin tsayiwar mota yasa sahr ta wullar da mopper dake hannunta ta fice da gudu har ta kusa fad'i ta nufi harabar gidan, isowarta yayi dai-dai da tsayuwar motan a parking lot tayi saurin bud'e b'angaren da uncle d'inta ke ciki ta fad'a motan kawai sai a jikinshi tana "oyoyo sweet uncle", rungumeta yayi yace "oyoyo Mami's little princess, har yanxu kina nan da halin naki koh? Don't u knw you re now a grown up" mak'ale kafad'a tayi tad'an tura bakin tace "I knw manah uncle, amma a wurinku ai am still a baby koh" dariya sosai yayi yad'an ja kumatunta yace "shegen wayon tsiya ne dake 'yar autar Mami... Of course u re my baby, our baby". Nailah dake tsaye a bayanta tace "toh malama ai saiki matsa muma mu samu damar yi masa barka da zuwan koh, ko uncle d'inki ke kad'ai ne aka fad'a miki" ta kare maganar tare da janyota zuwa gefe, da shagwab'a Sahr ta fara bubbuga kafafunta a kasa tana "uncle ka ganta bah", dariya sosai Mr Abeed yayi wannan karon yace "duk kuyi hakuri ai zan fito kuma ba ina nan bah, we'll all spend some quality time together" Sahr bata sake cewa komai bah ta rungume hannayenta a kirji tayi narai-narai da ido kamar zatayi kuka tana kallonsu, fitowa Khulayd yayi ya tsaya a gefenta yace " ni baza'ayi min oyoyon baneh, ko papa kawai kika gani a nan" kin kulashi tayi tayi banza dashi, murmushi yayi yace "ni ne fa jaan d'inki kike banza dani, yanzu idan na rama anjima you'll start crying" nan na batace komai bah, d'auke kai Khulayd yayi zuwa gefe yace "zan rama neh" babu shiri tace "Ya Khulayd fa bada kai nake fushin bah, da uncle da Nailah nakeyi kaga sun kyaleni sunje gefe suna ta firansu" kin kulata yayi shima ya d'auke kai, rike kafad'anshi tayi ta d'an girgizashi tace "Ya Khulayd am sorry", b'ata rai sosai yayi kamar da gaske ya juyo baya ko murmushi yace "and what happened to 'Jaan'?" Sai da ta yi ajiyar zuciya tukun tace "am sorry Jaan" ta rike kunnenta, Khulayd ya sake fuska babu yabo babu fallasa yace "zanyi hakuri amma akwai condition", d'agowa tayi tana kallonshi tace "which is?" Kamar bazaiyi magana bah kafin daga bisani yace " kiyi pecking na" babu shiri Sahr ta zaro ido waje kamar zasu firfito tace "a nan?" Ko a jikinshi yace "a nan manah kuma yanxu" turus ta tsaya kallonshi tama kasa cewa komai kawai kallon mamaki kawai take mishi, daya ga bata da niyyar yin abunda ya bukata yace "don't just stand there staring at me, kiyi kawai ko kuma inyi fushi dake neh yarinya" suna kan haka Mami ta fito harabar gidan itama da murmushi tana kokarin b'oye duk damuwarta kada d'an uwanta ya gani a fuskarta, tun fitowarta ya kafeta da idanu ganin yanda ta rame tayi fayau da ita kamar wacce tayi ciwo har ta karaso bai d'auke idanunshi a kanta bah, tun kafin tace wani abu yace "kinyi jinya neh my dear sister? Naga u look palled kuma kin rame compared to d last time I came, ko akwai wani damuwa neh da kika k'i fad'amun?" Murmushi tayi tace "ai saika bari mu karisa ciki tukun kayi min wad'annan tambayoyin, yanzu dai u re highly welcome, nasan ka gaji don haka mu shiga ciki so you'll freshen up and eat your food okay, den komai sai ya biyo baya" "I asked you something kuma kina maganar cin abinci? Just look at yourself sis, u don't seem alright, ki fad'amun meke damunki?" Mr Abeed ya sake tambaya a karo na biyu, jan numfashi Mami tayi ta fusgar tukun tace "toh Yaya tunda u insist zan fad'a maka, na d'anyi zazzab'i neh na kwana biyu but am feeling much better now coz my son here has taken a very good care of me" ta kare maganar tare da shafar gefen fuskan Khulayd, ajiyan zuciya Mr Abeed yayi yace "are u sure kinji sauki?" Tace "am very sure Yaya" daga haka suka d'unguma zuwa ciki. Koda suka shiga Mr Abeed baiga Neenah bah hakan yasa ya tambaya "where is my favorite girl, I haven't seen her tunda naxo" kusan sau uku ya tambaya amma amsar da ake bashi d'aya neh "bamu san ina ta shiga bah" bai kawo komai a ranshi bah ya wuce masaukinsa kawai don hutawa. *After Isha' prayer*❤ Kowa ya hallara wurin dinning don cin dinner amma banda Neenah da tun d'azu ta sa kafa ta fice daga gidan kuma har yanzu bata dawo bah, Mr Abeed ya b'ude baki da niyyar sake tambayansu inda taje tun safe saidai baima yi maganar bah yaji muryanta da ihu tana "uncle" tayi saurin karasowa ta rungumeshi ta baya duk da yana zaune, fad'ad'a murmushi yayi ya riketa shima yana "my favorite girl, ina kika shiga neh naketa tambayarki tun d'azu, meyasa kika jira har war haka a waje" kujeran kusa dashi taja ta zauna tare da riko hannunshi tace "uncle office name nd inada ayyuka dayawa akan desk d'ina shiyasa naga yakamata in rage, kasan yanda aikin namu yake balle kuma being a secretary to d CEO is a very difficult task" ta kare maganar tana kallon Khulayd, harara ya wurga mata babu shiri ta d'auke idonta a kanshi, cikin jindad'i Mr Abeed yace "this is why u re my fev, kina bawa aikinki muhimmanci... Keep it up" "awwn thanks uncle" Neenah ta fad'a daga haka Sahr ta mik'e tayi serving abincin kowa ya fara ci, babu wanda ya sake cewa komai. *After dinner* Duk suka koma parlor bayan sun kammala cin abincin, Khulayd da Papanshi suka zaunah a couch d'aya, Mami da Sahr ma akan d'aya sai Neenah da Nailah kuma kan different couch. Mr Abeed yayi gyaran murya yana kallon Sahr yace "little princess muna sake godewa Allah daya kwaceki a hannun mugayen mutanen da suka saceki and we re happy u came back home safe and sound, mun barki neh iya tsawon wannan lokacin don ki huta kuma ki cire abun a ranki kafin mu fara bincike, toh Alhamdulillah yanxu nasan kin samu isashshen hutu don haka lokaci yayi da zamuji ta bakinki, ko kinsan wanda ya aikata hakan a kanki?" Gyad'a kai Sahr tayi jikinta duk ya fara rawa don bata tab'a tsammanin za ayi mata tambayar nan yanxu bah, ita a zatonta komai ya wuce, a hankali tace "na san wanda ya aikata hakan a gareni Uncle saboda bai tab'a b'oyemin kanshi bah dai-dai da rana d'aya" duk hankalin kowa ya koma kanta barin ma Neenah da tunda Sahr ta fara maganar zuciyanta yake bugawa, "ko kinsan dalilin da yasa basu bukaci kud'i (ransom) bah iya lokacinda suka rikeki?" Cewar Khulayd "Bana tunanin cewa suna bukatar kud'i neh, akwai wani manufa da kudirin da suke dashi a kaina saboda sau da dama yakan zo min da wannan kudirin" cewar Sahr, shiru tad'anyi nad'an wani lokaci kafin taci gaba "I always heard him talking to someone whom I believed to be a lady on d phone, saidai bansan ko wacece bah amma inaji a jikina akwai bakinta a ciki" Mr Abeed have "Masha Allah, ko zaki iya sanar damu wanene? Idan kuma saninshi a fuska kawai za'a iya kiran mai zane idan yaso saiki kwatanta masa ya zana", da sauri Sahr tace "no, we don't need that uncle, nayi mishi kyakkyawan sani don ko a mafarki bazan tab'a manta fuskarshi bah kuma babu wanda yake zaune a parlor'n nan da bai sanshi bah" duk suka fara kallon juna kowa yana wondering waye wannan mutumin, Neenah kam yanxu bugun zuciyarta ya karu fiye da d'azu, kamar zai b'alle k'irjinta ya fito, Mami ce tayi karfin halin tambayan Sahr "wanene haka princess, kince duk nun sanshi... Who could that be?" Kamar bazata ce komai bah, maganar ya zo musu a bazata yayinda tace " *BARRISTER ZAYYAD NEH*" Posted on Monday Date: 02- April- 2018 Time: 09:00pm Writer: Seemby luff😘

Sahr-Khulayd Where stories live. Discover now