ONE

5.5K 282 5
                                    


🏵🏵🌸🏵🏵
       _RAYUWARMU A YAU!_
🏵🏵🌸🏵🏵
                          

                             *ONE*
✍🏻Ayshatuuu

Shatuuu095@wattpad

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
_United we stand and succeed our ambition is to entertain and motivate the mind of readers_

Bansan ta inda zan fara baku labarin rayuwata ba, Abu daya kawai na sani ni HASSANA nasha gwagwamarya kuma naga rayuwa wadda nasan har na koma ga Allah bazan daina gani ba Sede kullum ina cikin addu'a Allah ya kawo min komai cikin sauki. Na kasance kaf gidanmu ni ce wadda Keda duhun fata kasancewar baki daya matan Abbana farare ne yasa dukansu suke biyo complexion dinsu, ni daya ce nayi karambani na biyo dangin mahaifina wanda sune bakake. Ban fiye tsayi amma idan da aldaci baza'a sakani jerun gajeru ba, banda kiba se hips wannan wanda kukasan kullum shi nake roka gurin Allah, banda boobs sosae daidai misali, fuskata doguwa ce kuma komai na ciki matsakaita ne Wanda suka dace da fuskar, idanuna da hakorana su suka fi ruda mutane a kaina saboda yadda sukeda kyau, haske a kuma Jere shi yasa ina secondary Kawaye na ke cemin _*SPARKLE*_ Da yawa mutane na ganin kyauna, sukance da ni Fara ce da tabbas na fitini al'umma a cewarsu kenan Danni idan naji haka se su bani dariya.

Shekaru masu yawa da suka shude sosae anyi wani fada cikin maiduguri ta borno state wanda ake kira fadan Rabe, wannan fada yasa kakkani na wanda suka haifi mahaifina suka baro maiduguri inda suka shigo cikin current jihar jigawa, idan ka taho wajensu hadejia, kafin Hausa da taura yawancinsu barebari ne hakan yana da nasaba da wancan fadan da na sanar muku basu kadai ba mutane da yawa na wannan yankin hakance ta kawosu.

Majiya ba wani babban gari bane sede ni a gurina ya fiye min garuruwa da yawa saboda a wannan garin nakan samu farin cikin da nake jimawa ban samu ba. Majiya na karkashin Taura LG, 'yan garin babu laifi suna da ilimi Don suma sunyi western education kuma yanxun haka ana damawa dasu.

Kakana shi ne dagacin garin, wato district head na majiya Alhaji Sama'ila, ya kasance adali ne wanda mutane da yawa a garin ke alfahari dashi, hardly kaji wani yana kuka dashi sede adawa, matan aurenshi uku Hajiya Gambo wadda Itace uwargida, Hajiya Azumi se ta karshe Amarya. Hajiya Azumi ita ta haifi Abbanmu wato Malam Adamu wanda yake da' na biyar cikinsu sha takwas, yawanci kasancewar gidan sarauta ne yasa sukai karatu na Boko dana islama, dukda na islama bawai anyi wani zurfi bane a ciki.

Mahaifina Malam Adamu yayi karatunshi a nan cikin garin na majiya a primary din, Seda ya kammalla kafin ya dawo Kano ya fara secondary school dinsa a Rumfa college, makaranta me Cikeda dimbin tarihi cikin birnin na Kano. Hajiya kamar yadda ake kiran hajiya Azumi Tasha bamu labarin cewa Abbanmu Tun yana yaro mutum ne shakiyyin gaske baya ji ga fitina da kuma yawo, tun yana karami yakeda jarabar yawo, duk kauyikan dake kusa dasu babu inda baya zuwa, kullum sede a dinga Yi mishi addu'a don kuwa ita ce kadai abinda zai daidaita shi.

Bayan Abbanmu ya kammalla secondary dinsa se ya dawo gida ya fara teaching a primary school din majiya, one thing about him Yana da kirki sosae, yanada farin jini, hakan yasa yake da 'yan mata yadda kukasan jumper a jos haka yake dasu, shi ba wani kyau ne dashi ba amma ya iya magana, ya iya tsari yadda bakwa tunani hakan yasa Mata da yawa ke falling masa.

Daga baya yaga gwara kawai ya tafi karatu hakan yasa yaje yayi NCE a FCE Kano akan English, wannan yasa masa interest sosae akan karatu tareda Kara masa iyayi da kwainane kai ka rantse mace ne, ga fafa, gayu da kuma karya dole Se yayi Abinda yaga wasu nayi Koda kuwa bashida halin Yi.

Daidai wannan lokacin Alhaji ya kira Abbanmu akan yazo zancen aure, Bayan Yaje ya nunawa Alhaji shifa gaskiya bazai iya aure ba don kuwa karatu zai yi hasalima bai isa Tara iyali ba, sosae Alhaji yayi mamaki yace

"Kai Adamu kalle ni nan, ni Kake cewa baka isa aure ba? Kannen ka nawa ne sukai aure zaka gaya min maganar banza!"

Shiru Abbanmu yayi har Seda Alhaji yayi shiru kafin yace

"Allah yaja da ran sarki! Ko daya ba haka nake nufi ba, wane ni naja da zancenka, kawai dai na samu admission a Zaria ne idan na kammalla nayi maka alkawarin kawo maka mata har garin nan."

Wata tsawa Alhaji ya daka mishi yace

"Har shekaru Nawa kayi niyyar daukar wa kanka ba tareda ka aje Iyali ba? Tashi ka fice min Daga guri.

Dama Bada hakuri baya daya daga cikin halayenshi haka ya shura takalmanshi ya shige cikin gida gurin Inna, ganin yanayinsa yasa wanda ke gurin suka fito dan basu guri, zama yayi gefenta fuska a murtuke kamar kunu _lol_ ita ta Fara fadin

Dan Inna meye ne,

Dan tsaki yayi yace

Inna meyasa ake min haka ne? Dan Allah me yasa ne?

Cikin rashin fahimta saboda Batayi tunanin zancen da sukai da Alhaji kenan ba tace

Kayi min bayani yadda zan fahimta, me akai yi maka?

Dauke kanshi yayi Yana kara bata rai yace

Kin sani mana, ba dake aka ce xa'ayi min aure ba

Baki wangalau tace

Kai! Kaci ubanka ni Kake fadawa haka? Tashi ka fice min a daki zaka zo Kamin dibar albarka, aure kuwa kamar anyi an gama ehe!

Dama Duk yadda take sonshi amma Bata daukar nonsense, haka ta fatattake shi ya tafi, bai kara awa ba ya koma Kano Don gani yake lokacin Kwana a kauye ya wuce.

Sati uku da faruwar haka ya tafi Zaria yayi registeraton ya samu accommodation sannan ya dawo Kano inda gidanshi yake, Bayan two weeks ya koma Zaria ya fara degree.

A Majiya kam babban bacin ran Alhaji shi ne tafiyar Abbanmu, sosae ya dinga fada kamar zai ari Baki yanayi hajiya Azumi na tayashi, to tunda ga Wannan ranar yasa a ranshi se ya kuntatawa Abbanmu Sede bai furta ba yabar abin a ranshi.

Shikam Allah sarki ubana yana can yana ta karatu ga yanmata kamar me, idan ka ganshi kace shi din ba karatu yazo ba, kuma se Allah ya mishi nasibi da kokari Don 4 points yake ja hakan yasa ake binshi Don ya koya karatu gashi da yan canji cikin pocket hakan ya kara masa yanmata, ga shi akwai Afro, a saka baggy trouser da suit hakan yasa kowa Ke kaunarshi ana rubibinshi.

Duniya tayi dadi bai taba tunanin wani abu zai iya faruwa ba ganin babanshi bai fiya matsa maka ba amma wannan Karon bai san ya taro match ba gashi babu yan wasa. Haka nan ranar ta kasance Monday, most busiest day ga kowanne mutum, saboda Monday ita ce tushen aiki ranar da take da bakin jini, Sede ga Abbana ba haka take ba. Wajen maghrib ya fito don zuwa inda ya saba cin abinci, shikadai Ke tafe kasancewar bai Faye abokai ba amma akwai kadan, Shiyasa hardly kin ganshi da friend sede budurwa. Yana Zuwa Yaje canter gurin yayi placing order sannan ya dawo ya zauna yayi shiru Yana tsara yadda gobenshi zata kasance.

A hankali wani sassanyan kamshi ya fara shiga kofofin hancinsa wanda ya sashi dagowa tareda sniffing Don tantance daga inda wannnan kamshi Ke, Sede gurin cike yake bazaka tantance wanda ya wuce ba, hakan yasa ya maida dubansa kan eclairs dake aje Kan table din wanda take kamar appetizer kafin a kawo main course meal din.

Wannan kamshin ne ya sake addabarshi hakan yasa ya dago sede idanshi suka sauka kan wata waitress dake tsaye a kanshi, dauke da tray Tana sakin murmushi wanda take ya jefashi cikin wani shauki, zumbur ya Mike tareda karbar tray din Yana sake kallonta, Tana cikin knee length skirt army green da waist length simple white stripe top long sleeve haka, Bra ce kawai jikinta wanda ya bawa jikinta damar bayyana, ga hips se swaying yake, kanta yasha wig, a fuska kyakyawa ce ta gaske babu karya sede kana ganinta kasan Christian ce.

Ganin Tarkon ta ya Kama yasa ta juya don komawa cikin main inda suke zama na eatery din, Tasha jin zancen Adams kamar yadda mutane Ke kiranshi, wannan dalilin yasa tayi developing interest akanshi har tayi trapping dinsa, kuma ko babu komai tasan goal achieved.

Shikam Abba kasa zama yayi duk yadda yakai ga dauriya Abu ya faskara Don Yana jin shifa yaga mata, haushin kanshi ya dinga ji da bai bita ba amma yasan there's always a second chance!

Shatuuu ♥️

RAYUWARMU A YAU!Where stories live. Discover now