*WASHEGARI*
     Yau Monday *ZYNAH* da *ASHRAF* zasu koma school for second semester, Uncle Yusuf kuma ana can ana jiran amsa daga wurin Minal, ita kuma kwakwalwarta duk yagama daburcewa dan harga Allah batason ta amince mishi daga baya kuma ya rabu da ita ya barta da jinyan ciwon zuciya. Sungama shiryawa *ZYNAH* da Humaira suka fito waje, Ummi suka gani dukae tsugunna suka gaisheta ta amsa musu tareda cewa su shiga wurin Ammi su gaishe ta se suzo suci abinci,amsawa sukayi da toh, sannan suka tashi, part din Ammi suka shiga, Basma ce a parlour tana shan grape tana kallo _keeping up with the Kardashians_ da sauri Humaira ta karasa ciki tace "Basma kema Kina kallon wannan program?", Basma tace "sosai kuwa, har banso yana wuceni, kefa", "ina kallo, dashi da Wags Miami da Life of Kylie, programs din akwai dadi", "sosai", Humaira tace "cikin Kardashians wa kikafi lyk?", Basma tace "gaskiya nafison Kourtney", "nikam nafison Kylie", haka sukata hira *ZYNAH* ganin Humaira batada niyyar tashi yasa taje wurinsu tareda tambayan Basma ina Ammi,  tace musu Ammi na daki su shiga,  tashi Humaira tayi suka shiga dakin Ammi suka gaisheta da fara'arta  ta amsa musu tareda da tambayan su sun kwana lfy  sukace eh, tareda ita suka fito dan itama wurin Ummi zata shiga.

     Suna shiga sukaci abinci, sannan suka fito, dama *ASHRAF* su yake jira su tafi tare, shiga motan sukayi *ZYNAH* na gaba Humaira na baya suka gaishe shi ya amsa tareda juyawa wurin *ZYNAH* yace "kin saba alkawari jiya, nace karkiyi bacci shine kikayi inata kira baki dauka ba", hakuri tashiga bashi dan taga missed call dinshi, cewa yayi ya hakura daga nan suka shiga hira jifa jifa suna saka Humaira ciki, da haka har suka isa school, kallon school din *ZYNAH* tayi dan koba komai tayi miss din school din, Humaira ma school din ya mata kyau a haka har ya isa inda zeyi parking, yana parking suka fito yace "kince 12:00 zaki fito daga lectures koh", tace "eh", "ki jirani in kin fito, ni sai 1:00", "ok ba damuwa" wucewa sukayi shima yabi hanyarshi, tafiya sukeyi *ZYNAH* na nunawa Humaira department daban daban daga sama taji ance mata "hello, baby girl, long tym no see", dago kai tayi taga wanda tafi tsana a rayuwarta ne a gabanta wato KB, cikin daga murya tace "wai fisabilillah se yaushe zaka hakura ka kyalle ni ne?", kallon wurin yayi yaga ana kallonsu dukda ba mutane dayawa yace "keep down ur voice before u embarrass me here", tsaki tayi taja hannun Humaira suka wuce, shikuma ya bita da mayataccen kallon wanda shikadai yasan fassaranshi. Humaira ce ta tambayeta "waye kuma wannan", "shine KB", Humaira a zuciyar ta tace "well he's nt looking bad, kyakyawa ne sedai baki ne kuma bakinshi me kyau", nuna mata wurin zama *ZYNAH* tayi tace "zauna nan kafin infito,  in kuma kinaso ki zagaya school din toh, amma dan Allah kafin sha biyu ki dawo nan kar in saura nemanki", "jeki kawai karki damu",  shiga lecture hall *ZYNAH* tayi inda tana shiga Shaheeda tayi wani ihu tareda zuwa ta rungumeta tace "oohhhh my babe i missed u a lot", dariya tayi tace "i missed u more, ykk kwana dayawa", "wlh ina nan fyn, tun ran Friday nadawo, nazo hostel dinku, kinsan Ashanty bata pata lokaci wurin dawowa, saboda haka ita kadai nagani, take cemin wai kince mata ba'a school zaki sauka ba wannan karon", "eh ba'a school na sauka akwai lots of gist, amma se anjima na hango wannan mummunan lecturer nan zuwa", ai kuwa bata gama rufe baki ba segashi ya shigo duk suka nema wuri suka zauna dan baya wasa wannan lecturer, student ma Mr No Nonsense suke kiranshi.

     Minal ta fito zata wurin dinki ta hango Uncle Yusuf tsaye shida gate man suna hira harda dariya, sosai ya burgeta ganin yanda yake dariya gashi kuma beda girman kai tunda har ya iya ya tsaya yana hira da mai gadinsu, sauke kai tayi taci gaba da tafiyanta wanda batasan cewa tun fitowarta ya hango ta ba. Har ta kai bakin motanta taji yana mata sallama ta bayanta, amsawa tayi tareda juyowa tana fuskantar shi, yace "se ina?", "wurin dinki zani", "koyo kikeyi ne?", "eh, nama kusa kamallawa", "okkkk toh ya maganan mu", sunkuyar da kai tayi tana murmushi tace "ka bari inna dawo, ", shima murmushin yayi ganin yanda kunya ya lullubeta yace "wannan kunyan kuma fa, koda yake gado ne, na Fulani, an sansu da kunya, karfe nawa zaki dawo", "se 6 zan dawo", "toh ai kafin lokacin na kuma dan 4 zan bar nan, amma ba matsala ban contact dinki, inyaso na kiraki", ciro wayan yayi ya bata tasa mishi number nan ya kirata saboda ya tabbatar ba wrong number bane, kuma yaji ringing din a jakanta yace "number na kenan kiyi saving dinshi", tace "toh", sannan ta shiga motanta, kwankwasa mata glass din motan yayi ta bude yace mata "drive carefully", murmushi tayi tace "i will" sannan ya bata hanya ta tada motanta me gadi ya bude mata gate, ta fita shikuma be wuce ba seda yaga fitanta sannan ya wuce cikin gida dan yayi wanka.

     Humaira ganin zaman ya ishe ta yasa ta tashi danta zagaya, ta Kai wurin wani  café taji ana kiranta da "jimana dan tsaya", juyowa tayi dan taga wani dan iskan ne ke mata irin wannan kiran, mamaki ne ya kamata ganin KB a gabanta, murmushi yayi yace "kin gane ni, nine na dazun da...... ", bata bari ya karasa ba tace "naga neka menene me kakeso?", "kinga ba wani abu bane illa inaso muyi wata magana dake", "ba damuwa inajinka", "mudanje can mu zauna, dan maganan me tsayi ne", ba musu ta bashi suka zauna kan wani benci yace "ko baki fada ba nasan ke kawar *ZYNAH* ce shiyasa naga ke yadace in nema muyi magana ta fahimta dake", kallonshi takeyi ba tareda tace komai ba yace "sanda *ZYNAH* ta koma Lagos hutu nasa abinta har can wanda wannan yasa nasan ku kawaye ne", cike da mamaki tace "ka bari aka bita saboda me?", "nasan kinsan komai a kaina dan haka bazan boye miki komai ba, ada nayi sha'awar kawarki, kuma alokacin plan dina be wuce in kawar da kwadayina a kanta ba, amma yanzu d story has change sonta nakeyi kuma da aure", "se kuma aka ce maka zata auri watsastse irin  ka", dukda kalman ya mishi ciwo amma seya danne zuciyarshi yace "kinga ni sonta nakeyi ba komai ba, kuma abunda yasa kikaga ina miki magana yanzu saboda nasan kema Kina son *ASHRAF* ko nayi karya?", kasa bashi amsa tayi se dai mamaki da takeyi ya akayi ya sani, ganin bata bashi amsa bane yasa yasan cewa tarkon da ya dana yafara kamuwa, kallonta yayi yace "saboda haka indai zaki bani hadin kai in samu *ZYNAH* toh ni namiki alkawarin samun *ASHRAF*", dago kai tayi tace " ta yaya", "kedai bani hadin kai tukun sena fada miki abunda zamuyi", seda ta tsaya tayi tunanin hanya bataci amanar kwance ba, amma saboda idonta ya riga ya rufe bata gani se tace mishi taji ta amince, wani munafikin murmushi yayi yace "shikenan ban number ki, anjima zan kiraki semuyi magana", ba musu ta bashi number yayi save bayan ya tambayeta sunnan ta, sannan ya tashi ya bar wurin bayan yamata alkawarin ze kirata. Ita kuma tana nan zaune a wurin tana tunani sannan ta tashi ta koma inda take jiran *ZYNAH* .

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now