Karfe 9 na dare *ASHRAF* ya dau waya ya kira *ZYNAH* amma be shiga, wannan ya tabbatar mishi da basu sauka ba tukun, 9:30 jirginsu ya sauka, suna fitowa Uncle Yusuf yazo ya daukesu, cikin mota ta kunna wayanta wanda tana kunnawa kiran *ASHRAF* na shigowa, kashewa tayi sannan ta tura mai text cewar "sun sauka suna cikin motane, in ta kai gida zata kirashi", tafiyan 30min yakai su gida, duk sun gaji saboda haka suna zuwa gidan bayan sun gama gaishe gaishen su da masu aiki duk sukayi daki sukayi wanka tareda sallolin da ake binsu sannan suka sauko dan Jummalo ta musu girki,  suna gama cin abinci kowanen su yayi daki, *ZYNAH* na shiga daki ta dau wayanta ta soma kiran *ASHRAF*, kashewa yayi sannan ya kirata sukasha hiransu sannan daga baya tace mishi barci takeji sukayi sallama ta kwanta, bajewa tayi a kan gadonta sosai tareda cewa "i miss u my luvly bed, i knw u miss me too", sannan tayi kissing din gadon taja comforter, ba dadewa ta dauke wuta,(toh madam *ZYNAH* a tashi lfy). Da asuba da kyar ta tashi tayi sallah saboda gajiya, nan inda tayi sallah ta kwanta taci gaba da barcinta. Karfe goma na safe gidan kowa ya tashi Daddy har ya tafi office, Uncle Yusuf ma ya wuce aiki, Islam ma ta wuce school, amma gimbiya na nan na barci, Momcy ce ta fito taga dinning ba'a kwashe kullolin da sukayi breakfast dashi ba ta tambaye Jummalo, Jummalo tace " Hajiya *ZYNAH* ce batazo taci abincin ta ba", girgiza kai Momcy tayi tace "wannan yarinyar har yanzu bata canza ba kenan", sannan ta haura sama, shiga dakin *ZYNAH* tayi ta ganta kwance a kasa tana barci, karasawa tayi tana tashinta wanda da kyar ta iya bude ido dan ji take kaman an mata duka, "tashi kiyi wanka, kizo kici abinci seki koma barci", da kyar ta amsa da "toh", sannan Momcy ta fita.

     Da kyar ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka, ta fito ta shirya sannan ta sauka kasa, koda ta sauka Momcy na parlour, ta gaisheta sannan ta koma kan dinning taci abincin ta, tana gamawa ta wuce sama, wayanta ta dauka taga 5 missed calls, biyu daga *ASHRAF*, daya daga Humaira, daya daga Shaheeda, se last one din daga Ashanty, taso tasake kiransu amma kuma tana so tayi barci kuma tasan muddin ta kira *ASHRAF* toh ba ita ba barci, ajiye wayan tayi, ta kwanta tareda jan comforter ai kuwa nan da nan barci ya dauke ta, Karfe 1:30 Humaira ta fado gidan, ba kowa a parlourn se motsi da takeji a kitchen, kitchen ta shiga taga Jumallo na juye abinci a cooler, nan ta gaishe da ita sannan taje ta dauko plate tace a zuba mata taci dan yunwa takeji saboda daga school take, ba musu Jummalo ta zuba mata tana mata dariya, sama ta nufa da abincin a hannunta, dakin Momcy tafara shiga saboda Jummalo tace mata tana daki, da sallama tashiga Momcy ta amsa tareda cewa "Humaira ce a gidan yau, lalle, wato dan kawarki ta dawo ko, aini nayi fushi tunda bakya zuwa se in *ZYNAH* na nan", karasawa tayi ciki tana cewa "Momcy ba haka bane, wlh school ne yasani gaba, yanzu haka ma mun fara test", "OK, toh ya karatu", "alhmdllh", "toh a maida hankali sosai, jiya ma munyi waya da mamanki take cemin karatu yasa bakida lokacin kowa yanzu", "wlh Momcy ba sauki bane, ai ni naga kokarin *ZYNAH* ita me karatun medicine", dariya Momcy tayi tace ke bazaki iya ba kenan?" ,"kaiii gaskiya bazan iya ba, nida ko jini nagani se tsigar jikina ya tashi ina ni ina medicine ko nursing, gwara dai pharmacy dina, ya fiye min", dariya Momcy tayi tace "kinjiki da wani zance, ga abincinki na sanyi, *ZYNAH* na daki", Humaira tace "nasan bacci takeyi", "ai kema kinsan aikinta kenan", tashi tayi tace "bari inje in tashe ta", tana shiga dakin taga *ZYNAH* kududdine cikin bargo wacce ta dade da tashi amma tayi kaman tana barci dan taji shigowan Humaira, Humaira zuwa tayi ta ajiye abincin ta akan tebur dinda *ZYNAH* ta jera kayan system dinta akai na computer sannan ta ajiye jakanta da mayafi tayi kan *ZYNAH*, yaye comforter din tayi sannan ta dane kan *ZYNAH* ta fara mata chakulkuli, tun *ZYNAH* na gimtse dariyan ta harta kasa ta sake dariya me dadin saurare tareda fadin "dan Allah dena, wayyo Allah na, bestee dan Allah dena", tana fada tana dariya, sakinta Humaira tayi, gabadayansu suka dinga maida numfashi, seda ta nutsu sannan ta mike zaune itama Humaira ta tashi zaune suka kalli juna sekuma sukasa dariya sannan suka rungume juna tareda exchanging i miss u da miss u too, sakin juna sukayi sannan Humaira ta tashi ta dauko abincinta ta soma ci tareda cewa "so,  wats up, gist me nw, hw hav being, ya school, ya Zaria nd most importantly ya boo boo dinki", pillow *ZYNAH* ta wurga mata tareda cewa wani boo boo kika bani?", Humaira na dariya tace "kin fini sani ai", dariya sukayi gabadayansu sannan suka shiga hiran da baya karewa, suna cikin hira Humaira taga alamun wayan *ZYNAH* na flashing wuta alaman ana kira,  nuna mata wayan tayi ta dauka, taga *ASHRAF* ne kira,  murmushi tayi tace "shike kira", "dauka toh kar ya tsinke", dauka tayi tareda cewa "hello yayana ina wuni", yace "ban wuni ba,  wato har kin manta dani ko", tace "a'a wlh, na saura ina baccin gajiya ne, se yanzu bestee dina tazo ta tashe ni", "i see, toh ykk, ya gd, ya kowa da kowa, ya bestee dinki?", "duk lfy lau, bestee gatanan wai tana gaida kai", "bani ita mu gaisa", nan ta mikawa Humaira waya suka gaisa wacce muryan *ASHRAF* da taji yasata rudewa, mikawa *ZYNAH* wayan tayi sukaci gaba da hiran su, wanda ba dadewa sukayi sallama tareda kashe wayan, tana ajiye wayan Humaira tace "ni kuwa wannan *ASHRAF* ban taba ganinshi ba koh a hoto,
swthrt kodai rowanshi ake mana?", *ZYNAH* tace "lahhh, bestee yi hakuri bari in nuna miki shi", tareda dauko wayan tashiga gallery take ciro hoton *ASHRAF* ta nuna mata, kallon hoton takeyi bako kyafta ido, a zuciyarta tace "aminci ya tabbata ga Allah wanda ya halicce dan adam sannan ya fifitashi akan duk wani abu da ya halitta a doron kasa", mikawa *ZYNAH* wayan tayi tace "naga abunda yasa ake mana, rowanshi", dariya *ZYNAH* tayi tareda kaima Humaira duka tace "ke kika sani", hiransu sukaci gaba dayi, karfe shida Humaira ta wuce gida, *ZYNAH* na dawowa daga rakiyan Humaira taje wurin Momcy ta tambaye ta meyasa  Islam bata dawo ba,  "Momcy naga har past six amma Islam bata dawo ba", "eh, Daddyn ku yasata a extra lesson saboda zukancin ta", *ZYNAH* batace komai ba illa tashi da tayi ta nufi dakin Islam inda ta bude drawer dinda Islam ke ajiye school accessories dinta ciki, nan taga script din Islam na test dana exam which she performed woefully a result dinda girgiza kai tayi tareda daukan alwashin seta canza Islam kafin ta koma school. (Is dis possible? mu dai je zuwa).

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now