Ba dadewa Chima ta dawo da wata kyakyawan attendant dinsu tasa kayan da suke sawa in suna shagon which is Pink top da jeans anyi customizing sunanta a bayan rigan, suna zuwa Chima tacewa yarinyar "here she is, make sure u give her d best service" ,"ok ma" yarinyar ta amsa sannan ta juya wurin *ZYNAH* tace "shall we" tayi gaba *ZYNAH* ta bita a baya suka shiga wani daki da mutane a ciki duk ana musu gyaran gashi itama *ZYNAH* ta zauna inda yarinyar ta nuna mata ta cire kimono dinta da mayafi ta ajiye gefe, yarinyar tazo ta wanke mata kai da shampoo dan batasa relaxer saboda laushin gashinta, ana gama wankewa akasa mata roll on ta shiga dryer bata dadeba kanta ya bushe ta fito ta zauna gaban mirror aka gyara mata kanta sosai ta mayar da ribbon dinta tasa sannan suka koma wani dakin daban na gyaran farce aka gyara mata farcen kafa dana hannu ta fito fes da ita, Chima tazo dubata ko an gama taga harsun gama *ZYNAH* ta biya ta musu sallama ta fito ta shiga motanta ta harba titi, bata tsaya ko inaba se *JUSTRITE* tayi siyayyan kayan shirmenta na chocolates da sweet sannan ta fito taje *KFC* ta siya fried chips da chicken aka mata package dinshi ta fito ta kama hanyar gida. Koda ta kai gida karfe hudu saura ta shiga taga ba wanda ya dawo cikin en gidan itama Islam ta fita. Dakinta ta wuce direct ta ajiye kayan da tasiyo ta cire kimono dinta ta bar top da jeans din ta dauko chips da chicken dinta ta fito taje kitchen ta dauko plate ta juye ta dawo kan dinning ta soma ci hankalinta kwance harta gama.  Horn taji da kuma tayuwar mota a compound ta tashi ta leka taga Humaira ce, da saurinta ta fita tana cewa "my bestee is here" ta rungumeta itama Humaira tana murmushi tace "swthrt i missed so much" ,"i missed u more" suka rike hannun juna suka shiga ciki. "Swthrt yunwa nakeji" ,"yanzu kuwa nagama cin chips akwai saura zakici?" ,"kawo min zanci" *ZYNAH* taje ta dauko mata sauran chips dinda ta rage ta bata tanaci suna hira Humaira tace "swthrt ur hair looks nyc" ,"tnx, House of fashion naje" Humaira ta bata rai tace "shine kikaje ke kadai baki gayamin ba" ,"naga u ar busy wit lectures  ne dats y, bt am sorry" ,"naji na hakura, bt don't do dat again" ," I promise i won't". Haka suka ci gaba da hira Humaira nataba *ZYNAH* lbrn Hafsa har biyar tayi basu saniba *ZYNAH* ta kalli agogo tace " bestee banyi la'asar" ,"nima haka" suka tashi suka shiga daki dan yin sallah.

     Suna idar da sallah Humaira ta mayar da mayafinta ta dau jakanta tace "ni zan wuce, mu hadu a airport gobe" ,"ok, amma pls don't b late gobe, kar mu wuce baki zoba" ,"don't worry In Sha Allah by 12 ma ina airport din,ki gaishe da Islam" ,"zataji, muje na rakaki" suka sauko tare, Humaira ta shiga motanta gate man ya bude mata gate tana fita Momsie na shigowa  suka gaisa sannan Momsie ta shigo ya kulle gate din itakuma tayi parking ta fito itada Jummalo *ZYNAH* ta musu sanda zuwa suka amsa Momsie tace "zo ki tayamu shiga da kayan nan" ta bude boot kayan fast food suka shiyo Jummalo ta kwasa itama *ZYNAH* ta kwasa dede wanda zata iya deba suka shiga dashi, ko kafin su dawo Momsie ta kwaso ragowan ta kulle motanta ta shigo itama. Jummalo tace "Hajiya a kai kayan store" tace "eh a kai store" suka kwashe suka kai store *ZYNAH* ta dawo ta zauna tace "Momsie kun dade" ,"mun biya gidan Maman Jabir ne, a nan muka zauna munata hira, babban ki ya dawo" ,"a'a be dawo ba" ,"ina kanwarki banji motsinta ba" ,"itama bata dawoba" ,"har yanzu, daga cewa zata wurin yasunan kawarta dinnan" ,"Zeeza" ,"eh ita, shine har yanzu, kira min ita ta dawo yanzu nan" ta dau waya zata kira kenan sukaji sallaman ta *ZYNAH* tace "er halak gata ta dawo" ,"Momsie sanda gida" ,"yauwa sanda zuwa gantallaliya,daga ina" ,"Momsie ai na gayamiki zani gidansu Zeeza" ,"se me kikeyi a gidan har yamma haka,wlh Islam ki kiyaye ni, tohm" zama tayi ranta duk ya gama baci an mata fada. Suna zaune *ZYNAH* da Momsie nata hira itakuma Islam ta cika tayi pam zata fashe, saboda haka kiris take jira ta fashe da kuka. Sallaman Daddy ne ya katse su duk suka mai sanda zuwa ya amsa sannan ya zauna kusada Momsie yace "Mamana ban ruwa nasha" *ZYNAH* ta tashi ta kawo mishi ruwa yasha yayi hamdala sannan yace "Islam lfy naganki haka?" ,"Daddy ba komai" ,"tunda kince haka shikenan" yasa hannu ya dauko ledan da ya shigo dashi yace "Mamana karbi nan" ta karba tana cewa "Daddy me wannan" yace "bude ki gani" budewa tayi ta duba, wani razanannen ihu tasa ganin IPhone7 sabo dal a kwali, batasan sanda ta fada kan Daddy ba tace "tnx Daddy, u ar d best" murmushi kawai yayi yace "u deserve it Mamana" Momsie tace "Masha Allah wayan yayi" ta zauna da kyau tana bude kwalin dan taga wayan da kyau. Pink ne wayan da charger da earpieces dinshi komai intact, sannan ga pouch shima an siya mata. Dadi da ringa ji sosai, Islam ce ta katse su da cewar "Daddy ita kadai ka siyawa" yace "eh ita kadai na siyawa, nd dat is saboda ta kai tym dinda ya kamata ta rike big phone ne haka, kema kuma duk randa kika gama secondary nd ready for Uni i promise u d latest phone in town" ,"ok Daddy Allah ya kaimu lokacin, sista am happy for u" ,"tnx Lil sis".

**********
     *ASHRAF* ne da Haydar gaban laptop suna filling form din school dinda Haydar ze tafi, suna cikin filling form din Minal da ke zaune gefe tace " wayaga su Haydar a Oxford, rawan kai se abunda ze karu" Basma ta karba da cewar "ai kuwa dai,Allah yasama ayi karatun da kyau" yadago zayi magana *ASHRAF* yayi tapping keyanshi yace "maida hankalinka nan,sarkin surutu" yana sosa keya ta kallesu sannan ya juya kan laptop din sukaci gaba da abunda sukeyi, su Basma kuwa dariya suka dinga mishi. Da haka suka samu suka gama filling form din *ASHRAF* ya tashi ya fita, yana fita Haydar ya juyo wurin su Minal yace "aga aga, aga wa'anda basuje Oxford ba" ,"Basma tace saime dan bamuje ba, kaima kasan bamuga dama bane" yace "ko kunga dama ko baku gani ba for nw a history din gidan nan nine first person" Minal tace "wannan kuma kai ta dama ba muba" ,"eh din naji dai" haka suka ta hira har suka gaji suka tashi suka barshi wurin yanata shirmen shi. Sameer ne da *ASHRAF* zaune kan mota Sameer yace "guy Monday school fa" ,"ai kai ya kamata a tunawa ba niba" Sameer yayi murmushi yace "yanzu dan Allah Monday zaka koma" *ASHRAF* yace "sa ido ka gani, kai ni na manta na tambaye ka ya jikin Mom dinka?" ,"da sauki tana gida ma yanzu" ,"bayan Isha zan shiga na gaishe ta" Sameer ya kalli *ASHRAF* sosai yace "guy kwana biyu naga ka daina  drawing lfy" ,"na daina mafarkinta ne shiyasa" ,"okkkk, toh yanzu dai Allah ya kawo mu 400level do u hav any plans for it" *ASHRAF* ya kalle shi da mamaki yace "plans lyk" ,"lyk having a girlfriend" dariya *ASHRAF* yayi saboda magana ya bashi dariya yace "ar u kidding me? girlfriend at dis age of mine" Sameer yace "nd so" da mamaki *ASHRAF* ya maimaita "nd so, am just 24 nd u ar saying nd so, look guy to b honest wit u am nt ready, kai ni mata ma basa gabana so just forget it". Sameer kallon *ASHRAF* yayi ya girgiza kai kawai batare da yace komai ba har ya gaji da zaman kurame dan ya lura in bashi ya kikiro zance ba haka zasuta zama kawai se yace "guy zan shiga gida na huta" ,"ok se  later kenan" ,"eh ai kana gida" ,"ina nan ba inda zanje" suka tafa *ASHRAF* ya shiga gida Sameer ma ya wuce gidansu.

     _Nasan ina wasa dayawa yanzu, bana typing akai akai bt i promise am gonna make it up to u guys, much luv ❤_

          _Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now