BABI NA ASHIRIN DA DAYA

1.5K 122 7
                                    

DOGARO DA KAI
© Ayeesh Chuchu
1st September,2016

   I dedicated this chapter to Iftahal A. Naseer (Ukhty),Aysher Abdallah,Sanah Matazu, Mrs. M, Najfar,Meemee Hamza, Fatima M. Lawal, Zainab Yahuza, Khadijatul Kubra, Meelah Uthman, Aysha Lawan, Ummin Nazeer, Aysha Bizzy, Love you lodi-lodi.

{21}

  An sa ranar bikin Samir da Zainab watanni biyar.
A bangaren sana'ar Zainab kuwa ta samu cigaba sosai in da ta yi suna a arewacin Nigeria wajen fashion design. Ta na samun kuɗi sosai, saboda suna ɗinka ready-made, su na kuma ansar ɗinki wajen mutane.
Ma'aikatanta na ba ta haɗin kai yanda ya kamata, shiyasa ba ta samun matsaloli sosai.
                  **************
"Auta wannan abinci da yawa haka kamar za ki gayyaci mutane sama da dari".
"Momi ni fa ba a gida zanyi celebrating birthday ɗina ba".
"Ina za ki yi?".
"Orphanage Home! (gidan marayu)".
"shi ne ba ki faɗa ba, ai da ni ma na shirya wa ni abu, auta sukutum da guda na celebrating 26 years ai dole na yi hobbasa".
"yauwa Mummy a can zan yi cutting cake ɗina".
"am proud of you Zainab. Allah shi albarkaci rayuwar ki, ya karo shekaru masu albarka ".
" Amin Momi".
         Tsaye su ke bakin gate ɗin gidan Marayu. Kayan masarufi ne ake saukewa dangin su shinkafa, Macaroni, taliya, indomie da lemuka na kwali.
"yauwa sannun ku da kokari".
  Sun shiga cikin gidan,bayan sun gaisa da matron da ke kula da marayun. Nan Zainab ta faði makasudin zuwanta, aka ba ta visitor's book ta yi signing.
  Nan aka tara yaran mazansu da matan su, Zainab ta shiga cikin su suna ta wasanni. Sai bayan sun gama aka raba ma su abinci da lemun da aka zo da shi. Sannan ta yanka birthday cake ɗinta, ta bi kananan yaran ta na ba su a baki.
   Sun dau hotuna sosai, ba ta bar gidan ba sai gab da Maghreba.
  Wanka ta yi ta kwanta kan gado dan tana fashin sallah.
Wayarta ce ta dau kara. Ta gyara hular da ke kanta ta sake rufe gashin kanta.
Ta na dauka hoton shi ya bayyana a saman allon wayar zaune ya ke a bakin ruwa da ga gani kasar turawa ce. "Honey bunch where have you been? Tun dazu ni ke trying number ki, sai yanzu na same ki ta IMO".
"Ooh sorry dear na fita ne".
"am just missing you, ba kamar yau da na so a ce ina nan, mu yi celebrating birthday ɗin tare".
"kar ka damu dear, ni ma i Wish kana kusa, though I celebrate it with the orphans at orphanage home".
"MashaAllah! Jazakillahu khair my cutie pie. Ina alfahari da ke".
"Thanks my lovie dovie ".
" yauwa kun yi maganar kuwa da Momi, kin ga yanzu da na dawo za'a yi lunching branch ɗin mu a Abuja ni zan ci gaba da kula da wajen. So zamana zai dawo Abuja kacokam tunda sabon waje ne kin ga kema nan za ki dawo, shiyasa na ce kuyi maganar in ji yanda za'a yi da na ki wajen. Idan nan Gusau za ki zauna ba matsala every weekend sai in zo, bani son in tauye ki. Abin farin cikina ne a ce ke matata ce. Zan cigaba da supporting ɗin ki daga nan har karshen rayuwata".
"Ooh Booo.. U'r more than a darling, thanks for always been there for me. In Shaa Allah duk abinda muka tattauna zan sanar da kai".
Sun dade suna musayar kalmomin soyayya ma junansu.
                    ***********
Tuki ta ke cikin gwanancewa, ta na bin wakar "Love on the brain"  na Rihanna.
Ta na bin baitin tiryan-tiryan.
   Katafaren shagon ðinkinta ta isa, sun gaisa da ma'aikatanta. Sashin media tq shiga dan tana da abubuwan yi a Internet.
   "Miss Zee dazu ni ke ganin tallar gasar City people akan fashion design a instagram handle ɗin su".
"Eh jiya da dare na gani, I think ni ma zan shiga".
"Gaskiya ya kamata kar ki ji tsoro, You can make it".
"In Shaa Allah, thanks for the courage".
   Duk wani abu da ake bukata na shiga gasar Zainab ta cika wadannan sharuddan na gasar.
  Zaune suke a falon Momi su na firar su.
"Auta Daddynku ya baɗa kudin siyayyar ki na furbitures, Habib ya bada na kitchen appliances".
"Amma fa nagode kwarai Allah shi kara budi, anjima na kira in ma shi godiya".
"Ni kuma sauran abubuwan da suka rage zan yi".
"ai rabawa ma ku ka yi Momi?".
"Eh ai kin ga an sami sauki".
"ni kuma duk kayan da zan din ka kayan da zan sa".
"Inyee! Ka ji madinka"
"Momi ku taya ni addu'a, there's something good that am hoping for".
"toh Allah shi tabbatar da alkhairi ".
                **********
BAYAN WATA BIYU
Duk wani shirye-shiryen da ya kamata ayi na biki an yi, bikin kadai suke jira. Kowa ya ci ma bikin buri, ba kamar Aunty J da ta ke jin kamar kanwarta uwa daya uba daya za'a aurar. Duk wasu abubuwa na gyaran jiki da ta sani sai da ta tanadar ma Zainab.
  Ta bangaren ango Samir tamfatsetsen gida ya siya a life camp.
  Lefe kuwa kuɗi ya tura ma Zee ta siye duk kalar kayan da ta ke so.
  Da ya ke gwana ce wajen zaben kaya, ta online shopping ta siyi dangin su takalma, jakkuna, kayan shafa da costumes, atamfofi, laces, shadda da materials, sai inner wears,pyjamas, da English wears, gyaluluwa da kuma yadikan hijabai.
  Abayoyi kuwa ita ta zana abin ta da kanta ta yi order yadikan da za ta yi amfani da su saboda tana son abu unique. Ba ta wani cika kayan da yawa ba sai dai ta sayi ma su kyau da quality.
  Da kan shi ya zo ya karɓa ya adana kafin lokacin kai lefe ya yi.
    Alamar shigowar sako ta ji a wayarta ta na dubawa ta buga tsalle tare da kai goshinta kasa dan godiya ga Allah Madaukakin Sarki.
   Ta rasa wanda za ta faɗa ma wa, dan daga Amina ma'aikaciyarta babu wanda ya san maganar.
     Momi ba ta nan ta fita unguwa.
Yanda aka turo ma ta SMS ɗin haka ta yi forwarding ɗin shi zuwa ga Samir.
Ba'a yi minti biyu ba ya kira ta.
"My ever loving mi ki ke nufi da text ɗin ki?".
"Ina nufin na yi winning City people award Akan fashion design as the best fashion designer ".
" Huh! Yaushe ki ka shiga ban sani ba?". "two months kenan babu wanda ya sa ni fa, Ina dai son na baku mamaki ne".
"Ai kin bada mamakin, fiye da zato na. My wifey am proud of you. I always known you're the right girl for me, we were perfect for each other, meant for each other. I'll forever love you with all my heart".
"Awwwn! I feel like am the luckiest girl ever. I always appreciated the time we spend together and am hoping for much much more time to spend together in love with my hubby. You've been always the sweet morning songs that play in my head. Please be mine forever Sam! I can't afford to lose you ".
" Za mu kasance a tare har a Jannatul firdaus Zee.. Duk wuya duk dadi ki kasance a tare da ni, idan ki kai haka kin bani duk wani farinciki".

  Koda Momi ta dawo ta tsinci wannan labari, ta yi matukar yin murna haka ma Daddy da duk wani mai kaunar ganin cigaban Zee Gumi.
   A Abuja za'a yi taron da za'a karrama su.
  Ana gobe za'a karrama su ta tafi Abuja inda ta sauka gidan abokin Daddy, a can ta haɗu da diyar shi sa'ar ta Ameera Sadeeq.
  Da yamma su ka fita yawon shan iska.
WASHEGARI
  04:00PM
Tsaye ta ke jikin madubi tana shafa.
Ameera da ke kokarin sa ka belt ɗin takalminta ta ce "Wai Zee komi kin iya ne?".
"Kai Meerah ai nobody is perfect. Ina da abubuwan da ban iya da yawa".
"Ba zan yarda ba, kin iya girki, kin iya Makeup, kin iya dinki kin kin iya abubuwa da dama".
"Hmmm haka dai ki ka ce amma ni na san akwai inda ni ke da lapses sosai".
Ta yi masifar yin kyau cikin Gown ɗin material da ta saka, takalmi mai tsini (high-heels shoe) ta sa ma kafarta samfurin MB (Manolo Blahnik), ta sagala side bag mai chain samfurin Stuart Weitzman. Tsintsiyar hannunta daure da agogon Jaeger-LeCoultre.
  Ta feshe jikinta da turaruka ma su sanyi da dadin kamshi.
"MashaAllah! Black is beautiful. Zee kar ki rusa taro fa".
"Ke ta taro ki ke, Samir ni ke gudun ya yi fushi. Be son yawan makeup yanzu za ki ga ya haukace mun".
"Kishi halas ne! Amma kuma wannan taron sai da ke ce raini".
  A tare suka fito bayan sun ma Mami sallama cikin motar Meerah su ka tafi.
Ba su zarce ko ina ba sai gaban SHEHU YARADUA CONFERENCE CENTRE da ke a 1 memorial drive.
Cike wajen yake da motoci na alfarma. Sun shiga cikin hall ɗin cikin takun kasaita.
Waje su ka samu su ka zauna. Zainab na ta kalle-kalle dan ba ta ga fuskar sa ni ba.
  Kamar daga sama ta ji Muryar shi "Hey Zee".
"Oooh! Abdulhameed ashe za mu kara haɗuwa?".
"gashi Allah ya yi".
  Nan ya zauna kusa da Zee su na ta firar yaushe gamo.
  Daga can nesa ya hango ta, su na ta dariya ita da Meerah da Abdul.
Wani irin tukuki ya ji, kishinta ya rufe ma shi ido, ji ya ke kamar ya yi ta falla ma ta mari.
  Fara gabatar da shirin ne ya sa su ka natsu, nan taro ya fara bayan jawabai da masu hannu da tsaki su ka yi.
  Ana ta kiran sunayen mutane daban-daban ana faɗin award ɗin da su ka samu.
  Zee ta yi jugum jin har an kusa gama lissafo sunayen babu sunanta.
Kamar daga sama ta ji an ce "Zainab Isma'il Gumi the young lady ZG as the best fashion designer in 2016".
  A hankali ta taso, ta tattara duk wa ta natsuwa ta ta, ta isa bakin stage.
  DORU OLOWO (fitaccen fashion designer da ya sha karɓar lambar yabo. Mutumin da USA first lady Michelle Obama ta sa daya daga cikin DESIGN ɗin shi) ya miko ma Zee award ɗinta. Hasken camera ne ke ta haskowa ko ta ina, mutane sai zuwa suke ana daukar hoto da ita.
Yan jarida na ta aikinsu na daukar rahoto. Dole ta sa Samir fitowa su ka dauki hotuna bayan ya kara taya ta murna.
Yanayin shi kadai ta kalla ta tabbatar da yana cikin bacin rai dan sai wani fizgar kai ya ke yana shan kamshi.
    Karfe tara su ka fito daga hall ɗin, suna jingine da motar Meerah.
"Zee ba ni lambar wayar ki ma rika gaisawa".
  Ta karanto ma shi lambar wayarta.
Ya yi ma su sallama. Za ta shiga mota kenan ta ji an janyo hannunta.
Ta kai duba gare shi.
"Sam! Sakar mun hannu ma na".
"Ba zan sa ki ba, sai kin faɗa mun waye wannan mai shegen nacin da ya bi ya kanainaiye ko ina duk in da ki ka sa kafa ya na biye da ke. Ba ki faɗa ma shi cewa matar aure ki ke ba?".
"Haba Cheri, Abdul ne fa abokin karatu na a Riyadh. Ba wani abu bane tsakani na da shi".
"Shut up! Amma dan mi za ki ba shi Phone number din ki?".
"Saboda mu rika gaisawa".
"toh ba zan lamunta ba, ta ya ya za ki rika magana da wasu kattin banza. You know am over jealous and I never wanted anyone to come close to you, why not ba za ki kiyaye ba?".
"Why not ba za ka yi trusting ɗina ba? Kai kadai ni ke so, amma son ka ba zai sa in rika wulakanta mutane ba. Sam ina tsoron zuciyar ka. You're too emotional ".
" Yes am I in dai akan ki ne dan haka ki kula".
   Ya juya ya tafi. Mamakin halin Samir ta ke na shegiyar zuciyar shi. Ya na da saurin fushi.
                 **************

Hehehe I enjoy typing this chapter with my gyada a gefe..

   One word for Zainab & Samir.

I lobiyu lodi-lodi.. Ina kaunar ku.
   Indonku ce!

Don't forget to comment, like and vote on Wattpad @ayeesh_chuchu or blog chuchungaye.wordpress.com.

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now