BABI NA HUDU

1.7K 124 1
                                    

DOGARO DA KAI

©Ayeesh Chuchu

AUGUST, 2016

{4}
ASALIN SU

Alhaji Isma'il dan asalin garin Gumi ne, karamar hukuma a cikin jihar Zamfara.
Ya taso cikin wahalar rayuwa na rashin iyaye, wanda yayi sanadiyyar rashin mai tallafa ma shi a harkar karatunshi.
Shi ke duk wani faði tashi dan ya taimaki kan shi, duk wani aiki na karfi yana yi. Da haka yake samun kudin da zai biya bukatun kan shi.
Har Allah ya cika ma shi burinshi ya kammala digirin ɗin shi na farko a fannin PETROCHEMICAL. Cikin ikon Allah ya samu aiki da matatar man fetur ta kasa (NNPC).
Aure nufi na ubangiji Allah ya haɗa shi da salihar mace Fatima daga Daura ya auro ta. Tana da kwalin digirin inda ta karanta B. Ed Social Studies. Bayan auransu ne ta fara aikin koyarwa a Unity Kwatarkwashi. Har ta samu cigaba, aka ba ta mukamin principal. Daga baya aka maido ta Zonal Office na Gusau a matsayin Director, inda ya rage ma ta shekara ɗaya ta ajiye aiki.
Shekarar su biyu da aure sannan Allah ya basu haihuwar ɗa namiji, wanda aka raða ma suna Habib.
Shekarar Habib 10 Haj. Fatima da Habib ke kira da Momi bata sake haihuwa ba. Hakan yasa Alhaji karo aure, sam Momi bata damu ba, sanin halin Alhaji da ta yi. Zuwan Hajiya Hafsat ya kara tabarbara gidan bayan tayi haihuwa biyu wato Labiba da Habiba wadanda shekara uku ne a tsakanin su.
Alhaji ya sake gina wani tamfatsetsen gida a shiyar samaru. Part uku ne a gidan. Nashi ne a tsakiya, sai na Momi a bangaren dama, sai na Hajiya a hagu. Kowacce sashen yaran ta na ciki. Sai boys quarters daga gefe na masu aikin gidan. Akwai wadataccen fili a gidan wanda aka kawata shi da shuke-shuke ma su ban sha'awa.
Cikin ikon Allah Momi ta sami ciki. Ciki ya isa haihuwa ta sunkuto ɗiyar mace sankaceciya. Ta ci suna Zainab sunan mahaifiyar alhaji. Sam ya hana a boye sunan.
Sai dai sukan yi alkunya da kiranta Auta.
Arziki nata kara yawaita ga Alhaji, amma hakan besa shi ya yalwata iyalinshi ba. Store din kayan abinci shake da kayan masarufi. Amma babu mahadi irin su kayan miya, nama, juice da sauran su. Sai dai duk mai ra'ayi ta siya.
Hajiya bata aikin komi, bata sana'a. Momi ce dai ke ajiye duk wani abu da zasu bukata ita da ya'yanta na more rayuwa tana ajiyewa. Hakan ya jawo tsanar Momi a zuciyar Hajiya.
Tsaye take akan tarbiyya da ilimin ya'yanta. Duk wasu abubuwan da yara ke bukata bata jiran Alhaji yayi zata yi, wani sa'in har ta hada da su Labiba ba dan a gode mata ba.
Akwai tazarar shekaru goma sha biyar tsakanin Zainab da Habib.
Hakan yasa duk wata dawainiyya ta Zainab in dai yana gida shi ke yin ta. Shakuwa mai karfi ce a tsakanin 'Yan uwan biyu..
Zainab nada shekara biyu, Habib ya kammala secondary school ɗin shi. Ya samu gurbin karatu a Bayero University Kano (BUK).
A hankali Zainab na girma na dada wayau, ba ta da hatsaniya irin ta yara, sai dai ba ta barin ta kwana duk wanda yai ma ta nan take take ramawa, shiyasa bata da riko ko kadan.
Bayan kammala primary din ta ne, Momi tayi ruwa da tsaki Zainab ta tafi FGGC Bakori, wanda Daddy ya ce sai dai da kudin Momi dan shi ma haka ya taso a makarantar gwamnatin. Haka Momi tasa Zainab FGGC Bakori. Habib ya dauki nauyin duk wani abu da Zainab za ta bukata na makaranta.
Su Labeeba da Habeeba na karatu a PRINCE INTERNATIONAL SCHOOL.
A can Zainab ta hadu da k'awarta Jidda Umar. Ita kuma suna kiranta da Zee Gumi .
Zainab bata da wata kawa da ta wuce Jidda wacce suke unguwa ɗaya basu san juna ba. Sun matukar shakuwa da juna, wanda har gidansu an san amince da ke tsakaninsu.
Zainab na JSS 3 Hajiya ta hura ma Daddy wuta dole ya maido su Labeeba makarantar da Zainab take, ba yanda ya iya dole ya maido SS1 nan.


**************
Duk term in zasu koma makaranta da kyar Daddy ke fidda kuɗin provision ya basu. Kudin basu taka kara sun karya ba.
Ganin halin da mahaifin su ke yi yasa Habib duk term zai kara masu da na shi, tunda yana koyarwa a FCET Gusau.
Momi ma ta kara masu, daga baya ya hana Momi shi ke komi na Zainab. Ganin cewa duk abinda yake ma su Labiba Hajiya ba taba bude baki tayi godiya ba, sai dai ta biyo da kananan maganganu yasa ya daina. Sai dai in ya siya Momi ta dibar masu.
Kullum nuna ma Habib da Zainab muhimmancin su Labiba take a matsayin su na 'Yan uwa jini daya. Sam bata damu da duk abinda Hajiya zata yi ba.
Habib yayi aure ya auro Jamila yar Zaria ce. Yanzu take shekarar karshe a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, tana karantar Shari'a law. Haka take jeka ka dawo.
Girmama Momi da take yi, ya siyo mata kauna a wajen Zainab. Duk mai son Momi bata da kamar shi. Halin kirki na Jamila yasa suke dasawa da Zainab, ta su ta zo daya sosai.
Tana da kyauta, dan ta kan sa kudin ta ta siyo abubuwan da ta san Momi da Zainab naso ba tare da sanin Habib ta kai masu.
Watan Anti Jamila goma ta haifo danta namiji, mai kama da ubanshi sak. Yaci sunan Daddy, Isma'il ana kiran shi da Sultan.

Kwanaki sun ja, har su Zainab an shiga SS1 a lokacin tana da shekara goma sha hudu. Alamun 'yanmatanci na bayyana a jikinta.
Tun Zainab bata fahimtar halin mahaifin su har ta gama karantar sa tsab. Ita bata san wani dadin uba ba. Idan ta duba suturarta rabi da kwata duk babu kuɗin Daddy a ciki. Dan daga sallah sai sallah yake masu dinki, Shima kala biyu, dan dai duk masu tsada ne.
Idan taje gidan su Jidda har ji take ina ma ace baban Jidda ne mahaifinta, yanda suke zama suyi ta hira tare.
Daidai da pad da inner wears na Jidda babansu ke siyo ma ta. Rayuwar gidan na matukar birge ta.
Hutun nan da suka koma su Labeeba za su karasa jarabawar su ta NECO da su ka fara aka samu tsaiko suka dawo gida. In da Zainab zango daya ya rage ma ta ta shiga aji Shida (SS3).

check out chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu for more exciting stories

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now