DOGARO DA KAI

1.4K 99 7
                                    

DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August,2016

{11}
Cikin azama ta tashi ba tare da ta bari sun gan ta ba,cikin motar ta shige Habiba na kiranta ba ta ko kula ta ba.
Jingina ta yi da seat ɗin motar ta na tunanin mi ke shirin faruwa da ita?.
"Allahumma laa sahla illaa maa ja'altahu sahlan wa anta taj'alul hazna idha shi'ita sahlan". Ta ke ta nanatawa, har Habiba ta iso rike da ledoji biyu a hannunta.
"Sis Beeba kiyi driving ɗin, I can't drive in this mood".
"wai mi aka yi ma ki ne?".
"ba komi kawai dai ban jin dadi ne".
Addu'ar ta cigaba da nanatawa har ta ji tukukin da zuciyarta ke yi tayi sanyi.
A hankali ta shige dakinta tasa mukulli ta kulle, kwanciya ta yi tana tuni yanayin da ta hango Hafeez da Jidda.
Kuka Jidda ke yi na fitar hankali, Hafeez ya dukar da kan shi tare da tallabo kuncinsa. Ya kasa jure kukan Jidda, handkerchief ya fiddo ya matso kusa da ita ya hau goge ma ta hawayenta, ta kwantar da kan ta a kan kafadarsa, ba ta san mi yace ma Jidda ba ta yi murmushi.
Wani zafi ta ji zuciyarta na yi kamar za ta balle kirjinta ta fito.
Kamar an tsikareta tayi saurin tashi ta faɗa bandaki, alwala tayi ta dawo ta shimfiɗa darduma sallah tayi sallar azahar,Al-Qur'ani ta dauko ta fara karantawa har aka kira sallar La'asar ta tashi ta tada sallah, bayan ta gama azkar din bawan kowacce sallar farilla ta cigaba da karatun Al-Qur'anin daga inda ta tsaya har ta ji zuciyarta wa sai kamar ba ita ce cikin damuwa dazu ba.
Hannuwanta ta daga sama, ta na mai kai ma Allah kukanta hawaye na tsiyaya daga idanunta.
Murmushi ta yi ta mike tare da ninke hijabinta. Ledar shawarma da su ka siyo ta dauka kitchen ta wuce ta juye a filet, ta dawo falo kenan Momi ta fito.
"Auta daga zuwa wajen mai event planner sai yanzu kuka dawo?".
"A'a Momi tun dazu mu ka dawo ina ɗaki, na san bacci ki ke shiyasa ban leko ba kar in tada ki".
"In kin gama ki je ki amso dinkunan nan".
"ai na san sun yi kyau ma tun ban gan su ba. Da kyar fa Kasuna ya gane yanda na yi sketching ɗin design ɗin da ni ke so".
"Allah yasa dai ya gane, ni shirme na dau wannan zane-zanen na ki, kayan su Labeeba kawai ni ke ji su da suke amare".
"kar ki ji komi Momi trust me".
Ta cigaba da cin Shawarma tayi kat! Sannan ta kora da milk shake.
Wani irin nishadi ta ke ji a tattare da ita, sashen su Habeeba ta shiga.
Duk suna zaune a falo da Hajiya.
Ta gaida Hajiya su ka cigaba da hirar yanda bikin zai kasance.
Wajen karfe biyar su ka tafi karbo dinkunansu.
Zaune suke a falon Momi sun baje dinkunan suna kallo, sai yaba tsarin dinkin da kokarin telan su ke.
Labeeba ta gwada Gown ɗin da za ta sa wajen dinner, ihu su ka fasa ganin irin kyan da ta yi ba tare da ta yi Makeup ba.
"Wow! Auta gani ni ke kamar ba ke kika yi design ɗin wannan rigar ba,ji yanda tayi ma Labeeba kamar a jikinta aka dinka".
"Auta dama dinkin kika koya wallahi kina yi da kan ki" faɗin Labeeba. Hajiya ta ce "Lallai Auta akwai baiwa a tattare da ke".
Sai murmushi ta ke ita da Momi ganin yanda 'Yan uwanta ke kurarata.
Da dare tana kwance tunanin abinda ta gani a pinks cafe ya fado ma ta.
Duk yanda shaidan yaso tunzura ta be samu nasara ba. Tunaninta wace irin damuwa Jidda ke ciki da ba za ta iya faɗa ma ta sai dai Hafeez.
Wayarta da ke saman cikinta ta dauko tayi dialing lambar Jidda, ta yi saurin kashewa tun kafin ta shiga, tunaninta mi za ta ce ma Jiddar.
Tana kwance tana saka da warwara, har karfe 11pm, shiru ba ta ji kiran Hafeez ba, ya saba kiran karfe 10pm su yi firar su har 11pm, amma yau shiru. Kamar ta kira shi ta fasa. Kwanciyar ta ta gyara ta yi addu'a ta shafa ma jikinta.

HAFEEZ
Tun da ya dawo daga pinks cafe da su ka hadu da Jidda be sake fita ba, yana part ɗin shi.
Kwance ya ke ya rasa abinda ke ma shi dadi. Ya kai kallo ga katon hoton Zainab da ke a kan bedside drawer ɗin shi. Hoton ya jawo ya rungume.
"Habibty ki yafe ni,nayi ma ki ba dai-dai ba, tausayin Jidda ya sa na aminta da bukatar ta, I didn't mean to hurt you. Bani da yanda zan yi, ba zan iya kallon kwayar idanunta ba in ce bani son ta".
Haka yai ta sambatu har bacci ya dauke shi da hoton Zainab a kirjin shi.

ZAINAB
Sanye take da riga da skirt na lace mai adon pusher pink da blue a jiki. Da yake yau ta kama juma'a hijab ce pusher pink a jikinta, sagale da blue sidebag da flat shoe shima blue samfurin Chanel. Sai pink din bracelet watch dake daure a tsintsiyar hannunta samfurin IWC ita ma pink.
Siraran labbanta dauke da pink din jambaki, eye lashes ɗinta da suka yi gazar-gazar su ka kara ma idanunta kyau.
Duk wanda ya kalle ta sai ya sake kallo.
"Momi dan Allah ki ban aron motar ki in je school yau lakca ɗaya gare ni, kinga su Yaya Labeeba zasu yi amfani da motar anjima".
"ki dauka amma kar ki bari a ce mun an ganki kina rough driving".
"In Shaa Allah Momi na ta kaina".
Tuki take cikin natsuwa ta karya kwanar gidan su Jidda. Ta yi parking, ta fito rike da leda a hannunta. Da sallama ta shiga, Umma da ke sharar tsakar gidan ta amsa.
Zainab ta karaso ta gaida ta, sannan ta ajiye ledar hannunta, tayi saurin amsar tsintsiyar hannun Umma.
"Umma kawo in cigaba".
"A'a Zainab kin yi gayunki za ki ɓata da kura".
"ba komi Umma". Ba yanda Umma ba ta yi da Zainab ba amma taki.
Jidda ta fito daga wanka daure da zani, ganin Zainab yasa ta ji faduwar gaba.
"Sai na ma ki bulalar makara yau".
"sai ki bada himma yan mata".
Ta wuce ɗakinta. Zainab ta karasa sharar.
"ledar miye a hannunki?".
"kayanki na na ankon bikin su Yaya Labeeba jiya na amso su daga wajen tela".
"nawa su ke da kudin dinkin?".
"ba ni son iskanci Jidda".
Gasu nan in kin ga dama ki yadda bola.
Murmushi tayi, tana mamakin irin halacci na Zainab. Daga kasan zuciyarta tana jin wani irin nauyi kamar an dora ma ta dutse.
Sun fito ta mika ma Umma kayan da Zainab ta kawo ma ta. Umma tayi ta sa albarka su ka fita.
Har su ka isa school babu wanda yace uffan a cikinsu, kowa da abinda yake rayawa a cikin zuciya. Jidda ta fara fita, sannan Zainab ta samu wuri tayi parking motar. Wayar Jidda ta dau kara tana neman agajin a dauke ta.
Zainab tasa hannu ta dauka, ga mamakinta number Hafeez ce baro-baro a allon wayar. Zama tayi cikin motar ta amsar wayar.
Be jira sallamarta ba ya fara magana.
"Jidda! Na kasa samun natsuwa a tattare da ni tun jiya da mu ka rabu, kunyar kiran Habibty ni ke, duk wasu kalamai na sun kare ji ni ke daga nayi magana za ta gane abinda mu kai ma ta.
Jidda kin san irin son da ni ke ma Zainab, ita ce macen da ni ke ganin girmanta saboda kyawawan halayenta, ita ce wacce ke hanani abu kuma in hanu saboda kwarjininta. Rasa Habibty a rayuwata rasa farin ciki na ne.
Why Jidda? Ina tsaka da tsara yanda zamu gina rayuwar mu da Zainab kin zo kin wargaza. Kin san Jidda da zafin kishi, kiyi hakuri na canza tunani ba zan iya auran ki ba, nagode da soyayyarki a gare ni".
Be jira tayi magana ba ya kashe wayar. Wani huci mai zafi ta fesar, zuciyarta na azalzalarta taje ta samu Jidda.
Zaune ta iske Jidda ta kifa kai akan teburin da ke lecture hall ɗin. Dafa ta yi, tare da mika ma ta wayarta, wadda ta riga ta goge kiran da Hafeez yayi.
Har malamin da ke daukar su CHEM 351 (Polymer Chemistry) Dr. DanAzumi ya shigo.
Ya fara lakca ɗin shi akan PROPERTIES OF BULK POLYMERS. Jidda da hankalinta sam be kan abin da ya ke koyawa ta yi nisa cikin duniyar tunani. Zainab ta taɓo ta ganin Dr. DanAzumi ya doso wajen da su ke.
Jidda ta dawo cikin hayyacinta a sa'ilin da Dr. DanAzumi ya watso ma ta tambayar da ba ta san ta yanda za ta amsa. Ai kuwa ya nuna ma ta hanyar waje, haka ta dau jakkarta ta fita.
Zainab ta girgiza kai, tausayin Jidda ya kamata.
Suna fitowa ta hango Jidda tsaye ta na waya.
"Hafeez ka taimake ni ka so ni ko da rabin son da ni ke ma ka ne, ban san yanda na fada soyayyarka ba, Hafeez! I love you, I can't live without you".
Zainab ta yi tsaye galala ta na sauraren wayar da Jidda ke yi.

chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu.

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now