BABI NA SHA BAKWAI

1.4K 117 2
                                    

DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August,2016
{17}

Murmushi ya sakar ma ta, ya kasa sauke idanun shi a kanta. Ta yi saurin sadda kanta kasa,wani irin maganaɗisu ke fizgarta.
"Zee mi ki ka tsaya yi ne?". In ji Abdul
"Allah ko kin ki sai kin siya mun Chocolate ko orange juice ɗin da ki kai man alkawari".
  Jin su kawai ta ke.
"Zee kin mun laifi".
Kallon shi kawai ta ke, ta na mamakin abinda ya kawo shi Riyadh.
  Jin furucin shi ta yi "kaddarar ganin Zainab ya kawo ni".
  Kallon shi ta yi. Ji ta yi an fizgo hannunta, ta juya ta ga wa ke ma ta wannan aika-aikar.
"Yasmeen sakar mun hannu".
"ba'a saki kin zo kin wani yi tsaye nan gun wannan nutumin".
Ta na son ta ce ma ta Samir Alkali ne ta kasa.
  Ba ta da yanda za ta yi tabi Yasmeen. Cikin azama ya biyo bayan su, yana kissimawa ranshi abubuwa da dama.
  "Yasmin shi ne fa da ni ke ba ki labari".
  Tsalle ta yi kamar za ta kada Zainab.
"He is handsome".
"Uhm ni dai mu je, kin ga bin mu yake".
  Sun isa wajen da za su sayi Chocolate babu, sai dai ice-cream ta siya ma su kowa ɗaya.
   Waige-waigen in da za ta gan shi ta fara. Sun koma wajen da su ka zauna su na ta fira tsakanin Abdul da Yasmin ba ta ma san abinda su ke cewa ba. Hankalinta ba ya jikinta.
  "kar dai in kara rasa shi a karo na uku".
  Ice-cream ɗin da ta ke ta juyawa da cokali har ya fara yin ruwa, tun bayan cokali ɗaya da ta kai bakin ta. Hannu ya sa ya amshi robar, tare da kafe ta da idanunshi ma su firgitarwa.
  "What are you thinking of?".
"Nothing".
"ban yarda ba, tun da ku ka dawo ina kallon ki".
"tunanin gida ni ke".
"Good! By the way am Samir Alkali by name and you?".
"Zainab Isma'il Gumi".
"Nice name, za mu iya zama abokai?".
Girgiza kai ta yi alamar "Eh".
"Thanks, ashe dai gara da na zo garin nan, Allah ya san zan hadu da ke".
"Mi ka zo yi?".
"wani aiki na zo yi da TIGER PRINT FASHION DESIGN".
"That's wonderful".
"mi ki ke a Riyadh ke ma?".
"karatu na zo yi ".
" Ina ki ke karatun?".
"Raffles Design Institute ".
" MashaAllah! Ashe ina tare da 'yar uwata fashion designer, kuma yar garinmu right?".
Murmushi ta yi haɗe da gyada kai.
"ba ni lambar wayarki mu rika gaisawa, zan yi kamar sati biyu kafin in koma Nigeria".
Ta karanto ma shi, ya yi saving tare da kiranta ita ma tayi.
            *******************
SAMIR ALKALI
  Kwance ya ke a cikin hotel ɗin MENA GRAND KHALDIA HOTEL dake a khazan street.
   Ya kura ma screen ɗin wayar shi idanu,wani irin shauki ya ke ji game da ita. Hoton da ya dauke ta yake ta kallo.
  Yanzu yake jin lokacin ya yi da zai bayyana soyayyar shi a gare ta. Tun shekarun baya da ya haɗu da ita a JIFATU ENTERPRISES ya kamu da sonta, ya yi nemanta har ya gaji. Kwatsam! Su ka haɗu a filin jirgin saman Sokoto.
  Sai ga shi Allah ya kara haɗa shi da ita a Riyadh. Tabbas! Akwai boyayyen lamari a tattare da su.
"I can't hide it anymore am in love with her,she's like an angel".
   Washegari tun da ya fita be samu kan shi ba sai da dare, wayar shi ya jawo daga chargy lambar Zainab ya lalubo da ya yi saving da MY BETTER HALF.
    Gyara kwanciyar shi ya yi, daga can bangaren ta dauka.
"Amincin Allah ya tabbata ga wannan tsarkakakkiyar ruhin".
"Amin tare da kai".
"Kin tafi kin bar zuciya ta cikin taraddadi, hidimomi sun hanani jin sanyayyar muryar ki da ke gusar da duk wani rashin walwala da ke tattare da kowane gangar jiki".
"uhm banda zolaya fa Samir".
"babu zolaya, daga cikin zuciya ta ne, Zainab I can't hide it to you, I love you so very much ".
" Uhmmm".
"ba ki ce komi ba, ko ban kai wannan matsayin ba".
"ni ban ce ba".
"toh in haka ne, ki taimaki wannan marayan da ke bukatar wacce za ta kula da shi ta bashi dukkan soyayyarta".
"uhmmm Samir kenan".
"Zainab please say something, kar kisa na kasa bacci".
"Baccin ka za ka yi cikin kwanciyar hankali".
"A'a sai na ji something sweet from your mouth".
"Just sleep like a baby in his cradle, ka sa a ranka cewa there's someone that loves you ".
   Wayar ta kashe. Murmushi ya yi, yana jin maganganunta na yawo a cikin kwakwalwarshi. Cikin wani irin yanayi na farinciki ya kwanta.

ZAINAB
Mirginawa ta yi tare da rungume filo, ta na jin tsirgawar wani abu a dukkan sassan jikinta.
" hahaha Love birds".
"Yasmeen gidanku".
"ana so ana kaiwa kasuwa, kwana biyun nan naga har fresh kin yi,please Zee ki kula da shi na ga kina wani basar da shi, kar ki bari ya kuɓuce ma ki naga ki na sanyi-sanyi ki rike shi tsam kada shi ma a ma ki sagegeduwa irin wancan da ki ka ba ni labari".
"wannan karon I won't let him go, ina ma shi son da ban taɓa yi ma wani mahaluki ba, bayan iyaye na".
    Gyara kwanciyar ta yi, tare da lulawa duniyar tunani.
       *************
"My better half kin san gobe zan koma early in the morning, anjima ki shirya za mu fita Please don't say NO! Samir needs you in his life".
"Alright Mon Cheri, kar ka yi kuka your wish is my command".
"say something that will make me happy right now".
"I love you with you with all my heart, body and soul ".
" Xoxo honey bunch".
"Cheii! Haram fa".
  Murmushi ya yi, tare da kashe wayar yana jin wani irin nishaɗi.
     Zaune suke a NAJD VILLAGE RESTAURANT da ke kusa da PRINCE SULTAN UNIVERSITY. Traditional food aka kawo ma su, su na ci cikin nishaɗi kamar masoyan da su ka dau shekaru a tare.
"My better half I can't stop saying that we're meant for each other".
"You're my missing rib that am looking for".
  "Awwwn don't tell me that am the Mr. Right?".
"You don't have to ask question, only my eyes can tell you".
  "Am the luckiest person in this world, your words drives me crazy Babe".
"Ooh Mmm Gee! (OMG Ooh My God), I feel like am in the heaven. Your words are killing me Sam! ".
" Promise me da kin dawo gida zan je in ga Daddy,ina kara tsufa Zee I want to settle down and have a family".
"In Shaa Allah! Da na dawo Boo".
   "Mu je ki raka ni wani waje".
"Look at the time, it's getting late. Na san Yasmeen na can na nema na".
"Yasmin ta fi ni ko?''
"A'a ta ya za ka ce haka, na ga mun dade ne mun yi 2hrs a wajen nan".
"Ok! Mu je in kai ki, tunda you can't spend your time with me. Good thanks for everything".
"Sam! Ba haka ba ne, understand me mana, abinda ba zan yi a gida ba bani son in yi shi a nan kasan in gida ne ba wanda zai bari mu fita haka for a long time a waje, sannan kuma in kara raka ka wani waje,haba Samir ka yi mun adalci mana".
   Tsawa ya dakata ma ta.
"Keep quiet, I didn't want to hear anything from you. Kin nuna man iyaka ta".
"Yes! Ka faɗi duk abinda za ka faɗi, amma ni Zainab ba zan bi ka ko ina ba daga nan, don't think am fool, ko irin matan nan ne wadanda Samari ke takawa, you've made a mistake,coz I always stand by my self".
   Fuuuuu ta dau jakarta ko waigowa ba ta yi ba.

  Hey! This is neither breakfast nor lunch..
  In Shaa Allah anjima ina nan tafe da chapter 18. Just pray for me kada wani abin ya hana ni typing.
   Thanks for all your comments via my inbox, SMS, whatsapp messenger, wattpad followers. I can't find a word that suit my appreciation to you, all I can say is I LOVE YOU LOADS DEEP FROM THE HEART ♥ THAT CARES.
    Ayeesh na maku barka da juma'a.

  Drop your comments and likes at chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu.

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now