BABI NA SHA BIYU

1.6K 123 9
                                    

DOGARO DA KAI
  ©Ayeesh Chuchu
August,2016

   {12}
Murmushi ta sakar ma ta bayan sun haɗa ido.
Ta kasa motsa kafafunta daga daga in da take.
"mu tafi gida, ko akwai abinda za ki yi ne?".
Girgiza kai ta yi, Zainab ta yi gaba, Jidda na biye da ita a baya.
Suna cikin tafiya Zainab ta ce "Wai mi ya same ki ne duk kin canza?".
"Ba komi ban jin dadin jikina ne".
"A'a Jidda kar mu soma yar haka da ke, akwai abinda kike ɓoye man da har ya fara shafar karatunki".
"ba fa wani abu ba ne Zee".
"hmmm shikenan ai".
Wayar Zainab ce ta dau kara,har ta katse ba ta dauka ba, aka sake kira shi ma haka.
"Zee wayarki na ta ringing kin ki dauka kuma na san Hafeez ne".
"ban yi niyyar dauka ba idan ya sake kira ki dauka ai kun fi kusa".
Jidda da take wa ta zufa ta keto ma ta.
"kamar ya mun fi kusa?".
Zainab da ke ta addu'a cikin ranta dan ta yi controlling mind ɗinta kada ta kai ga zagin Jidda.
Murmushi ta yi mai kama da yake.
"ai kin san duk wani abu da ya shafe ni kafin Hafeez ya tambayi kowa ke ce ta farko, saboda yadda da amincin da ke tsakaninmu".
"Hakane Zee".

HAFEEZ
Tunda ya tashi da safe ya kasa fita wajen aiki, yana ganin kiran Manager ya yi biris da kiran.
  Dole ta sa ya kira Jidda dan zuciyar shi sam ta kasa yarda da bukatarta.
Kiran Jidda daga baya ya kara dagula ma shi lissafi, ga Zainab ya kira ta ki daukar wayarshi.

ZAINAB
Ta na sauke Jidda gidan Yaya Habib ta wuce. Sultan ya rugo da gudu ya dare ta.
"sauka kar ka karya ni,ina Momi na?".
"tana ɗaki ita da Momi, nima yanzu na dawo school ina jiran Abba ya dawo mu tafi masallaci".
"Good boy,je ka wajen Haule ta ma ka wanka kafin Abba ya dawo"..
Kaciɓus su ka yi da Aunty J.
"A'a yau Auta ce a gidan, ai na yi zaton kin manta hanyar gidan nan, watan ki biyu rabon da ki tako gidan nan".
"aiki ke man yawa ai kin sani, ni na ma manta ban taho ma ki da kayan ki ba, daga school nan na wuto da motar Momi na san dai zan sha faɗa".
"lallai ko ni ba ni ba ta hakuri".
"au haka za ki ce Aunty J?".
"Eh mana kin dauke ma Momi na mota, ki yi zuciya ki sayi ta ki mana kina da kuɗi ba za ki fidda ba".
"tab! Babu bajet ɗin mota a cikin kudina, ina ma ki ce in je in sauke farali".
"wannan Momi ko yayanki za su kai ki,tsaya ma na ganki wani sukuku kamar kina cikin damuwa".
"ba kama bane, ina ciki wallahi aunty J, Allah ma ya taimaka da sai dai ku ji zuciyata ta yi bindiga".
"mi ya faru?".
"wai ni Hafeez da Jidda za su yaudara duk irin yanda na aminta da su".
"kamar ya ban fahimce ki ba?".
"Jidda ke son Hafeez kuma ya amince zai haɗa mu dukka ya aura".
Ta fashe da kuka mai ban tausayi.
"Aunty J ina son Hafeez, shi ne First Love ɗina, sai da na sha wuyar gyara shi sannan daga sama Jidda ta mun haka".
"Auta! Saurare ni da kyau ".
" Ina saurarenki".
"Shekarar ku nawa da Jidda?".
"shekarar mu goma a tare".
"Good! Haɗuwarki da Hafeez fa?"
"shekarar mu biyu a tare".
"ki zauna ki yi nazari, amincin shekara goma da biyu ba daya su ke ba. Abin da ya samu Jidda hadda ruɗani, ba son Hafeez ta ke ba, ta kasa ganewa ne kila irin kulawar da yake baki yasa taji ina ita ce, shedan ya kawata ma ta.
  Sannan yanzu idan kin rabu da Jidda ki ce mi ya raba ku? Saurayi? Haba Zainab shi fa namiji be da kunya, yanzu ki zo kuyi faɗa da Jidda abin jin dadin shi ne yace ya hada kawaye biyu faɗa saboda soyayyar shi".
"aunty J bazan iya cigaba da soyayya da Hafeez ba matukar Jidda na son shi, ina da kishi".
"ki nemi zabin Allah dan shine zabi dan haka addu'a ita ce mafita, Allah kadai ya san wacece matar Hafeez a cikin ku".
"na gwammace in rasa Hafeez da a ce gashi can da Jidda".
"Ki dai je ki yi nazari kafin ki yanke hukunci".
"shikenan aunty J".
                ****************
Tunda aka fara hidimar bikin Labeeba da Habeeba ba ta samun zama gida. Kullum tana titi siyo duk wani abu da za su bukata. Dan Momi ta hana su Labeeba fita suna gida ana gyara su.
Hafeez ya rasa gane kan Zainab gaba daya ta tattara shi ta watsar,duk iya bakin kokarinshi ya yi amma abin ya ci tura. Har Jidda ya tambaya ko Zainab ta san akwai wani abu a tsakaninsu, tace ba ta tunanin ta sani dan Zainab ɗin ba ta nuna ma ta komi ba, kila dai shi ya ma ta wani laifi daban.
    Daga gida ta fito za ta je dauko mai decoration ta kai ta Maryam Hall in da za su yi kamu.
  Motar Hafeez ta hango ya karya kwana ya shiga FULBE HOTEL, gefen titi ta gangaro ta yi parking sannan ta fito ta bi bayanshi.
  Shi kadai ta ga ya fito cikin motar, ya nufi bangaren restaurant, a baya ta bi shi. Suna shiga ta hango Jidda zaune, hakan yasa Zainab ta gyara gyalen da ta naɗe kanta da shi rufe kusan rabin fuskarta.
  Waje ta samu inda ba mutane, mai kula da wajen yazo ya tambayi mi za'a kawo ma ta.
"tea ni ke so da chips".
"Ok Madam".
Ta na hangen su Jidda. Ba ta san abinda Jidda ke faɗi ba, yanayin ta kawai ta duba ta ga yanda ta marairaice fuska ta san alfarma ta ke nema.
  Ice Cream ɗin da aka kawo ma su. Jidda ta ɗebo ta kai cokalin saitin bakin Hafeez. Ya kauda kai, Jidda ta juyar da kanta gefe. Kafadarta ya dafa ta juyo ya sakar ma ta murmushi, ita ma ta maida ma shi martani.
A hankali Zainab ke kurɓar shayi ta na haɗawa da chips ta na kallon su Jidda da ke ba juna ice-cream. Wayarta ta saita su da ita taita daukarsu huto. Sannan ta dauki video.
  Murmushi ta yi, ta taso a hankali ta isa gaban teburin mai kula da sashen restaurant ɗin, ta fiddo kudi ta ba shi.
Cikin karfin hali ta isa gaban su Jidda.
"Jidda idan na ce bana son ki nayi karya, sai dai ki san wani abu son da ni ke ma Zainab ya ɗara na ki nesa ba kusa ba. Da son Habibty aka halicce ni".
"Na san da haka Hafeez, duk da haka ka taimaka ka ba ni koda dan kankanin gurbi ne a cikin zuciyarka da sannu zan cike duk wani gurbi da ya yi saura da soyayyata".
"Na yarda na amince, zan aure ki amma sai na auri Zainab".
  Ganin cewa ba su ma san da zamanta ba, yasa ta ɗaga hannuwanta ta yi ma su tafi.
Firgigi su ka ɗago kai, ganin Zainab tsaye gabansu yasa kowannensu duburcewa.
"Inyee love birds! Abin ma yar wariyar launin fata ce shi ne babu gayyata in zo in raka ku".
Kasake su ka yi, kowannensu da abinda yake sakawa a zuci.
"kun yi shiru, wato banda amsa. Ok asha soyayya lafiya. Jidda kar ki manta da kamu fa anjima 5pm".
Ta juya ta barsu a wajen.
"kin ga abinda ki ka jawo man Jidda shikenan Habibty ba za ta kara yadda da ni ba, na so ni na fara faɗi ma ta ba wai ita ta gani ba".
"ka yi hakuri Hafeez".
"wane hakuri Jidda? Idan na rasa Zainab ke ma ki tabbatar da cewa kin rasa ni".
  Ya tashi ya fita da sauri.
Tafiya take a mota wani irin ɗaci ta ke ji a makoshinta. Sai da ta yi kuka sannan ta ji zuciyarta ta yi sanyi.
Ta dauko mai decoration sannan ta wuce gida dan su shirya ma kamu da za'a yi.

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now