BABI NA SHA TARA

1.4K 92 4
                                    

DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August,2016

I dedicated this chapter to Sanah Matazu, Halima Wasagu, Barr. Jam33lerh, Lubie Maitafsir, Maijidda Musa.

{19}
Address ɗin da Yasmeen ta turo ma ta ta nuna ma mai taxi ya kai ta har gaban CENTRIA.
  Yasmeen ta hango tsaye, fizgo hannunta ta yi tasa kyalle ta rufe ma Zainab idanu.
"Yasmeen mi ye haka? Ba ni so fa".
"matsalata da ke rashin hakuri".
     Wani kayataccen waje su ka shiga.
"Mmmmmm Yasmeen wannan kamshin mai dadi fa na minene?".
  A hankali ta zare kyallen da ke daure da idanunta. Ta kai duba ga yanda wajen ya tsaru da kalolin da tafi so purple and pink.
  "Success will always knock your door Zainab".
  Haka ta ga an rubuta cikin kyakkyawan rubutu. Cake ne mai hawa biyu hade da zanen fuskar Zainab a ciki, shi ma kalar purple da pink.
  Daddadan kamshin turaren shi ya bugi hancinta, ta ware idanunta akan shi ba ta ko kyaftawa.
Shi ma haka a na shi bangaren, tattausan murmushi ne bayyane a saman fuskokinsu. Ji ya ke kamar ya ruga ya rungume ta, amma ina akwai hijabi a tsakaninsu.
  Kalmomi ma su dadi da sanyaya zuciya ya ke fitarwa, wadanda suka jefa zuciyar Zainab cikin wani yanayi da ta kasa tantance abinda ta ke ji.
  "Samir ka shammace ni, komi na ka daban ne".
"haka ke ma komi na ko daban ne".
     Dan karamin partyn da Samir ya haɗa ma Zainab wanda daga shi sai Yasmeen da Abdul, sai ita uwar gayyar. Sun ci sun sha, ta yanka Cake. Sun yi hotuna sosai,daga nan su Yasmeen su ka wuce makaranta in da Samir da Zainab su ka wuce hotel ɗin da su Yaya Habib su ka sauka.
  Sun gaisa da su Yaya Habib sannan shi ma ya koma masaukin shi.

KING KHALID INTERNATIONAL AIRPORT
  Kuka suke kamar ransu zai fita na rabuwa da juna.
"Zee mun shaku da juna, mu yi faða mu shirya ".
" Zaman shekara biyu yasa ina jin ki tamkar yar uwata, kin wuce kawa Yasmeen".
"In Shaa Allah wata rana har Nigeria zan kawo ma ki ziyara".
  Haka wadannan kawayen juna suka rabu suna masu kuka da jimamin rabuwa da juna.
   NIGERIA
Murmushi ta yi tace "nayi kewar ki Momi".
"ba sai kin faɗa ba Auta mun yi kewar juna".
  Farin cikin da ta ke ciki baya misaltuwa, bakinta ya gaza rufuwa kamar gonar auduga.
  Washegari tun bayan da ta yi kalaci tana falon Daddy su na fira, ta na ba shi labarin yanayin karatun ta. Sun dade su na fira da Daddy irin firar da ba ta taɓa yi da shi ba.
"Mamana Allah ya nuna man kin gama karatun nan lafiya, saura aure ya rage ma ki babban burina kenan da ya rage in ga na aurar da ke ga nutsatstsen namiji wanda zai kula da ke ya goya ma ki baya a dukkan al'amuranki matukar basu saba ma shari'a ba".
  Kanta a duke ta na sauraren Daddy.
"kwanaki akwai wanda ya zo da maganar ya na son ki, na kuma gama duk wani bincike na tabbatar da irin gidan da ya fito na yarda da tarbiyyar shi.
Na ba shi izinin zuwa neman amincewar ki".
Kanta ya kulle, tana addu'ar Allah ya sa Samir ne.
  
  Sati biyu cur! Zainab ta dauka ta na zagaya danginta, har Daura ta je ta gaido sauran dangin mahaifiyarta da su ka yi saura. Sun ji dadin ganin ta ta sada zumunci, kwanta uku ta dawo Gusau da tsaraba tsibibi.
  Kwana biyu ta huta, ta tafi Gumi gun dangin mahaifinta,kwana biyu ta dawo gida. Ta bi gidajen su Labeeba da Habeeba.
        *********************
"Auta kin kuwa je gidan Jidda tun da ki ka dawo?".
"A'a Momi, Jidda ce ba ta son zumunci da ni yanzu tunda na tafi wancan zuwan da na yi sai dai ni in ta kiranta, ko a whatsapp ni ke ma ta magana. Sam! Ba ta damu da ni ba, na ga ba dole shiyasa na fita harkarta".
"Gaskiya ba ki kyauta ba, ai kin fi ta har wurin Allah, amma yanke zumunci da ita be dace ba. Shekarar ku nawa tare? Sai yanzu da ya kamata a ce kun rike amincin da ke tsakanin ku, za ku bullo da wani abu sabo".
"Momi ita fa ta yanke alaka da ni, ba ta ban ci da sha ba mun komi na rayuwa na ga gara in kyale ta".
"to ba ki isa ba, ki je ku sasanta kan ku ba ni son sakarci".
"Momi ki....".
"ba ni son jin komi,kin dai ji abinda nace".
  Dole ta sa bayan la'asar ta shirya zuwa gidan Jidda.
    Kallon kanta ta ke jikin mudubi, ita kanta ta san ta yi kyau. Sanye ta ke da riga da siket (skirt) na atamfa, da ya zauna dabas! a jikinta. Ita ta dinka kayanta da kan ta a Riyadh. Ta kafa daurin dankwali, ta yafa mayafin da ya dace da kalar atamfar da ta sa.
  Takalmin kafarta mai igiyoyi hade da tsini kalar golden brown hade da jaka mahaɗin takalmin samfurin Jimmy Choo.
  Cikin takun kasaita ta fito, a harabar gidan ta iske Momi da Hajiya suna fira.
"Momi na dauko makullin motar ki ki ara mun".
"ai fa kin dawo kenan mota ta ba ta kara lafiya".
Murmushi ta yi,ta taka zuwa ma'adanar motocin.
  A hankali ta ke murza sitiyarin motar (steering wheel) har ta isa bakin gate ɗin gidan Jidda. Ta yi horn mai gadi ya buɗe ma ta.
   Ta yi parking motarta gefe.
Ta yi sallama shiru, ta murda hannun kofar ya bude ta sake yin sallama ba'a amsa ba.
  Kutsa kai ta yi ta shiga. Kwance ya ke saman cushion, karar takun takalmi ya ji, ya bude idanunshi. Fes! Ya sauke su akan ta.
  Cikin azama ya tashi zaune. Ya tsinkayi muryarta ta na gaida shi.
"Jidda na ciki ne?". Ta faða fuskarta a daure kamar ba ta dariya.
"Eh ta na ciki".
Dakin Jidda ta shiga ba ta ciki, jin alamar karar zubar ruwa daga cikin bandaki ya sa ta zauna.
  Jidda na fitowa daga bayin ta ci karo da fuskar Zainab. Turus! Ta tsaya suna kallon juna.
  "Bakin Riyadh saukar yaushe?".
"na dan jima da dawowa".
"Allah sarki, kwana da yawa ".
" ai kuwa dai, da ma biyowa nayi mu gaisa".
Ta mike tare da gyara mazaunin gyalenta.
"Zee ba dai tafiya ba?".
"Eh a hanya ni ke".
"Dan Allah ki tsaya akwai maganar da za mu yi".
Ta koma ta zauna ba dan ta so ba.
"please Zee ki yi hakuri na datse zumuncin da ke tsakanin mu, na sa son kai acikin abotarmu. Wallahi kishi ne da sharrin shaidan. Kwanaki ne Hafiz ya canza gaba daya be zama gida, ya tsiri tafiye-tafiye, duk abinda na yi ma shi sai ya nuna ban iya ba. Be da magana sai ta ki,ta ya ya ba zan ji zafi ba? Zuciya ba ta da kashi Zee. Har ila yau zaman mu be daidaita ba. Idan har samun kwanciyar hankalinmu ne Hafiz ya aure ki am ready for that. Da ma tare na gan ku na raba ku Please ki yafe ni Zee".
  "Jidda maganar in auri Hafiz ba ta taso ba, ina da wanda ni ke so, kuma zan aura so ki bar maganar. Yanzu ya rage tsakanin ki da Hafiz, ku zauna ku fahimci junanku wannan zaman be dace da masoya irin ku ba".
  "Da ma can ni ke son Hafiz ba shi ke sona ba, na yi da na sanin abinda nayi. I would've wait for my own charming prince that would give me all the love and care".
" You're late Jidda. Dan haka Hafiz ne last hope din ki, in ma dai ki tsaya ki fahimci abubuwan da yake da wadanda be so inma rayuwar auran ku ya zama kamar filin dambe. Hafiz namiji ne yana da damar kara mata uku. Ki yi kokarin karkato hankalin su, auren shekara daya da watanni ana samun irin wannan matsaloli ai be kamata ba".
"Zee ki taimaka ki ma Hafiz magana na san yana jin maganar ki".
"please stop it! Ni zan ma Hafiz magana kada Allah ya nuna man wannan ranar, ke dai da ki ke mace ki yi tunanin mafita dan zama tare da mijin ki har abada".  "Zee Hafiz botsatstsen hali gare shi".
"ni dai kin ga tafiya ta, ba dan Momi ta tilasta mani zuwa ba da ban zo ba".
  "to ki gaishe ta, nagode. Ni ma ina nan zuwa".
  Tare su ka fito, yana zaune da remote yana canza tasha. Ya bi Zee da kallo kamar be taɓa ganinta ba.
Ita kuwa ko kallon in da ya ke ba ta yi ba.
       **************
"Daddy alfarma da taimako na zo nema wajenka".
  "Ina jin ki Mamana".
"Dama akan karatun da na je na yi ne, naga ya kamata a ce nayi amfani da shi ko dan ni ma in taimaki kasata".
"ta wace hanya ki ke ganin za ki bi".
"Daddy shagon ɗinki ni ke so na bude wanda ya bambamta da shagunan dinkuna a kasarmu, irin shagunan dinkuna na can".
"Eh gaskiya kin yi magana me kyau, yanzu mi ki ke bukata?".
"Daddy kuɗi ni ke so, wanda zan siyo duk abubuwan da ake bukata a can, ina da dubu dari uku a ajiye".
" kamar nawa ki ke so yanzu?".
"duk yanda ka ba ni Daddy".
"to shikenan ki je za mu yi magana da Mominki".
"Nagode Daddy, Allah shi karo arziki mai albarka ".
" Amin Mamana".
  Farinciki fal a tattare da ita,ta wuce bangaren su. Nan ta zauna ta ba Momi labarin yanda su ka yi da Daddy.
"kin ga yanzu Momi da ya ba ni, zan yi ordering irin sewing machines ɗin su da duk abubuwan da ake bukata,amma fa kudin Daddy maida ma shi abin shi zanyi a hankali ina tara ribar da aka samu".
"kin yi dabara gaskiya Allah shi taimaka".
   Haka ta kira Samir ta faɗi ma shi kuɗirinta, ya kuma goyi bayanta tare da karfafa ma ta gwiwa".
                      *****
"Inyee ashe yau muna da cin dadi gidan nan".
"uhmm Momi ba fa na gida ba ne,Samir ne zai zo".
"Oh ni Fatima! Yaran yanzu sam ba ku jin kunyar hirar saurayi. Ni ki ke faɗi ma Surukina zai zo".
  Murmushi ta yi tare da sunne kai.
  Duk wani abu da ta san bako na bukata sai da ta yi. Wannan ne zuwan Samir na farko gidan su Zainab bayan Daddy ya ba shi iznin zuwa zance wajenta.
  Ta yi kwalliya ta kece raini, duk wanda ya kalle ta sau daya sai ya sake kallonta. Ita kan ta ta san ta yi kyau.
Wayarta ce ta dau kara alamar ana kiranta.
"Haba Cheri ba ni son irin wannan wasan, kai fa ka ce kana hanya amma yanzu ka ce ka fasa zuwa".
Murmushi ta yi,cikin sauri ta fito.
  Jingine yake jikin motar shi, ya harde hannuwa a faffaɗan kirjin shi. Tun da ta fito ya ke jifanta da murmushi, ita ma ta na mai da martani.
"Welcome to my home".
Murmushi ya yi "Thanks babe".
  Ta yi ma shi jagoranci zuwa falon Daddy ya zauna, ta koma cikin gida.

    Jiya ban samu damar posting ba. Ga bashin nan na biya. Saura na yau In Shaa Allah.
  Thanks for all your love and care.

  chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu

DOGARO DA KAI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora