BABI NA SHA SHIDA

1.5K 102 4
                                    

DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August,2016
{16}

    Wasu irin kibiyoyi ne ma su kama taurari su ka fito daga idanunsu, ta kasa jure irin kallon da yake bin ta da shi. Ta yi saurin yin kasa da idanunta.
A hankali ta furta "Am so sorry for what had happened, please ka yi hakuri ba da niyya na yi ba".
"ba zan hakura, kin so ki nakasa ni in zama mara kafa".
Murmushi ta yi, "tunda ba ka zama ba ai da sauki".
" ooh! Haka ki ka ce ko? In bar ki da Allah kenan?".
"A'a kayi hakuri dai".
"No! Ga card ɗina nan ki kira ki ban hakuri ba anan ba".
Ta amsa tare da jan akwatinta.
"you can't even say a word of goodbye".
Murmushi tayi tare da ɗaga ma shi hannu.

GUSAU
Farin cikin da ta ke ciki ba ya misaltuwa, ganin ta zaune cikin yan uwanta. Duk su Labeeba sun zo, sai hira su ke ta na basu labarin Riyadh.
  Ta rasa gane wanda yafi wani farincikin ganin ta cikin Momi, Daddy da Hajiya.
  Da dare tare suka ci abinci da Daddy, abinda basu taɓa ba a tarihin rayuwarsu.
  Da dare bayan ta gama duk wata al'adarta kafin ta kwanta. Ta kira Yasmeen da Abdul su ka sha fira.
  Kwanciya ta yi tana tuno arangamar da su ka yi da Samir Alkali. Katin da ya ba ta ta dauko tare da adana lambobinshi a kan wayarta. Kamar ta kira shi da Layin ta na Nijeriya, sai kuma ta fasa, tunaninta mi za ta ce ma shi.
Abu ɗaya ta sani, ta na kaunar Samir Alkali fiye da tunaninta. Kaunar da ta ke ma shi be sa idanunta sun rufe ba, bare ta ji idan ba shi ba ta iya rayuwa. Tana dai jin so da kaunar shi har cikin kashinta da bargonta.
Haka ta kwanta cike da mafarkai ma su dadi duk akan Samir Alkali.
  Washegari misalin karfe sha daya ta shirya cikin riga da skirt na atamfa, sun matukar karbar jikinta, tayi kyau sosai.
"Momi za ni gidan Jidda".
"ki gaida ta".
  Motar Daddy ta dauka, ta isa GRA unguwar da Jidda su ke.
  Ta yi horn bakin kofar gidan, mai gadi ya bude ma ta, ta shiga.
  Ta fito ta na takunta cikin natsuwa, a bakin kofa su ka haɗu.
Ya tsare ta da idanunshi, ya ki ba ta hanya ta wuce.
"Congrat! An yi biki Allah shi sanya alkhairi ya ba ku zaman lafiya da zuri'a dayyaba".
"Hmmm! Kin ban mamaki Habibty".
"Please Hafeez Kar mu yi haka da kai, ka bar kirana da wannan sunan. Ban hanya In wuce".
"ba zan wuce ba, har sai kin faɗi man dalilin ki na kin daga kiran da ni ke ma ki".
"Saboda be da amfani,ka ban waje Hafeez tun rayuka ba su ɓaci ba".
"miye na taɗa jijiyoyin wuya wuce".
Ta wuce ya bi ta da kallo. Fitar da be yi ba kenan.
  "Jidda! Jidda!! Jidda!!!".
Firgigit ta ɗago kan ta. Murmushin yake ta yi.
  "Zee saukar yaushe?".
"tun shekaranjiya ina ta sallama ba ki ji ba, mi ke damun ki?".
"ban jin dadi ne, zauna ma na kin tsayw".
"inyee ko dai kin kunsa ne, tunda yanzu kamar tuntuɓe ake da shi a bakin kofa".
"kai Zee ba ki da dama".
Ta tashi ta kawo ma ta drink da cup a tray.
"kin iske ko abinci ban yi ba".
"laa! Ba komi ai ba bakuwa bace ni".
Su na ta firarsu ta kawayen juna, har azahar ta yi.
Sallah su ka yi. "Jidda girki fa kada mai gidan ya dawo".
"ko Indomie ma dafa".
"Hafeez ɗin ne ke cin Indomie?".
"ban jin dafa abinci ne".
"lallai Jidda mazan da ake tattashin su da abinci, kar ki ce mun haka ki ke wannan kyuiyar dafa abinci?".
"Ina yi Zee but not all the time ".
" hmmm to tashi mu je mu yi tare".
  Tare suka shiga kitchen ɗin, ganin lokaci ya ja su ka dafa jollof ɗin couscous da ya ji kayan lambu da hanta a ciki, hade da  zobo drink da suka jefa kankara ciki.
  Suka jera a dinning room, nasu su ka zuba a filet su na ci suna fira.
  Sallamar Hafeez su ka ji, ya shigo ya zauna.
  "Abincin ka na dinning".
"Ok". 
  Sai la'asar Zainab ta shirya tafiya bayan ta ba Jidda tsaraba. Jidda ta shiga daki ta fito, Hafeez ya kalli Zainab ya ce "har yanzu taste ɗin abincin ki na nan special, ni ina tawa tsarabar?".
"ka tambayi matarka".
"Habibty please ki rika daukar kirana, gaisawa kadai za mu yi".
Ba ta tanka ma shi ba.
Ita mamakin su take kamar ba sabbin ma'aurata ba.
  Sun rako ta har bakin mota, ta tafi. Gidan Labeeba ta biya sannan ta wuce gidan Habeeba.

            ****************
"Hajiya ji ni ke kamar kar in koma".
"duka nawa ya rage ma ku kamar gobe ne ".
" ki zauna kar ki koma kin ji". In ji Momi.
  Daddy da ke zaune sai murmushi ya ke.
"Daddy kana jin Momi ko".
"kyale ta Mamana ke dai ki dage da abinda ya kai ki, da kin dawo ki dawo min da mijin aure shi ne kadai buri na".
  "In Shaa Allah Daddy ai ta mana addu'a".
   Bayan kwana biyu Zainab ta ɗaga zuwa Riyadh da ke Kasar Saudi Arabia.
RIYADH
Sun cigaba da karatun su, in da yanzu dinkuna kala-kala ba wanda Zainab ba ta iya ba, design na abaya duk ta iya. Ta na amfani da karatun da ta ke koya ta sa basirarta wajen zana style na kaya kala-kala yawanci irin dinkunanmu ne na Africa.
  Zaune suke a ðakin ita da Yasmeen suna fira.
"Zee ni ban taɓa jin kin bada labarin saurayin ki ba,kullum ni ce uwar bada labarin Fu'ad".
"ni fa banda saurayi, ada dai na yi shi yanzu kam ya zama tarihi mantawa ma ni ke da shi, mutum ɗaya ni ke so da kauna SAMIR ALKALI. Kuma be ma san ina yi ba, Yasmin I so much love him".
"Kamar ya be sa ni ba?".
"ni kadai ke son shi, sau biyu mu ka taɓa haduwa sai dai ina yawan ganin shi a TV,shi ne namiji na farko da ni ke rokon Allah akan shi a duk sanda na kai goshi na kasa".
"Lallai Zee, to ba ki nemo shi ".
" ta ya zan nemo shi? Ke har katin shi ya bani in kira shi last time da na je gida ban yi ba".
"Ki kira shi ma na kila shi ma son ki yake, I believe that duk zuciyar da ka ke so ita ma ta na son ta ka zuciyar".
"Yasmin I can't, zai ga kamar wani abu ne ya sa na kira shi".
"ba son shi kike ba shiyasa".
"ba ki san yanda ni ke ji bane, ina boyewa ne kawai".
        *****************
Yau tunda ta tashi ta ke jin wani irin farin ciki da annashuwa.
  "Yasmeen tashi tashi, ji na nike kamar ba ni ba".
"Zee what's the secret behind your happiness?".
"Allahu a'alam, tashi ki shirya yau yawo zamu je kawai tunda weekend ne".
"promise me za ki siya mun chocolate ko orange juice".
"I promise you, bari in kira Abdul Hameed kin san shi da son yawo shi ma".
    Sanye ta ke da cikin kimono Red & black,ta sa riga da wando ciki suma Red & black. Turban head wrap ta yi da Red scarf, bakin boot shoes ne aka kafarta ma su tsini,sai bakar side bag black itama.
Fuskarta sai kyalli ta ke.
"MashaAllah! Zee kar ki kashe mutane yau fa".
"Yasmin gidanku".
Dariya ta yi "ai gaskiya na faɗa, kin yi kyau sosai".
" Thanks my honey bunch".
Tare suka jera su uku suna tafiya, Abdul ya ce "yanzu ina ya kamata mu je?".
"beach please Abdul ba mu taɓa zuwa ba".
"toh wane zamu?".
"tab yo ni ina na sa ni ".
" mu tambayi mai taxi ɗin da za mu hau".
"yeah good idea".
  Sun hau taxi su ka tambayi mai taxi beach da ke kusa.
  Al-Rawabi Walk Track ya kai su dake Zubair bn Al awam street. Wajen ya matukar kayatuwa.
  Gefen ruwa su ka samu, suka zauna. Suna fira nishaɗi kwance saman fuskar su.
  "Zee ina alkawari na?".
"Yasmeen acici, mu je mu ga idan za mu  samu Orange juice ɗin ko ice-cream".
  "Abdul ya je siyo".
"da yake ni ne ma rainin wayon ki ba, sai dai dukkanmu mu tafi".
  Tare suka Mike zuwa in da za su samu abin kusa da baki.
    Jakarta da ta faɗi ta duka ta dauka, a hankali ya furta "I've found my missing rib".
Da ɗago dara-daran idanunta ta sauke su akan shi, dan ta tabbatar da Muryar da kamshin na mamallakin wanda ta dade ta na mafarkin ga ni ne.

  Indo Aa'ishah

chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu dan

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now