BABI NA TARA

1.4K 109 2
                                    

DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August,2016

{9}
Fitowar Hafsat kanwar Hafeez ya dakatar da su.
"Mum time ya yi, mutane fa sun taru friends ɗina duk ga su can".
"Ok ki jira a gama arranging sai ki fito".
Aunty J da Zainab su ka fita harabar gidan da aka sa canopy da kujeru anyi decorating wajen.
Kowanne tebiri mutum hudu ne, da abinci da drinks, daga kasan kowacce kujera souvenirs ne a ajiye cikin jakka. Aunty Jamila ta hadu da makwabtanta da suka shigo, suka zauna waje ɗaya dama su hudu ne.
Zainab ta samu waje can gefe karshen canopy ɗin ta zauna, an fara gudanarwa da walima inda mahaifan Hafsat ɗin su ka fito suka yi jawabi, sannan yayanta Hafeez ma ya yi.
Hankalin Zainab be ga jawabin da su ke yana kan wayarta da ta lula duniyar bincike, duk wani abu da ya shafi fashion design kama daga Nigeria har sauran kasashen ketare da suka shahara a wajen fashion design sai ta karanta. Shiyasa ba a raba wayarta da tarkacen documents da hotuna da tayi saving.
Hatta screen saver na wayarta hoton sketching da ta yi ne na wata wedding gown.
Kamar daga sama ta ji an ce "ke yar karamar yarinyar nan".
Dago kai ta yi ta sake harararsa.
"ki bi a hankali kar idanun su faɗo kasa". Murmushi ta yi, ya ja kujera ya zauna.
"How comes ki ka iya girki haka?".
"It's my passion!".
"Wow! Ashe muna da babbar chef a Gusau I didn't even know?".
"wannan ne yi ne na farko,ban san zan iya ba ma".
"ehen! Da ma ai sai an gwada akan san na kwarai,your food is yummy".
"Thanks". Ta faɗa a takaice dan ta gaji da surutun sa, ita ba gwanar iya magana.
"Na takura ki ko? Don't mind this Hafeez he's talkative".
"Alright Mr. Talkative".
"ba sunana kenan ba, am Hafeez Sulaiman Ibrahim,ya sunanki?".
Saboda gajiya da ta yi da tambayoyinsa ga shi ya tsare ta da mayun idanunsa da ke firgitata.
"Zainab Isma'il Gumi".
"Nice name".
Ya miko ma ta hannunsa tare da furta "Friends".
Girgiza kai ta yi.
"why Zee?".
"bana haɗa hannu da maza ni".
"Ok na gane,but can you be a friend of mine? Please don't say no".
Gyada kanta ta yi, alamar "Eh".
Murmushi ya jefeta da shi, tare da hura iska a tafin hannunsa.
Murtuke fuska ta yi,ta buɗe takeaway ɗin jin yunwa na nukurkusarta dan tun abincin safe rabon da ta ci wani abu.
Kamshi ya baɗe wajen. Ta kai cokali ɗaya a bakinta,ta runtse idanunta ta na taunawa cikin natsuwa saboda ɗadin da ke ratsata har kunnuwanta.
Ta na bude ido ta sauke su akan Hafeez da ya kura ma ta ido, be ko kiftawa.
"why are you looking at me?".
"naga kin kara kyau ne, komi na ki mai kyau ne".
Murmushi kawai ta yi, dan ita ba ta ga kyan da ake cewa tana da shi ba. Ganin cewa bakar fata gare ta, hancinta ba wani tsawo ne da shi ba sai dai ba za a kira ta cikin sahun marasa hanci ba.
Taɓo ta yayi, "tunanin mi ki ke".
"Nothing, ka daina taɓa ba ni so".
"Ok na daina".
Surutun Hafeez ya ishe ta, dan ba ta son mutum mai surutu. Tsam ta tashi ta bar ma sa wajen, kasa bin ta ya yi sai kallonta da yake har ta bulle ma ganin shi.
Mamakin kan shi ya ke, shi ne yau ke ma mace surutu abin da sam be cikin tsarin sa, murmushi ya yi tare da shafa sumar kan shi da ke kwance luf, baka kirin kamar ana sa ma ta relaxer.
"She's a nice girl". Ya furta tare da mikewa yayi wajen da ake ta daukar hotuna.
Zainab na tsaye ita da Aunty Jamila taga mai camera a gabansu, sai ga Hafeez da Hafsat sun karaso wajen.
Hafsat ta ce "hoto zamu dauka".
Murmushi tayi ta gyara tsayuwarta aka dauke su su biyu sannan su ka yi su duka,sai na karshen da suka yi su uku. Sun yi matukar yin kyau.
Zasu tafi ne Hajiya Laila ta sa aka kira Zainab, ta amshi lambar wayarta.
Suna shiga suka iske Yaya Habib ya dawo shi da Sultan.
"Dama tunanin komawa gida ni ke ga maghrib har ta yi, tunda Allah yasa kun dawo sai ka maida ni gida".
"kin raina ni yarinyar nan, wato ga direba ko, sai ki san yadda za ki yi".
"Please Yaya Habib".
"Mu yi sallah ni in kai ki ba sai an ma ki gori ba".
"naga mai fita daga gidan nan da mota".
Sallah su ka yi,tare suka fita dukkansu.
"Yaya idan anzo Al-Ameer restaurant ka tsaya dan Allah".
"Mi za ki yi a Al-Ameer ɗin?"
"Liver kebab nike so".
"yarinyar nan kin cika kwadayi".
"mu ma a siyo da mu".
"toh ka ji aunty ma na so".
"ai duk jirgi ɗaya ya kwaso ku".
Sun tsaya Al-Ameer, yaya Habib ya fita ya siyo sannan su ka wuce.
*****************
Fitowarsu daga Chemistry practical kenan, Zainab ta ce "Ina jin dadin practical ɗin nan na Mr. Christopher".
"Ko ni,he is one of the best lecturers a department ɗin nan".
"Ba ni jin zan iya tsayawa jiran Danliti yau, mutum yai ta yawo cikin makaranta tun safe har yamma".
"mu jira shi mana, ni fa ban dauko ko kwandala ba".
"mu taka zuwa bakin titi, za mu samu taxi".
Wayarta ce ta yi kara alamar text ya shigo. Ta bude kamar haka:
"Ki turo da address ɗin ki ga sakon nan zan bada a kawo ma ki, nagode kwarai ɗiyata.
Hajiya Laila".
Murmushi ta yi, tare da tura in da take.
"murmushin mi ki ke?".
"kudin abinci da nayi ne na ranar Saturday ɗin nan da na baki labari".
"Inyee My Zee za'a ji dumus".
"wane dumus,ke dai ayi sha'ani".
Tafiya su ka cigaba da yi har su ka iso bakin titi. Wayarta ta yi kara alamar kira, ta ɗaga.
"gani nan na wuce FCET Gusau, ina zan same ku?".
"muna bakin titi za mu tafi gida".
"ku jira ni in the next 5mins".

You'll come across of many mistakes /typing errors, I didn't edit the chapter. Am so sorry for the inconveniences.

Ayeesh loves you irin da yawa da yawa nan. Lol

Waiting for your comments and vote on Wattpad @ayeesh_chuchu.

What's your view about Zainab's lifestyle?

chuchungaye.wordpress.com

DOGARO DA KAI Où les histoires vivent. Découvrez maintenant