BABI NA BIYU

2K 133 14
                                    

DOGARO DA KAI

©Ayeesh Chuchu

July,2016

{2}
Tunda ta dawo ta lek'a ɗakin Momi bata nan ta shige ɗaki, sai da Momi ta dawo daga ɗayan sashin Hajiya, ta shigo ɗakin taga Zainab kwance. Ta ce "auta manya mi aka yi kuma daga dawowa kika kwanta bayan kin san gab ake da kiran magriba". Beeba ta muskuta ta ce "Momi naga har jibi zamu koma Daddy be bada kuɗin provision ɗinmu ba". Momi ta yi murmushin yake tace "ina ga hiɗima ce tayi ma shi yawa, be manta ba. Gobe na kara tuna ma sa, Idan Habib ya shigo kuma ko gobe ne sai ya kai ki kuyi ba san kin jira daddyn ba, ai an rage ma shi wani nauyin tunda ba ke kadai bace ba".
Kaða kai kawai tayi ba dan tayi na'am da abinda Momi ta ce ba, illa dai dan ta nuna ta gamsu.
Bayan ta sha jin gumurzun da ake akan provision ɗin su na makaranta.

Washegari da safe Zainab na gama sallar asuba, ta daidaici lokacin shigowar Daddy, tayi saurin tashi daga kan daddumar sallarta, bata ko tsaya linkewa ba tayi hanyar part din shi dake tsakiyar gidan. A falo ta iske shi ya kafa ma talabijin idanu da farin gilashi manne a idanunsa yana kallon NEWS HOUR a tashar ALJAZEERA.
Ta durkusa har kasa ta gaida shi, ya amsa ba tare da ya kai duba gare ta ba . Idan da sabo sun saba da hakan, tayi kwafa ta ce "Daddy gobe muke komawa school In Shaa Allah".
Yace "toh ya aka yi ne?", tace "dama kuɗin provision zan tuna ma nasan hiɗima ce ta sa ka manta".
Girgiza kai yayi,yana jin har acikin zuciyar shi yafi son Zainab ko dan iya maganarta da kuma addu'ar ta gare shi duk kankantar abinda zai bata, koda za ta ɓata rai sai bayan idon shi.
Ya ce "ku uku ne ko?" tace "eh Daddy".
Yace "ok ranar Talata na ba Habib kudin school fees ɗin ku, ya je ya biya. Idan ya shigo zai baku bank teller ɗin ku". Yasa hannu a aljihun jallabiya dake jikin shi ya ciro kudi ya kirga yace "gashi nan kuje ke da 'Yan uwan ki kuyi siyayyar da zaku yi". Ta amsa tare da furta "mun gode Daddy Allah shi saka da alheri, ya kara buɗi na alheri". Yace "Amin".
Ta tashi ta fita. Sai da tabar side ɗinshi sannan ta k'irga kuɗin. Wani malolon bak'inciki ya tokare ma ta wuya ba ta san sa'ar da kuka ya kuɓuce ma ta ba. Tayi hanyar side din Momi. Ďakin Momi ta wuce, bayan sun gaisa tace "Auta kuka da sassafe nan". Zainab tace "yanzu Momi a ce kamar Daddy ya ɗauki dubu sha biyar yace muyi siyayyar provision da su, mu uku fa, ko ni daya in dai komi enough ni ke so ya mun kadan".
Momi tace "na hane ki Auta da rainuwar duk abinda aka baki, idan ma cewa yayi ki tafi makarantar haka ai mahaifinku ne yana da iko daku. Bawan Allah nan fa danku yake nema".
Zainab tace "kiyi hakuri Momi na daina". Ta cire dubu biyar tace "zan je in kai ma Labiba da Habiba kuɗinsu". Momi ta ɗaga ma ta kai. Ta fita.
Fitar Zainab ke da wuya, hawaye suka zubo ma Momi, tana mai jin haushin halin mai gidan nasu, daga ya ajiye abinci shikenan ya gama komi sai dai suyi ma kansu.
Su fita waje ana masu kallon matan mai kuɗi, bayan basu san abinda su ke ciki ba.
Sashen Hajiya ta nufa, ta lek'a har ɗakin Hajiyar ta gaida ta, sannan tace "dama kuɗin siyayyar makaranta ce na amso mana gun Daddy ya bamu dubu sha biyar, na ciri dubu biyar ga na su Labiba nan".
Tsaki Hajiyar ta yi tace" ina mamakin son kai irin na Alhaji koda yaushe sai dai ya baki ki ba su ba dai su je ya basu da kan shi ba, na gaji da wannan cin kashin da ake man".
Karaf Labiba da ta shigo ta ce "kuma fa Hajiya sai kiga idan an tashi tafiya kayanta sun fi yawa, mu dai Daddy ya rika ba kowa na shi".
Zainab tace "Allah shi sauwake mun in cuci daya daga cikin ku, kuɗin da Daddy ya bada koni zan iya bada ukun su, ban dogara da kuɗin Daddy ba, DOGARO DA KAI shi ne abinda na yarda shi, idan yau Daddy ya daina bada kuɗin provision wannan ba damuwa ta bace, dan ku ni ke zuwa in kasa in tsare tunda abin wulakanci ne kowa ya je ya amso abin shi". Fuu ta fita bayan ta gama mai da ma su amsar da daga ta dace da su.
Hajiya tace "wannan Auta anyi tsageriyar yarinya sam bata da ta ido". Habiba dake tsaye bakin kofa tace "ni fa banga laifin ta, halin ta yamun kana ma ta zata maida maka daga nan kuma abin ya wuce sam bata da rik'o".
Labiba tayi tsaki bayan ta amshi kuɗin hannun Hajiya tace" Hajiya sai ki kara mana kin san dai ba isar mu zasu yi ba".
Hajiya ta ce "banda su ban ba wani ajiya ba, k'ila idan Habibu yayi niyya ya kara maku".
Habiba tace "kin manta cin mutuncin da kikai ma shi Hajiya wancan term ɗin, daga ya siyo mana cartoon biyu na short bread".
Hajiya tace "ai kin san Fatima sai tasa shi yayi".

chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now