BABI NA UKU

1.8K 145 5
                                    

Assalamu Alykum Wa Rahmatullah Wa Barakatuh. Am so sorry for the delay. Am fully back now In Shaa Allah. Vote and comment.
Love 😍 you loads 😘.

AUGUST, 2016

{3}
Misalin karfe sha daya na safe, Zainab na tattara kayanta da ta goge tana sakawa a wardrobe. Ta gama ta share ɗakin tsab, dan bata yarda mai aiki ta gyara ma ta ɗakinta da banɗaki ba. Haka in dai tana gida ita ke girki.
Sallama ta ji, ta amsa tace "oyoyo anti Jamila". Ta fito fuskar ta dauke da murmushi.
Wadda aka kira da anti Jamila tace "ai fushi ni ke da auta kamar mun maki laifi wannan hutun ko gidanmu baki taka ba".
Zainab tace "ai kya bari mu gaisa kafin ki mun korafin ki anti Jamila".
Tace "ba wata gaisuwa da zamu yi, Momi na zo gaidawa ba gun ki na zo ba".
Zainab tace "ɗaɗin abin dai ni ce mijin idan kika yi wasa yanzu in karo sabbi fil guda uku, harda kwarkwarori ma".
Murmushi tayi tace "ki karo gaba da haka ma idan ana yi, na san dai ni ce ta karfen".
Zainab tace "banga _my better half_ ba?", ta ce "yana wajen Abban shi na baro su part ɗin Dadi,Momi fa?".
Zainab tace "Momi taje wajen aiki amma yanzu zaki ga ta dawo da 12pm tayi".
Yaya Habib ne ya shigo rik'e da Sultan mai sunan mahaifin su (Ibrahim). Zainab ta gaida shi, yace "bafa zama zanyi ba, ku tashi mu je,Auta dauko mayafinki mu je kiyi siyayyar ki kafin a tafi masacallaci". Cikin ɗoki ta shige ɗaki ta dauko mayafi kalar ruwan ɗorawa (yellow), wanda ya shiga da doguwar rigar material dake jikinta mai adon bula,baki da yellow. Ta fesa turare ta fito, fuskarta fayau babu kwalliya. Wanda hakan al'adarta ce.
Anti Jamila ta kalle ta tace "Auta manya ko yar kwalliyar ta 'yan mata baki tsaya yi ba, kika sani ma in mun je mu sami wani banker ya lora". Yaya Habib ya harareta, Zainab na kallon su, tayi murmushi tace "kin dai san ni makeup ba damu na yayi ba, amma dai duk wanda ya san high Class ya dube ni ya san ina cikin top class ko yaya Habib?".
Yace "ina zan sani ni kuwa tunda kallon matan ni ke". Zainab da anti Jamila suka yi dariya.
A bakin katafaren super store din nan Jifatu Enterprises suka yi parking. Kowanne su ya fito, Zainab na dauke da Sultan a kafaɗarta suka shiga.
Cikin mintuna talatin suka gama siyayyar da zasu yi suka wuce wajen biyan kudi, Yaya Habib ya mik'a ATM card ɗin shi aka cire iya adadin kuɗin kayan da suka siya.
Gida ya maido su bayan Zainab ta zuba ma shi godiya da addu'o'in da ta saba. Suka shiga da kayan ya juya zuwa gida dan shirin zuwa masallaci.
Nan suka iske Momi ta dawo, tana kitchen ita da Asabe mai aikinsu. Momi ta fito suka zauna a falo, bayan anti Jamila ta gaida sirikar tata. Zainab ta nuna ma Momi kayan da Yaya Habib ya siya ma ta, Momi tasa albarka. Tace "sai ki ɗibar ma su Habiba dan kayan sun maki yawa".
Zainab tace "baki san mi fa Hajiya ta mun ba, ni ba wanda zan ɗibar ma komi". Momi tace "komi za su yi maki 'Yan uwanki ne da baki da kamar su, kar in sake jin haka. In ji kin sake ma wani rashin kunya". Zainab ta zumɓuri baki, ba dan taso ba ta raba kayan biyu taba Asabe ta kai ma su.
Ko da Asabe ta kai kayan, Habiba kadai ta nuna godiyar ta. Labiba tace "banza mara zuciya, mai shegen son abin duniya".
Habiba tace "ke ce k'atuwar banza wadda ba ta gode ma alkhairi, sai ki gaya mun idan kuɗin da Dadi ya ba mu zasu isa ayi wannan siyayyar, kuna raina alkhairi bayan iyalan Momi basu cancanci haka ba".
Bayan La'asar yaya Habib ya zo ya tafi da Anti Jamila. Zainab ta fita zuwa MAINASARA ta amso kuɗin cake din ta. Inda ta cire naira ɗari uku ta ba Auwal, ta ce "ga kuɗin ku nan, nagode sai kuma mun dawo". Auwal yace "toh Allah shi bada sa'a Zainab". Tace "Amin".

Ranar Asabar wajen misalin karfe 12pm na rana Zainab ta gama shirinta cikin housewears ɗin ta, masu gida-gida kalar pink. Anyi mata dinkin da yabi jikinta,rigar ta kai ma ta gwiwa,da dogon wando sai maroon ɗin dankwali da ke daure a kanta, bayanta goye da damdamemiyar school bag, ta janyo trolley bag din ta babba, Momi na janye da ta tsakiyar.
Momi tace "Auta a dai dage karatu kinga dai daga wannan term ɗin SS 3 zaku shiga bani son wasa da karatu".
Nan dai har suka fito, tasa kayanta a bot sannan suka wuce part ɗin Dadi. Nan ta iske su Labiba. Ta durkusa har kasa ta gaida shi, tace "Daddy zamu tafi school", yace "toh Allah shi bada sa'a a dage da karatu". Tace "In Shaa Allah".
Ya mik'a ma kowacce cikin su 1k. Labiba ta amsa tare da furta "gaskiya Daddy 1k ba zata ishe mu ba, ai abin kunya ne ma aga kamar mu da pocket money 1k".
Daddy yace "sai ki bani kuďina in baki so, dubu dayar ce nike da halin baku".
Zainab tace "an gode Daddy Allah shi kara budi na alkhairi". Yace "Amin, ungo dari dubu daya ku kara ke da Habiba".
Nan ya tashi ya shige ciki. Momi ta kara ma kowanne su 1k, dama Zainab yaya Habib ya bata dubu biyar ta haɗa da kuɗin provision da daddy ya basu dubu goma ta ba Momi ta ajiye ma ta sai ta dawo, kuɗin da ta amso na cake ne a hannun ta.
Sun isa bakin motar Momi ta kara jadadda ma su su dage da karatu. Zainab ta shige gidan gaba,Habiba da Labiba a baya. Danliti direbansu ya jasu cikin motar gidan kirar TOYOTA HIGHLANDER duk wanda ya gansu cikin motar ya san ya'yan wani kusa ne,takaicin Zainab kenan. Bayan a gida ba haka abin yake ba.
Ta kalli direba tace "Baba Danliti zamu biya gidan su Jidda". Yace "toh uwar dakina".
Sun dauko Jidda, daga nan suka mik'i hanya.
Cikin 1hr 45mins suka isa bakin gate din Federal Government Girls College, Bakori (FGGC). Dalibai ne jingim a bakin gate din suna mik'a teller ɗinsu na bank da suka biya kudin school fees kafin su shiga.

chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now