25

124 5 0
                                    

Zumuncin Zamani....

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

Daidai lokacin Saudat na tsakiyar gadonta tana kwararo Addu'oin samun zaman lafiya da rinjaye a kan mak'iya. A zuciyarta take Addu'oin yayin da kanta take sunk'ufe cikin laffayar da take jikinta.

Idanunta gaba d'aya a kumbure suke alamar ta ci kuka ta k'oshi. Hisham da sallamarsa cikin murna da farin ciki ya shiga d'akin Saudan, shi ka d'aine don bai amince da wani rakiyar abokai ba.

Tattausan k'amshin da aka gauraye d'akin da shi ya ziyarci hancinsa, bai san sanda ya lumshe ido ba, k'amshin ya bada ma'ana sosai musamman ya ha'du da k'amshin sabbin kaya da sanyin Air condition. Shi da kansa mamakin kansa yake ta yarda lokaci guda ya angwance da zaratan mata har guda biyu, ya zama dole ya yiwa Allah godiya don shi ka'daine zai masa hakan ba wayonsa ko dabararsa ba.

Kai tsaye ya hau tsakiyar gadon yana murmushi karo na farko ga Shi ga Saudat ba a matsayin muharramai ba, a'a a matsayin mata da miji yana da iko da komai na sassan jikinta zai yi yarda yaga dama da su sab'anin da da suke masa dangwaliliya. Sosai ya sa hannunsa ya janye lullub'in da ta yi wa fuskarta Saudat ta yi saurin runtse idanunta wata irin matsananciyar kunyarsa ce ta bijiro mata, ganinsa zaune daf da ita har yana gugar jikinta. Shi kuwa a razane yake kallonta ya yi saurin cewa "Subhanallah, Saudat me ya samu fuskarki haka? Kin ga k'asan idonki kuwa?" Ya fa'da yana kaiwa fatar idon shafa. Da sauri ta ture hannunsa tana sunkuyar da kanta. Murmushi ya saki ya ce "Gangan kenan, ai yanzu ba ni da shamaki da ko ina na jikinki." Ya sake jan mayafin da take k'ok'arin kare fuskarta da shi yana fa'din "Kada ki gaya min kuka ne dalilin wannan kumburin idon, kamar wacce za'a kai gidan mak'iyi ba masoyi ba." Hawayen ne suka sake wanke mata fuska, iyayenta da y'an uwanta su kawai take tunawa kukan ya zo mata, da wayonta bata tab'a zuwa wani wajen ta kwana ba Abba da UMMA basa barinta cewa suke ko wane gida tarbiyyarsu daban. Amma yau kacokam an 'dauketa an mata togaciya da ganin iyayenta. 

Hisham gaba 'daya ya janyo tattausan hannunta yana murzasu a hankali cikin wani salo tare da mamakin taushi da sulb'i hannun Saudan irin wanda ake kira kamar auduga. Cikin wata irin murya da ta nuna zallan halin da yake ciki ya ce "Saudat Ranar farin ciki ce, please kada ki b'ata mana ita. Kin san tsawon lokacin da na da'de ina jiran wannan ranar? Kullum imagining 'dinta nake a mafarki sai ga shi yau tazo idanu bu'de please wipe those tears away. Ban san ma me ya kawo wannan abin akan wannan kyakykyawar fuskar ba." Ya fa'da yana lakato hawayen da hannunsa yana musu kallon jin haushi "Wallahi maza ki tattara ki mayar da su anjima ka'dan zasu miki amfani amma yanzu kam bana buk'atarsu ki bari suna hurting heart  'dina." Ya fa'da yana lek'a fuskarta, yana dariya da y'ar wak'arsa, da ta dinga saka gaban Saudat dukan uku-uku. Ta san ma'anar maganarsa shi yasa tsoro da razani suka shigeta." Hannunta ya ja da nufin mik'ar da ita tsaye ya ce "Oya taso mu je, mu ga gidanmu muga k'ok'ari da bajintar da su Abba suka mana."  Cikin slow Saudat 'din ta mik'e lamarin da ya ki'dima Hisham har bai san sanda ya jata jikinsa ya rungume tsam ba yana fitar da wani irin numfashi. Sosai bugun zuciyarsa ya k'aru ya dinga fad'in "Alhamdulillah Ma sha Allah." A cikin kunnuwanta.

Saudat kuwa k'afafunta har rawa suke ta dinga jin wani yarrr a tsigar jikinta, ga wani fitsari da ta fara ji na ba gaira ba dalili. Dole ai karo na farko fa kenan a rayuwarta da ta fara jin kusantar 'da namiji kusa dai ita manne da jikinta. Yanayin da yake jin kansa shi kansa abin ya girmami tunaninsa ya rik'e ya gam a jikinsa tsawon lokaci kafin ya zareta daga jikin nasa idanunsa a lumshe ya jingina da bango yana maida numfashi. Ya da'de a haka kafin ya iya controlling kansa ya shige toilet. Sai sannan Saudat ta bu'de nata idon zuciyarta na buga mata da sauri ji take kamar ta fice da gudu ta bar 'd'akin sai dai ta san ba dama tunda ta karanta wannan shine auren.

Alwala ya 'dauro ya fito yana dubanta ya ce "Madam Alwudu." Da sauri ta fa'da toilet Hisham ya bita da kallo yana murmushi ya ce "Za ki yi mai dalilin."


Suna idar da Sallah da Addu'oin da suka dace da Alkur'ani da sunnah. Ya janyo masa ledojin da ya shigo musu da shi. Kaji ne gasassu sai fresh milk mai sanyin gaske ga dabino da Zuma a gefe. Sosai yake janta da hira don ya lura a takure take da shi, shi kuma so yake ta sake sosai kafin ya gabatar da k'udirinsa na gaba.

Saudat kuwa tana saka cinyar kaza a bakinta, mahaifanta suka fa'do mata. Tunaninta 'daya suna can ko me suka samu suka ci oho! Yanzu haka zata dawwama cikin daula nata iyayen na cikin wahala anya kuwa zata iya? Take ta ajiye naman saman ba zata iya ci ba, ta sani a gidansu sai su shekara ba su kaza ba, gwara naman miya suna iya ci sau 'daya a sati idan an samu sukuni.

Da mamaki Hisham yake kallonta kafin ya ce "Me yasa?" Cikin hawaye ta ce "Na k'oshi Yaya Hisham." Girgiza kai ya yi ya ce "Wasa kenan, me kika ci? Zauna na baki a baki, ba kyau kwana da yunwa balle ke da za ki amshi bak'uwar rayuwa yau, ai harkar ba zata tafi yarda ake so ba idan da yunwa a cikin nan." Ya mik'e yana cewa "Bari na baki waje ki ci sosai Zan je wajen Fareeda ban shiga ba nan na yiyo direct."

Tsaf ta 'dinke fuskarta sai yanzu ta tuna da wata aba Fareeda, da shauk'i Ya 'debeta ta manta da ita. Da sauri ta mik'e ta haye gadonta ta kwanta flat a mimmik'e. Hisham gaba 'daya ya ji yawun bakinsa yana shirin k'afewa ganin diri iya diri bai San sanda magana'disu Ya ja shi Ya bita gadon ba a wani gaggauce......... tun daga wajen labari Ya canja ya manta da zuwa wajen Fareeda yana amsar wata iriyar Sabuwar rayuwa a wajen Saudat da ba zai iya kwatanta ta da komai ba, abu 'daya yake jaddadawa kansa da Ya San haka auren yake da bai Bari Ya kai wannan shekarun ba bai yi aure ba.

Ba su sake sanin inda kansu yake ba sai daf da asubahi Sallah kawai su kayi suka sake komawa barci.


*********_____________********

Bugun k'ofar da ake ne Ya farkar da Hisham daga nauyayyan barcin da yake. Ya 'dan saki tsaki ka'dan ha'de da lallab'a wa ya janye Saudat daga jikinsa, daga yanayin da take barcin Ya san barcin wahala take, don ma ta yi jarumtaka amma fa kowa na gidansu ya sha kira. Rigarsa ya zura ya fita da sauri don yana da tabbacin Fareedah ce. Idanunsa a kan agogon Falon da yaga 11:00 daidai na rana.

Yana bu'dewa kuwa ya ga Fareeda ce a tsaye cikin 'daure fuska ta kuma rik'e k'ugu masifa ce kwance a cikin idanunta, sam bai hango sassauci ba. Murmushi ya 'dan sakar mata don ya san tarin laifukansa masu girma ne. Ya 'dan dunk'ule hannayensa ya kai mata jijina "Am sorry Reeda yanzu nake shirin zuwa wajenki." Ta dinga masa wani irin duba kafin ta yi k'wafa tana k'ok'arin mayar da k'wallar da take shirin zubo mata, bata son nuna masa gazawarta. Murya a tunzire ta ce "Ka ji da shi, magulmaci ka gama ha'intar tawa ka 'dau kwana ka bawa wata kucaka, to wallahil azeem ban yafe ba kuma sai na kai k'ararka gidanku. Saboda kowa ya san nice uwargida amma don munafunci......."
Cikin zafin rai ya ce "look Fareeda, ni fa ba shashashan namiji bane da zan zauna Kina gaya min maganar da kika
Ga dama, watch your tongue before ki fa'da min son ranki, ya isheki daga aure jiya yau ki tsaya gabana kina gaya min magana gatsal. Ba zan d'au raini ba I warned you for the last time kada ki sake furta min kalmar munafuki, ko ki kirata kucaka idan ba haka ba kuma tabbas zaki girbi abinda kika shuka. Daga haka ya mayar da k'ofar ya rufe da k'arfin gaske ya barta a tsaye tana masa kallon mamaki, ita ba irin zaman da ta so yi a gidan miji ba kenan so ta yi ta zauna ta dinga sarrafashi kamar control kuma haka Mommynta ta ce mata. Tunda ubanta yana da ku'di to duk mijin da ta aura zai ji shakkar wulak'antata. Da gudu ta koma d'akinta, dole ta kira Mommy su yi sharing wannan takaicin tare. 

Ai kuwa tana sanar mata Mommyn ta dinga shak'ar wani irin numfashi tana fesarwa, a zafafe ta furta "Kan uban can, shi Hisham 'din ne ya miki wannan wulak'ancin? Ki bar ni da shi kwantar da hankalinki daughter wallahi akan iyayensa Zan huce kuma sai na nuna masa ke jininace kuma jinin Sa'a ba abin wulak'antawa bane. Sai na mayar da shi abin kwatance sai ya zama mijin kan tace ma ba mijin ta ce ba. Sai ya zama abin nuni a wajen jama'a don sai kin juya shi juyin da ko uwarsa sai kin so ta ganshi zai yarda ta gan shi. Yanzu ki kira Uwarsa ki gaya mata. Matsiyacin yaro ni zai ba'dawa k'asa a ido, to ko Hamza ubansa ai ya yi ka'dan balle shi." Daga haka ta kashe wayar a fusace tana tsaki.


Jikar Nashe ce! ❤️❤️✍🏽

Zumuncin ZamaniTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon