10

135 10 0
                                    

Zumuncin Zamani.
Na

Nazeefah Sabo Nashe.

(Typing Fad'ima Sabi'u D'ankaka. Ku mata Addu'a Allah Ubangiji ya kawo k'annen Meenah, ya albarkaci zamanta da mijinta da zuri'a d'ayyiba. Nagode.)

Lokacin da Hisham ya bar gidan su saudat,kifa kansa kawai ya yi a kan sitiyari. Zuciyar sa na kuna shi kadai ya san yadda yake jin sauda a ransa. Wani irin zaxxafan so yake mata Mai wuyar kwatantuwa, amma kuma ya rasa ta yarda xai bullowa iyayensa da suke ta Shirin bikinsa da diyar senator mai k'ok'arin tsayawa takarar shugaban kasa( president) a Zab'e mai zuwa.
Shi kansa ya san iyayensa mutane ne masu d'aukaka darajar kud'i fiye da zumunci, musamman mahaifinasa da yake wa kud'i son da bai had'a shi da komai a duniya ba, tabbas ya rasa mafita. Ina ma Abban Sauda zai amince ya aura  masa Sauda da amincewar iyayensa ko babu.
 

A harabar gidan ya ajiye motarsa gurin makeken filin da aka tanada don ajiye motoci. Barorin gidan suna ta kawo gaisuwa da yake kwana biyu ba ya gari, d'aga musu hannu kawai yake..
Ya isa falon mahaifiyarsa, ransa ne ya b'aci ganin fareeda a gefen mahaifiyarsa. Ya sani ba zai wuce ta kawo k'arar sa ba, don shi ya mance ma rabon da ya ziyarce ta, ya san ta wargaza masa shiri.
Da sallama ya nutsa kansa cikin falon, mahaifiyarsa ta jefe shi da wani mugun kallo kafin ta ce "Sannu da zuwa ishasshe d'an kansa".
Ya zauna sosaii yana d'an sakin fara'ar dole. yace  "Mommy me ya faru kuma?"
Ta girgixa kai had'e da cewa, "Dama Allah _Allah nake ka zo in ji dalilinka na rashin zuwa wajen Fareeda tsawon lokaci, ka san sarai an fara shirin bikinku da za a gabatar nan da wata uku,amma ka d'auke k'afarka Sam ka daina zuwa, kuma ta yi waya baka amsawa sai ka ga dama, alhalin kai ba kiran ta kake yi ba."
Ya juya ya d'an saci kallon fareeda, kafin yace "Mummy hak'uri za ta yi da ni, kin san harkar business ta yimin yawa, ba na samun kaina sai tsakiyar dare shi ya sa ko an yi auren gaskiya sai ta yi hakuri da ni."
Sai sannan mummy ta ji dadi, ta kuma dafa kafad'ar Fareedan had'e  da cewa "Kin yarda da abinda na gaya miki ko? Abinda na fad'a exactly shi ya fad'a. Don  haka kada ki damu idan akai yi auren ke da kanki za ki canza abinki."
Murmushi kawaii fareeda ta saki, don ta san Hisham sharo ta kawai ya yi."
Mummy ta mik'e hade da cewa, "Bari na ba ku guri, kai Hisham sai ka sake lallashin ta, ga juice nan ka ba ta don tun d'azu da ta zo ba ta ci komai ba, ka lallashe ta ka ji na gaya maka."
"To"  kawai ya ce da mummy, ya fara daddana wayarsa, tsawon mintuna biyar da fitar mummy bai d'ago ya kalli inda take ba, ita kuma ba ta yi masa magana ba, don yadda yake jin kansa ita ma haka take jin daidai da shi ce ita.
Sai can ya d'ago ya dube ta a shagub'e ya ce "Fareeda ya gida?"
Ajiyar zuciya ta saki tace, "Lafiya lau Hisham"
Ya girgiza kai "kin kyauta, wato tun kafin a yi auren har kin fara kawo k'ara ta gidanmu ba za ki iya juriya ba ashe idan akai auren?"
Fareeda ta girgixa kai had'e da cewa, "Hisham kenan, kana zaton kana kyautawa abin da kake min.? kada ka manta fa ma'aurata za mu zama, Amman a ce ba ka da lokacina."
Cigaba ya yi da danna wayarsa, sai can ya d'ago kai  ya ce "shi yasa na ce miki ba za ki iya jurewa ba, tun kafin a yi ki zo kina complain gwara ki hakura don bana son k'ananan maganganu, Ni business man ne, don haka ba ni da wani isasshen lokaci nawa idan kin ga ba za ki iya ba ki sake jaddada shawara da zuciyarki"

Daga haka sai ya fice ya bar fareeda da sakakken baki tana bin shi da kallon mamaki, wai ita da maza suke rububin son ita ce yau namiji yake gwara kanta don kawai ta zub da ajinta ta nuna masa so.
Tun ganin farko da ta yi masa ta k'allafa wa ranta soyayyarsa, hawaye ya kwaranyo a fuskarta, banda tsananin son da take yi masa yau kam da ta hak'ura da shi ko shine autan maza.
Bata jira fitowar mummy ba ta mik'e tai ficewarta, ko da ta fita ba ta ga motarsa ba, ita ma rantsattiyar motarta ta hau ta yi tafiyar ta. Zuciyarta a matuk'ar zafafe.

Yau gidansu sauda da mugun tashin hankali suka tashi sakamakon sallama da aka yi da mahaifinsu da asuba, sai gani suka yi ya dawo yana Jan tasbihi ga sarki Allah.
Ummansu ta tare shi had'e da cewa, "Lafiya Abban Sauda? wani ne ya rasu?"
Sam babu alamar damuwa a ransa ya ce, "Taso yaran nan yau iKon ubangiji ya sake sauka a kanmu shagona ne ya k'one k'urmus an ce har Yanzu an kasa kashe wutar."
Umman Sauda a gigice tace "Innalillahi wainnah ilairrajiuna"
Sauda kuwa da take tsaye da buta a hannu sakar butar ta yi hade  da cewa "Wayyo Allah, mun shiga uku!!!"
Abba ya zabga mata harara yace "Sauda, wannan wane irin shirmen banza ne? mun shiga uku a ina? Kada Allah ya sa mu shiga uku. Idan masifa ta faru innalillah ake ja ko ba ki karanta alkur,ani ba ne? bana son shashanci maza ki kira yayyen ki."
Jikinta a salub'e ta Isa zauren gidan ta k'wala musu kira ta dinga yi, gaba d'aya suka fito suna fad'in, "Lafiya?"

Hawaye ne kawai yake fita daga idonta, don kam babu bakin magana. Ganin haka yasa suka wuce zuwa cikin gidan cikin tashin hankali. Y. Saeed ne ya fara cewa "Umma lafiya?"
Abbansu ne yaja ajiyar zuciya don umma babu bakin magana.yace "Bakomai yau kudurar ubangiji ce ta sauka a kanmu, sai dai fatan ubangiji ya bamu iKon amsar jarrabawar daidai. shagonamu ne ya k'one k'urmus."

Jikar Nashe ce!

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now