26

189 7 0
                                    

Zumuncin Zamani

Na

Nazeefah Sabo Nashe

08033748387.

Tana kashe wayar da suka gama yi da Mommyn ta dannawa Mommynsu Hisham waya. Ta ci sa'a lokacin suna tare da Alhaji Hamza suna hirar yarda bikin ya kasance. Da yarda abubuwa suka tafi musu yarda suke so Hisham ya auri d'iyar manya.  Ta ji wayarta na k'ara da sauri ta 'daga ganin Fareedah ce tana fa'din y'ar nema yanzu haka angon nata ya amsheta a matsayin aure yau, tafiya gashi da ruwan 'dumi ya kamani. Ko amsa sallamarta Fareedah ba ta yi ba ta shiga rattabo mata k'orafi sab'anin nata hasashen. "Kin ga 'Dan iskan 'danku abinda ya yi min ko? Yana can wajen waccan y'ar matsiyatan ya kai mata kwanana da alama kuma ya gama mata aiki, to bari ki ji tunda na lura kuma ba jin maganar Ku yake ba yanzu zan bar masa gidansa, Allah yaso ni bai kwashe min ni'ima ta ba."

Cikin salati Mommyn ta ce "A'a Fareeda saurareni ba za'ayi haka ba yanzu zan zo gidan na ji dalilinsa na aikata haka. Ba ke zaki bar gidan ba ita y'ar matsiyatan dai ita zata bar gidan tunda dama ni zaiciyata ba wai tana son zamanta a gidan bane, amma ina tabbatar miki bai kusanceta ba don Malamina ya sanar da ni ba zai kusanceta ba, idan ya kusanceta ai muna cikin masifa don tsiya zai jajib'o mana." Cikin b'acin rai Fareeda ta kashe wayar bayan ya zabga tsaki.
Alhaji Hamza da yake zaune gabansa ya fara lugude jin ana maganar rabuwa. Da sauri ya ce mata "Wai me ya faru ne na ga kina ta masifa ke ka'dai." Tsakin itama ta yi kafin ta ce "Bar ni Alhaji in ji da bala'in da wannan yaron yake son jefa mu wai can 'dakin y'ar gidan Mustafa ya kwana, ai kawai tashi zaka yi mu je gidan a yi wacce za'a yi ni addu'a ta ma Allah yasa bai kusanceta ba ya haifa mana irin tsiya. Mu je ka saka ya saketa kawai ina dalili? Sai ka ga uwar dukiyar da ya narka musu don dai na san Mustafa ba shi da wannan arzikin da zai narka mata wannan dukiyar. Ka je ka saka ya saketa tun kafin nan gaba su gama da shi ka manta shi kansa Mustafan da ya auri uwarta Daga haka aka fara, ya zo ya gagari kowa baya jin maganar kowa a dangi. Yanzu fa ita Fareeda fa'di take ita zata bar gidan zancen da ba zai yiwu ba kenan sai dai ita y'ar gidan Mustafa ta bar gidan a yau ba sai gobe ba." "Dole kuwa, jazaman tunda ba ubanta bane ya haifa min 'dan." Alhaji Hamzan ya fa'da yana mai tabbatarwa. "A yau zan masa mai k'ank'at zab'i zan ba shi ko ni ko yarinyar can na gaji da wannan maganar." Cikin farin ciki Hajiya Laraba ta ce "Abinda za ka yi kenan wallahi, haba ina dalili?" Hijab kawai ta zura ta mik'e suka fice daga gidan a hassale.

Wani irin gigitaccen bugun k'ofa ne ya farkar da su daga nauyayyan barcin da ya sake 'dibansu. Gaba 'daya suka farka a gigice jin kamar ana shirin b'alle k'ofar sashen Saudat 'din.

Hisham ya 'dan janyeta daga jikinsa yana mata kallon tausayi jin zazzafan zazzab'in da ya gauraye ilahirin jikinta. "Koma ki kwanta ina zuwa."

Ita kuwa haka kawai ta ji gabanta yana fa'duwa ta 'dan runtse idanunta tana jin yarda jikinta yake sake amsawa a duk yayin da ta motsa, wani irin zubi da ra'dad'i take ji a k'asanta.  Hisham ya zura jallabiyarsa ya fice da sauri, yana fa'din "Wanene? Haba muna zuwa." Duk a tunaninsa Fareeda ce ta sake dawowa. Yana bu'de babbar k'ofar da zata sadaka da falon ya ci karo da mummunan kallon da mahaifinsa yake watso masa. Mommy kuwa da ya kalli fuskar ta ba zai so ya sake kalla ba saboda ba wani farin ciki a tare da ita sai huci take kawai. Tana jan numfashi tana fesarwa. Bangajeshi ta yi ha'de da cewa "Matsa mu wuce mara mutunci kawai." A firgice Hisham ya ce "Lafiya Daddy?" A tsawace ya ce masa "Lafiyar kenan don ubanka. Ina ita mai k'ashin tsiyar da ka ajiye a ciki? Wuce ka kirata a yi komai a gabanta." Hisham kansa ya sunkuyar ya ce "Mhmn Daddy ba sai an kirata ba, bata da lafiya wallahi." Cikin firgici Mommy ta ce "Shikkenan mai afkuwa ta afku, ya gauraya jininsa da na masu Dattin hula wallahi Hisham ka cucemu kuma ba mu yafe maka ba." Cikin b'acin rai Alh. Hamza ya ce "K'yaleshi Laraba, ai wallahi ko cikin ya shiga sai ya fita ta dole ka wuce ka taso ta na ce." Zuwa lokacin Hisham ya kai matuk'ar b'acin rai kuma a yau ya sake tabbatarwa iyayen nasa akwai rashin ilimin islama a tare da su. Ransa a b'ace ya wuce su ya haye wani k'aramin step ya bi corridorn da zai sadashi da 'dakunan barcinsu, zuciyarsa na wani irin tafarfasa. Bai k'arasa 'dakin ba ya ganta ta janyo jiki ta fito sanye da hijabi har k'asa. Da sauri ya kama hannayenta jikinsa na rawa idanunsa jajir kamar me shirin zubar da hawaye ya ce "Wallahi Sauda ban yi dace da iyaye na gari b......." Da sauri ta saka hannu ta toshe masa bakinsa tana girgiza masa kai. Bata buk'atar k'arin bayani ta ji komai duk wani zagi da cin mutuncin da suka yiwa iyayenta ta jisu a kunnenta. Ta ce "Mu je kawai Y. Hisham su aikata duka abinda suke so, kada kuma ka sake cewa ba Kayi dace da iyayeba ba kyau." 

Suna zuwa Alhaji Hamza ya dinga jifanta da kallo na tsana kamar ba jininsa ba, ji yake kamar ya shak'eta ta mutu ya huta da ganinta. Ya dubi Hisham ba tare da ya amsa gaisuwar da Sauda take musu ba a durk'ushe kanta a k'asa ya ce "Tsakanin ni da Mustafa Hisham waye ubanka? Waye ya yi 'dawainiya da kai daga gaiguwarka har yanzu?" Hisham kansa a k'asa ya ce "Kai ne." Alh. Hamza ya saki murmushi mai nuni da zallar takaici ya ce "Idan ka amince da hakan har zuciyarka a yanzu ba sai anjima ba nake son ka saki yarinyar nan. Na haramta auren da yake tsakaninku har abada." Wata irin fargaba ce ta riski Hisham gumi ya dinga tsatstsafo masa ya dinga wa mahaifinsa wani irin kallo kamar zuciyarsa zata buga cikin k'araji ya ce "Haba Daddy why? Me ya yi zafi haka?" Cikin masifa Daddyn ya ce "Ubanka ne ya yi zafi Hisham zaka aikata abinda nace maka ko a'a? Umarni fa na baka dolenka ka bi ko billahil azeem na tsine maka, na gaji da magana 'd'aya na gani da maganar Ahalin Mustafa shi kansa ban 'daukeshi komai ba balle ahalinsa." Daga shi har Sauda zuk'atansu suka dinga bugawa ba k'ak'kautawa, ji suke duniyar kawai na katantawa da su musamman Sauda ta dinga kallon Hisham tana son ta ji hukuncin da zai yanke. Hisham harshensa ya yi nauyi "Innalillahi kawai yake ja ar ransa.

Tsawar da Alh. Hamza ya daka masa ita ta farkar da shi daga zuzzurfan tunanin da ya tafi ba ya raba 'daya biyu suman wuncin gadi ya yi. "Kai nake sauraro zaka aiwatr da k'udirina ne ko sai na tsine maka?"

Hisham ya dinga goge zufar da take karyo masa kafin ya kalli Daddynsa cikin wani irin yanayi ya ce "Please Daddy don't do this to me.... Wallahi ba zan iya ba zuciyata zata iya bugawa..." "shine ya fi min sauk'i gwara ka mutu akan na dinga kallon wannan yarinyar a matsayin matarka. Wallahi mintuna uku na baka ka aikata abinda na ce ko kuma tsinuwa ta tabbata a kanka." Zuwa lokacin ya tabbatar da gaske mahaifinsa ya ke don haka jikinsa a sanyaye ya mik'e ya wuce cikin d'aki.

Tsawon mintuna biyu ya fito jikinsa a sanyaye, hannunsa 'd'auke da farar takarda ya isa gurin Sauda yana rintse ido ya mik'a mata takardar hannayensu dukkansu rawa suke sosai kamar masu kakkarwa.......

(A yi hak'uri yau typing ka'dan Mufeedah ce ba lafiya. Ku saka min ita a addu'oinku da bakunanku masu albarka. Nagode Jikar Nashe Ta ku ce.)

😊😊🙏❤️

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now