27

120 8 0
                                    

Zumuncin Zamani

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

______________

Sauda ta runtse idanunta ta bu'de tana sakin wani malalacin murmushi ta damk'i takardar a hannunta, idanunta cikin na sa kafin ta sauke ganinta akan Alh. Hamza wani k'arfin hali yazo mata ta ce "Tabbas a yau na shaida na kuma tabbatar da cewa Naira ta fi zumunci. Amma ina so ka sani wannan abin da ka yi Annabi S.a.w yana tir da kasancewarka musulmi a yau saboda yana fushi da duk wanda baya zumunci....."

"Ke saurara!" Alh. Hamzan ya daka mata tsawa "Ina fata ba wa'azi za ki min ba? Don ko ubanki bai isa ya dubi tsabar idona ya ce zai min wa'azi ba, aikin gama ya gama burina ya cika sai ki dangana ga gidan ubanki ba gidan Hisham ba..." cikin tafarfasar zuciya ta bi shi da wani irin kallo na tsabar raini kafin ta ce "Ai d'anka ko da gold aka sassak'ashi na bar shi kenan."
Ya kai hannu zai tsinka mata mari Hajiya Laraba ta yi saurin tare shi tana fad'in "K'yaleta Alhaji zafin samu da rashi ne ya dabaibaye zuciyarta an kwanta cikin a.c ga luntsimemiyar katifa dole bak'in ciki ya kusa kasheta zata koma gidan gado da ko wuta babu ta arziki. A yi gaba Hisham dai ya rabu da gayyar tsiya arna a idi..." zuwa lokacin zuciyar Saudat ta kai k'ololuwar b'aci ta dinga ha'diyar zuciya idanunta cikin na Hajiya Laraba ta ce "Zan tafi kuma na ji da'di da  ban yi dogon zama a gidan nan ba, gidan da babu tarbiyya sai son zuciya." Daga haka ta mik'e ta fice daga gidan da sauri ko 'dakinta bata koma ba burinta ta dangana ga iyayenta, gaba 'daya Hisham da aurensa sun fita daga ranta.

Tafiya kawai take ba tare da ta san inda take jefa k'afarta ba, ga wani irin ra'da'di da take ji daga k'asanta. Rashin ku'di a jikinta yasa ta dinga jefa k'afarta ta k'udiri niyyar ko da k'afa sai ta je gidansu. Babu ko 'digon hawaye a tare da ita.

Sai da ta isa k'ofar gidansu sannan ta ji wani irin kuka ya taso mata. Iyayenta kawai take tausayawa suna murna sun aurar da ita a cikin kwana 'd'aya ta dawo musu matsayin bazawara bata san wani irin bak'in ciki za su ji a zuciyarsu ba. Duk kuma wannan abin an mata shine a sanadiyyar talauci, da ita 'din y'ar wani mai ku'di ce a cikin danginsu da ba a
Mata haka ba, da kowa haba-haba zai dinga yi da ita a dangi, kowa kuma burin ha'da iri zai yi da ita amma dubi yanzu yarda ake gudunsu kamar Mujiya, kai duniya ina zaki da mu? Ta runtse idanunta tana jin saukar wasu irin hawaye masu zafi da k'unan zuciya suna zubo mata ji yake ina ma Allah ya 'dauki ranta ta huta da ganin wannan abin takaicin.

A hankali tura zauren gidan nasu da aka sakaya, Yayanta yana kwance yana shan hantsi. Da sauri ya mik'e cikin fargaba yana mata kallon mamaki. "Ke Sauda lafiya haka da tsakar rana?" Bata amsa masa ba illa saka kai da ta yi da sauri ta shige gidan, shi 'din ma bai yi k'asa a gwiwa ba ya mara mata baya yana sake fa'din "Ba ki ji ina miki magana bane? Wani irin shashashanci ne wannan wa ya gaya miki yaran yanzu suna gudun gidan miji ko ma wace irin sabuwar rayuwa kika gani? Ai haka za ki hak'ura da haka
Kowa ya saba." Umman da ta dinga jin maganar daga sama da sauri ta fito jikinta itama har b'ari yake ta tsaya tana duban Sauda baki a hangame, "Subhanallahi Ke Sauda Lafiya? Yau na ga shashashar yarinya gudun aure kuma?"

Sauda ta jingina da jikin bango kafin ta zame ta yi zaman y'an bori a k'asa ta kuma daddage ta kurma ihu. Umma ta yi saurin toshe mata baki "Dakata kada ki tara mata jama'a abinda kika gani ai shine auren, ko don baki da y'an uwa mata ba ki san gundarin abinda aure yake nufi ba." Sauda ta 'dan zame jikin Umman ta kwanta tana mai da numfashi tausayin Ummanta ya kamata wato ita hasashen da take daban.

Abba ya fito daga 'daki ransa a b'ace ya ce "Ai laifinki ne me yasa tun kafin a kaita baki bayyana mata menene auren ba? Ke saudat bana son shashanci mik'e zaune ina mijin naki?" Idanunta a runtse ta ciji leb'enta ta ce "YA SAKE NI" gaba 'daya lokaci guda suka ware ido ha'de da cewa "Ya sake ki?" Saudan ta sake runtse ido tana jijjiga kai ta ce "Eeh ya sakeni bisa tilastawar iyayensa." Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna kawai suke ja kafin Abban ya nemi waje ya zauna Umma kuwa gaba 'daya k'afafunta sun kasa 'daukarta nema take ta zube a k'asa da kyar ta dafa bango ta zauna tana jin yarda gumi yake tsiyaya daga jikinsa duk da garin da 'dan sanyi.

Zumuncin ZamaniDonde viven las historias. Descúbrelo ahora