4

160 10 0
                                    

Zumuncin Zamani

Na Nazeefah Nashe

08033748387

Page 4

Adaidai lokacin umma tayi sallama, ta shigo tadawo daga unguwar. ji na yi tana "wannan kayan fa daga ina?" Na fito daga d'akin  ina bin umma da kallo.Ita ma ni din take kallo, tana jiran karin bayani. "Ba tambayar ki nake ba?"Na d'an tab'e  baki na ce "wannan mutumin ne da yake zuwa ya kawo.Ta sake bina da kallo, "Waye wannan mutumin?" 'Dan jim na yi ina tunani,sannan na ce,"Mtsw Hisham ko hashim?"Umma ta girgixa kai had'e  da murmushi ta ce "Saudat kenan hashim din ne kike kokwanton sunan sa? Yaro d'an albarka kenan, wannan yaro sam bai yi halin uwarsa da ubansa ba Wannan kayan haka jimgim? Allah ya yi masa albarka"
Tsit nayi mata ta dube ni,kafin tace "Yana ganki wani sukuku dake?"
Na gyara tsayuwar kafin nace" "Bakomai"
Ita din ma tabe baki tayi tace,"Allah ya kyauta ta shige dakinta."
Koda malam din yadawo ta nuna masa kayan,murmushi yayi yace"Allah kenan mai fitar da rayayye daga cikin matacce, shi kuma Hisham sam baiyi halin iyayensa ba.to Allah ya saka masa da alkairi,yakuma sa shine silar shiryiwar iyayensa"umma "Amin _Amin"kawai take fada
Xuwa can abba yace gobe ma ku shirya ke da sauda kuje gidan yaya falmata ku dubata,an ce tayi fama da jinya duk  da dai ni ma ban sami kallon arxiki ba. Amma ya wajaba ka sauke hakkin musulunci a kanka".
Umma tace,"haka ne kam"
Ina daga cikin daki ji na yi kamar na xunduma ihu,gidan inna falmata? Na shiga uku! matar da ta tsane mu muguwar tsana,ba ta mana kallan arziki, ita ce za mu je gidanta? Gaskiya gwanda na kwanta ciwon karya akan naje gdn inna Falmata.

Tun dare na fara nuku - nuku na cutar karya. Umma na hankalce da ni ba tace dani ''kala ba.
Koda safe kallo na kawai ta yi ina daga kwance tace," baki tashi bane?ko ciwo ne?"
Na daga kaina.
Fita tayi daga dakin zuwa mintuna ta dawo da cup din ruwa da paracetamol a hannunta ,ta miko min." Tashi ki sha maxa ki shirya mu je dubo Innarki."
Na langwabe murya na ce ."Umma ba zan iya xuwa ba
Dariya ta yi ta ce" Ai kuwan xuwa ya xama dole yarinya,ina kula fa da take - takenki tun jiya da Abbanki ya yi maganar xuwa gidan Innarki kika langwabe ki ka fara cutar k'arya. To duk wani lagonki na gane sarai kuma xuwa dubiya ko da jan ciki sai kinje."
Ai ban san lokacin da na d'ora hannu a ka na runtuma ihu ba. Umma kuwa ta doke bakina ta ce "Wallahi,kina tara min mutane ranki xaiyi mashahurin b'aci."
Don dole na ja baki na yi tsit.Sai hawayen bakin ciki da yake malale akan k'uncina.
Ban wani shirya ba da kayan jikina na mike na xura xumbulelen hijabi, da sauri na fita Jin umma na zabga min kira. A tsaye take fuskarta a hade ta nuna min hanyar zaure, na zira takalmina na ja k'afata muka fara tafiya
Ko a mota ban yi wa kowa magana ba, har muka Isa kofar makeken gidan mai kama da gari guda.k'ayatuwarsa ma fad'a b'ata baki ne. Mai adaidaita sahu yayi parking, umma ta fito ta biya shi kud'insa,sannan muka nufi kofar shiga gidan.
Sojan da yake gidan ya dube mu sama da kasa ya watsar, to ba dole ba ya gan mu a adaidaita sahu ba a irin manyan motocin da suka saba shiga gidan ba.
"Malamai daga ina? ba fa yau bane Alhaji yake raba sadakar,sai ranar jumaa,
Fuskata na hade ita kuwa umma murmushi tayi ta ce "Bawan Allah matar gidan mukaxo dubawa"
Ya sake kallon ta a wulakance yace " matar gidan wacce daga cikin"?
Da sauri umma tace , " hajiya falmata. Ni matar kaninta ce."
Ba tare da ya yi magana ba ya wangale kofar, yana fadin "Haba malama ki ce dai kawai kin zo maula amma ta ina kika yi kama da matar k'anin Hajiya k'annen Hajiya fa duk na sansu
kuma ba talaka a cikinsu, Matansu kuwa a galla -galla motoci suke zuwa"
Umma tace"Haka ne, mun gode da alfarmar shiga da aka bar mu mukayi "
Hakimar a hakince a falo muka sameta. Tana kishingide tana danna remote ga masu yi mata hidima nan sun kewaye ta suna mata tausa. Wasu kuma suna yanka mata kayan marmari tana sanyawa abaki tana taunawa cike da nishadi tana lumshe Ido.

Ko sallamar da mukai ba ita ta amsa ba sai daya daga cikin barorintace ta amsa mana. Umma ta samu gefe ta durkusa ta gaisheta ta,da kyar take amsawa.ni kuwa daga tsaye fuskata a matukar had'e
Hajiyan bude baki tayi tana min kallon mamaki."ke tsagera wani irin iskanci ne yasa ki ka yi kikam ba kya gaisuwa?"
Fuskata a hade na russuna na gaidata.
Ba ta amsa ba sai sake tunxura datayi tana zabga masifa."ke wallahi ki kiyayeni,don ana yawan fadar rashin tarbiyyar ki, To ni ba zan d'auka ba. Uban waye yace kixo gidana? Me zuwan na ku zai k'areni da shi?ban da ya rageni? Don ko ba komai idan za ku tafi tilas na ba ku kudin mota, don nasan k'ila bashi ma kuka ci kuka taho shegiya ke ba y'ar kowa ba sai fadin ran tsiya. To ki kiyayeni ehe don ni ba kanwar lasa bace kin yi  na farko kuma wannan ya zama na karshe" Umma ce ta shiga bata hakuri, ta mik'e tana fadin kin bata hak'uri ko sai nayi kasa-kasa  da ke?"
Murya shake  na ce ."Allah yabaki hakuri"
Bata amsa ba ta shige daki tana cewa masu aikin ta "ke kawo musu pure water,ki kuma basu #500 idan xasu tafi"
Mai aikin ta ce "To"
Zata mik'e umma tace."Yarinya barshi kinji tafiya ma za mu yi kuma wallahi muna da kudin mota mungode Allah ya saka da alkhairi."
Mai aikin ta tab'a baki ta ce "kun yi wa kanku."

Cikin jan k'afa ni da Umma muka fice daga gidan, muna barin gate d'in gidan umma ta dubeni cike da masifa ta ce "To ishasshiya mai bak'ar zuciya ,saiki tafi naki wuri do ni ba zan jera dake ba don kece uwar yanzu, Ni na zama y'ar tunda ke ba za'a  fad'a  miki ki ji ba.Kuma wallahi sai nasa yayanki ya yi miki dukan tsiya shashashar banza da wofi kawai.

Kuka na saka  ina ba ta hakuri don na san dukan yayyanmu ba bu sauk'i, amma umma tayi burus dani haka muka dinga shan tafiya a k'asa don sam layin babu ko adaidaita sahu, kasancewar layin shahararrun masu kud'ine.
Wata bakar motace ta dinga reverse (baya) tana yi mana horn alama anaso mu tsaya, Amma babu wanda ya tsaya a cikinmu ganin haka mai motar ya yi parking ya fito k'amshin turarensa shi ya sanar da ni shine. Ai kuwan ina juyawa nayi arba da shi.
Cikin sakin fuska umma take amsa gaisuwar da ya russuna yake mata.  Ni kuwa da yake ina son mu shirya da umma da Dan hanzarina na ce "Ya Hisham ina wuni?"
Ya juyo yana min kallon mamaki, bai ce komai ba baya ga amsa gaisuwata da ya yi a can k'asan makoshinsa ya mayar da hankalinsa akan umma." Umma daga unguwa kuke ne?"
Umma ta daga kai tace"Wallahi daga gidan innarku falmata muke,munje duba ta an ce ta Dan kwanta cuta kwanaki."
Hisham ya gyada Kai hade da fadin,"Exactly " nima chan xanje amma umma kun wahalar da kanku don nan unguwar ba a samun mota sai dai private car da kin sani kin gayamin sainaxo na kai ku."
Umma tace"Hisham kenan menene abin wahalar dakai a sadar da zumunci?,banda samun dinbin lada"Hisham ya gyad'a kai yace haka ne umma ga mutum mai hasashe da tsinkayen tunani mai kyau irin na ki kenan,ammn don Allah ki yi min uxuri na fara biyawa na duba inna falmata"
Umma tace"bakomai Hisham daka bar mu mun karasa kada mu dora maka wahalar"
Hisham din da sauri ya ce,"Haba, umma daina fadar hka wace wahala ce a aikin iyaye banda d'imbun samun lada?"
Ni dai ina tsaye a gefe tamkar an dasani a wurin.Hisham ya budewa umma mota gidan baya yana cewa "Bismillah umma tashiga motar, sannan ya juya ya dubeni "Malama shiga mu tafi" ya bude min gidan gaba.
Fuskata ba yabo ba fallasa na shiga na zauna, wani  sanyi da kamshi dadi ya shiga bugata. Hisham ya kunna karatun Alkur'ani cikin suratul bakara, kira'ar Sudais mu ka sake komawa gidan inna falmata.

Ai da sauri maigadin ya wangame mana gate yana kai wa Hisham gaisuwa.

Hisham ya zura hannu aljihu yafito da hannu a dunk'ule ba wanda xai ce ga abinda yake Cikin hannun irin kyautar da annabi yakeso hannun hagu bai san abinda dama ta bayar ba. Ya mannawa mai gadin
Koda ya tsaya da motar sake russunar da kai yayi yace"dan Allah umma ki yi hak'uri yanxu zan  fito idan ya huce ynxu ba zan samu damar zuwa ba don gaskiya bani da lokaci, amma ki bani minti biyar kacal"
Umma da sauri ta ce "Haba Hisham wallahi bakomai kaje ka xauna ku gaisa a nutse mu ba bakin xafi bane." fita yyi Yana cewa "Nagode umma"
Na bishi da kallo na ce " NAGARI A BAYA MUGU."
Umma ta ta watso min harara tace "kinga dan arziki kenan irin Al barka, ke ynxu don Allah wannan bai zame miki ishara ba? Ai ba duka aka taru aka zama daya ba."
Gum nayi da bakina don kam bani da bakin magana.
Mintuna biyar d'in daya fada kuwa cif ya fito har kofa Inna falmata ta rakoshi don ina hango ta ta cikin duhun gilas din motar, sai dai ita bai xama lallai ta gan ni ba. Da sauri har da sassarfa ya k'araso daidai lokacin da barorin hajiya suka biyo shi d'aukeshi da wasu manyan kwanuka masu siffar kwalba. Kusa da umma suka ajiye ina kallon su suna mana kallon mamaki.
Hisham yaja mota muka tafi
Koda muka isa gida,shi ma fita yayi daga motar ya d'au flask din nan biyu na taimaka na dauko masa biyun, don dole na dauka ba don komai ba, Saboda daga gidan falmata ya zo.
A tsakar gida yace na ajiye na samu plate na zuba masa kad'an tamkar  na kwarara ihu haka na ji, don tilas dai na nufi kitchen. Umma ta ce, "ki d'auko masa a fararen plastic din nan"
"Tom" nace na burma kitchen.
Kawo masa na ya ce,"Bubbud'e ki zuba min, rigimar Inna ce daga ta yi min tayin abinci nace sauri na ke ba zan samu ci ba, duk da ina jin yunwa, shine ta biyo ni da wannan tulin abincin."
Umma murmushi ta yi kawai daga gani kasan na yak'e ne ta ce"Ai ta taimaka ka kuwa baka ce rigimarta ba."
Na taso ba don  na so ba a' a sai dan ganin idon umma na bubbud'e flask d'in na farko farfesun dakwalen kaji ne,na biyu kifi ne,irin manyan kifin nan da ake kira ragon ruwa, sai  na uku shikuma sinasir ne da waina masa, na hudu kuma hadaddiyar basmati rice ce
Abincin kam ya hadu,na fara xuba masa.
"Kad'an _kad'an, za ki zuba"ya ce da ni cikin wata salon murya".

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now