40

112 8 0
                                    

Zumuncin Zamani....

Na

Nazeefah Sabo Nashe

Book 3

Page 3


________________

A gaban dressing mirror take tsaye tana gyara sumar kanta, cikin kwalliya take sosai a k'ok'arin ta na son farantawa mijinta.

Yau da annashuwa da tarin yalwa da farin ciki fal ranta ta tashi. Ko bakomai dole ta godewa Allah ta San ta yiwa mata zarra da Allah Ya dubeta Ya bata mijin bugawa a jarida.

Abu 'd'aya da yake bata tsoro har ya sa mata bugun zuciya duk da farin cikin da take idan ta tuna iyayenta, da fargabar ba da amincewrsu ta biyo Hisham ba. Shin me za su 'dauketa? Y'ar da bata gudun b'acin ran su a koda yaushe ta fi son farin cikin mijinta... Ya zama tilas yau idan Hisham Ya dawo ta rok'eshi Ya kira mata Abba ta nemi gafararsa ko zata samu nutsuwar zuciya.

Sai abu na biyu da yake sake karyar mata da zuciya shine "Iyayen Hisham da ba su san bai saketa ba suna nan tare, wani hukunci za su 'd'auka anan gaba a duk yayinda suka San hakan?

Ta saukar da k'wayar idonta a hankali kan cikinta da Ya tasa ka'dan d'an wata hu'du. Ta Shafa shi a hankali ta furta "Allah ga mu gareka, Allah ka zama gatanmu a lokacin da ba mu da wani gata sai naka."

Ta na'de kanta da wani 'd'an kwali 'daurin Zamani da ake Ya yi. Ta sake ambulawa kanta turaruka masu k'amshi sosai sannan ta fice da sauri don tsoron kada girkin da take ya kama. Tuwo ne take yi da miyar kuka, shi Hisham 'din yake so kasancewarsa masoyin abincin gargajiya. Tsaf ta shirya su a saman dinning bayan ta dama masa kunun tsamiya da yake shan sa duk dare ta kuma ha'da masa dadda'dan zob'o.

Tsaf gidan yake zuba wani sihirtaccen k'amshi, kafin ta koma Parlour ta zauna tana kallon series film a tashar zee world.

Tun daga harabar gidan yake shak'ar dadda'dan k'amshin da ya saka shi lumshe ido bai shirya ba. A hankali kalmar "Alhamdulillah!" Ta fito daga bakinsa ba tare da Ya shirya ba. Tabbas samun Mace Ta gari shine kwanciyar hankalin 'da namiji cikon farin cikinsa kuma.
Ya ayyana a ransa bayan ya sauke maganansa akan kyakykyawar matarsa da ta mik'e itama cikin sakin murmushi ta yi hugging 'd'insa kamar yarda ya koya mata.

Tsawon mintuna Ya rungume da ita cikin lumshashshan ido kafin ya jata a hankali zuwa 'dakinsa. Don ta taimaka masa ya yi wanka kamar yarda ya koyar da ita.

Tsaf ta gyara shi cikin shigar da yake yi idan yana gida wando three quater da riga armless musamman idan ana zafi. Ta 'd'an sunkuyo saman kafa'darsa tana binsa da kallon so tana murza wuyansa cikin wani salo. Ya juyo da ita ta dawo saman cinyarsa Ya fara shafa cikinta "Baby na fa? Hope k'alau yake dai ko?" Ta lumshe ido tana 'daga masa kai. Ya lakaci kumatun ta yana matsa su cikin tsokana ya ce "Nan gaba ba fa y'ar lukuta za ki koma."

Ta cono bakinta kamar zata yi kuka ta ce "Yaya Hisham bana so fa."

Yana dariya ya kai mata sumbata a kumatu "Wai me yasa ba kya son k'iba ne? Baki son ni ina son Naga matata b'ulb'ul da ita ba." Ya fa'da yana saukar da idanunta saman k'irjinta Yana shirin kai hannu ta mik'e da gudu ta fice don ta San abinda yake shirin yi. Hisham Ya bita yana dariya.

Bayan gama cin abincinsu suna zaune saman kujera kanta a saman cinyarsa, da wayarsa a hannunta tana buga game. Kawai sai ta ga kira ta shigo Wife 2 ta ga an saka. Take annurin fuskarta ya 'd'auke ta mik'a masa wayar tana shirin barin wajen ya janyota da sauri. Yana amsa wayar "Ya aka yi Fareeda?" Tsawon minti biyu yana wayar kafin ya kashe ya mayar da kansa kan Sauda da take ta faman cika tana batsewa. "Haba Uwar gidana first love 'dina, me zai dame ki da ita, ina tabbatar miki ko mata uku na aura kece a gabansu, bari na fallasa miki sirrin zuciyata ban tab'a son wata mace sama da yarda nake son ki ba, tun ban san ki a matsayin mata ba balle yanzu dana sanki ciki da bai."

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now