34

121 8 1
                                    

Zumuncin Zamani....

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

Ba zan yarda ki ha'da zuri'a da mutanen da basa son ki ba, Ba don komai zan saka a zubda cikin nan ba sai don na tabbata kafatanin zuri'ar ubansa ba za su so shi ba, saboda ya fito daga tsatson talauci idan kuwa ta tabbata kin haihu da su wani farin ciki kike zaton 'dan ko 'y'ar za su samu?"

Shiru Saudat ta yi zuciyarta na dukan uku-uku, sam bata son ko da cikin ne ace za'a zubar mata da shi, da Umman zata bi tata tabbas da ta ce mata ta bar mata abinta tana son sa. Amma hakan ta ja bakinta ta yi gum tana bin Umman duk in da ta saka k'afarta kamar rak'umi da akala.

Sun ci matuk'ar sa'a sun Samu Sadiyar a gida bata tafi aiki ba.

Da fara'arta ta taresu zamontowarta a cikin mata wayayyu ta dinga jera musu "Sannunku da zuwa." Ta fa'da tana malala musu shimfid'a a tsakar gidan.

Umman ta zauna tana fa'din "Yauwa Sadiya, sai ki gan mu katsaham da yamma tsaka"

Sadiya ta saki murmushi "Waye ba lafiya? Ba dai Saudatu manyan likitoci ba."

Girgiza kai Umman ta yi ta ce "Ko 'daya wallahi, lau muke daga ni har ita, kawai dai watanni biyu al'adarta shiru ga shi yanayin jikinta duk na ga ta canja shi yasa na ce bari na kawota ki auna min ita."

Sadiya ta juya tana duban Sauda da ta yi kicin-kicin da fuska ta mik'e tana zaro wata y'ar roba ta mik'a mata "Shiga ga toilet nan Sauda ki yi yo fitsari ki kawo min." Sauda ta amsa ta shige 'd'akin da ta nuna mata Wanda toilet 'din yake ciki.

Sadiya ta juya ta kalli Umma, ta ce "Ai babu tantama Umman Sauda ciki ne da Sauda, ga alamu nan sun nuna yarinya ta 'danyance ta yi luwai da ita."

Umma ta zabga hannu a kumatu tana jan Innalillahi kafin ta ce "Bana fatan hakan ta kasance Sadiya, ke aminiyata ce ba wacce zan b'oyewa komai b'ace Allah ne ta ha'da jininmu da ke Idan Har ta tabbata Sauda ciki ne da ita to zan rok'i alfarmar ki a zubda cikin nan ba wanda ya ji ba wanda ya gani."

Sadiya ta zaro ido tana fa'din "Zubarwa kuma Umman Sauda? Me yayi zafi haka? Ina ce Sauda da aurenta?"

"Da aurenta tabbas, ku shaida ne tunda kun je bikin Amma b'arin cikin a jikinta akwai matsala...."

Nan ta shiga bata labarin matsalolin da suke cikin auren Saudan.

Daidai lokacin Sauda ta fito ta mik'a mata y'ar kwalbar mai 'dauke da fitsarin a ciki.

Sadiya ta 'd'auko abinda ake auna ciki ta auna. Tsawon mintuna biyu kafin ta saki murmushi ta ce "Ai ni dama na San ko ba a auna ba ciki ne da Sauda."

Umman Sauda ta saki tsaki ta ce "Ai dama na San za'a rina. Abin mamaki dare 'daya fa jal ta yi a gidan mijin amma har ta k'unso ciki, kai yaran Zamani! Ko ko don ubanki kina binsa ne hotel kina ba shi ha'din kai bayan kin baro gidansa."

Da sauri Saudat ta girgiza kai. Sadiya ta saki dariya kafin ta ce "Ke ma dai Umman Sauda da rigima kike banda abin ki mace da mijinta kuma ba sakinta ya yi ba daga samun sab'ani har ki tuhumeta irin wannan kamar wata saurayi da budurwa, balle ma a dare 'daya idan Allah ya nufi ikonsa sai ya bata cikin ko don ya ga k'arshen iyayensa marasa mutunci. Ni da zaki bi ta shawarata ma wallahi ba za'a zubar da cikin nan ba, barinsa za'a yi bak'in ciki ya kashesu."

Umma ta girgiza kai "Ba dani ba Sadiya, idan su bak'in ciki bai kashesu ba, ni sa kashe ni da bak'in cikin yanzu ma Ya aka cika balle su ji wannan labarin ni dai ki taimakeni ki bani maganin da zai wankeshi tas tunda ba wani girma ya yi ba. Ko ma a Ina suka yayi bo shi ita ta sani ni dai ta k'arfin tsiya sai na cire shi."

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now