2

194 12 0
                                    

ALK'ALAMIN JIKAR NASHE

Zumuncin Zaman

📄 2

Umma ba abinda ya dameta da umarnin da aka bata, madadin b'acin rai ma a fuskarta sai fara'a take tana jaddada Allah ya raya d'iyarki Munira ya yi mata Albarka, alfarmar annabin Rahma.

Cikin shan k'amshi mai jegon take amsawa da kyar sai wani muzurai take tamkar Umman sa'arta ce sai kace Umman bata haifi wad'anda suka girme mata ba, kawai don dai ba ta da kud'i shi yass bata da wata daraja da k'ima a idanunsu. Ganin Umman ta mik'e sai ni ma Na mik'e na bi ta a baya, har na kusa k'ofa na ji muryar Muniran cikin gadara tana cewa "Ke Sauda ba kya gaisuwa ne? Saboda rashin mutunci kina ganin mutane ba za ki gaishe su ba?" Na juya na zuba mata wani kallo kafin na ce "Shi yasa naga kin gaida tawa uwar.. uwa ai ba tafi uwa ba.." A fisge ta d'ago ta zuba min na mujiya "Kan uban can ashe fetsararki da rashin mutuncinki yana nan? Shegiya kina y'ar talaka sai girman kan banza, ciki fal yunwa.." Na jiyo zan bata amsa a zafafe don har wani turirin b'acin rai nake tsabar tunzira da zuciyata ta yi. Ji na yi kawai Umma ta damk'i hannuna da sauri don ta san ba zan furta mai kyau ba, muka fice duk da turjewa da na ke. Aljihun rigarta ta zira hannu ta d'auko Naira d'ari wanda ba na haufi ita kad'aice da ita ta manna min a tafin hannuna "Maza wuce gida kada ki tsaya a ko ina, kuma ki yi ta jan matayassara minal k'ur'ani daga zuciyarki zaki samu sauk'in nauyin da zuciyarki ta yi." Idona jajur na d'ago na zube su akan fuskar Umma "Amma Umma....." "Kada kice komai Sauda wuce maza ki je Allah ya yi miki albarka wata rana sai Labari, babu wani abu da yake dawwama a duniya, komai na cikinta hudusin fana'un ne, fararre k'ararre haka manzon rahma ya ce, da kin d'auko irin zuciyata da ta ubanki da duka abubuwan nan ba su dameki ba." Cikin sauri kawai na juya na fice daga gidan hawayen takaici yana zuba daga ido na.

******

Sai dare bayan magriba sannan Umma ta dawo, kai daga ganin ta ka san a wahalce take sai haki take saukewa da ajiyar zuciya, hakan yasa na mik'e na kawo mata ruwan cikin randarmu mai sanyi. Na dubi hannunta da take karb'ar ruwan har rawa yake tsabar gajiya ko take away d'in bikin na san basu bata ba, k'iri-k'iri suke bawa masu ido da kwalli ko kunya a hana ya ku bayi. Tsaki na ja a fili na ce "Kin gani ko? Haka kawai kin je kin wahalar da kan ki a banza don ba gani za suyi ba matsiyata." Umma ajiyar zuciya ta yi kafin ta ce "Ba burina dama su gani ba, Umarnin Manzon Allah (S.A.W) Na cika da ya ce a sadar da zumunci, da dukiya da jikinka, tunda kuwa ba ni da dukiyar da zan bayar, dole ne na yi da jiki na Allah yasa mu dace." Ta kafa bakinta ta sha ruwan sosai sai da ta kusa shanyewa sannan ta dire kofin tana fad'in Alhamdulillah, Sai bayan da kika taho na tuna gudar d'arin kenan na baki ba ni da kud'in mota, don haka da sayyadata na tako." Na tab'e baki don na tabbatar wasu daga cikin su sun zo wucewa da mitocinsu kuma sun gan ta, don sun saba su gan mu muna tafiya a k'afa su bad'e mu da k'ura su wuce..
Hmm, duniya kenan idan kana cikinta zaka sha kallo.

Umma ta dubeni tana kama hannuna ta matsa shi sosai kafin ta ce "Sauda ki nutsu ki san duniya makaranta ce, ki daina sakawa kan ki b'acin ran mutanen nan a banza a wofi."
Na d'ago idanuna jajur suna kwararar hawayen bak'in ciki na ce "Don Girman zatin Allah Umma ki rabu da mutanen nan, ki daina shiga sabgarsu mu tsaya iya matsayinmu kawai tunda ba sanin mutuncinki suka yi ba."

Murmushi ta saki kawai kafin ta ce "Sauda kenan! Cewa za ki yi Umma ki daina bin Umarnin Manzon Allah (S.A.W) ki dawo bin umarni na, kin ji Uwata haka ya kamata ki ce, to ba ki isa ba, har abada kuwa. Me za'a yi da mai yanke zumunci? Ke ma so nake ki yayyafa wa zuciyarki ruwan sanyi, don Allah ki dinga sakin ranki da fuskarki idan kin shiga Dangi."

Na yi tamkar na ji nasiharta, amma ina! Sam ni na san irin bak'in cikin da yake rura wuta a zuciyata. Na lumshe ido sai ga wasu siraran hawaye sun zubo min.

Umma ta saka salati had'e da rungumeni a jikinta tana buga bayana alamar rarrashi "Kuka kuma Sauda? Yanzu kuma ki ke fisabilillahi menene abin kuka anan? In dai kika ce za ki dinga saka irin wad'annan damuwoyin na duniya a zuciyarki to tabbas ciwon zuciya zai kama ki."

Sunkuyar da kaina kawai na yi a cinyarta ina sakin wata irin ajiyar zuciya akai-akai.

Maganar Umma ce ta sake katse ni da na ji ta ce "Bayan tahowarki kuwa da kad'an sai ga Yayanku Hisham ya dawo daga k'asar da ya tafi karatu. Tsawon shekaru sha biyar fa Kenan, sai yau ya waiwayi gida duk ya canja ya yi kyau sosai ya sake fari da kyau tamkar d'iyar larabawan Qatar."

Tab'e baki kawai na yi ba tare da na furta komai ba, na shige d'aki a zuciyata ina mitar "Ina ruwana da Wani Hisham, ban ma San shi ba, duk wani jinin Baba Hamza ni cikakken mak'iyi nake d'aukansu balle wannan da ban sani ba.
Umma dai ba tabi ta kaina ba tana daga zaune ta cigaba da laziminta tana sakin d'an murmushi da alama zallar rigimata take tunani.

*******

Da y'ar wak'a ta na shigo gidan. Dawowata daga islamiyya kenan. Yaya Khalil ya zabga min harara "Wai ke shashashar ina ce? Ki shigo ko sallama babu kuma kina tafe kina wak'a kamar matan k'auye sun dawo daga dandali."

Raina na had'e dama shi kullum ba ma shiri da shi, mun fi shiri da Yaya Sa'eed. Na cire hijabi na na sak'aleshi akan igiyar shanyar da take tsakar gidanmu, sannan na na shige d'an d'akin girkinmu na langa-langa da yake gefe. Abinci nake nema don dama gwanace ni a wajen ci.

Yaya Saeed ya dubi kwanon da na zubo shinkafa Manja da yaji sai salad daga gefe, yau murna ce ta cika ni musamman da naga har salad aka saka mana a abinci, tsaki ya ja ya ce "Acici kenan, ke ba ki da aiki sai cin abinci kuma a rasa ina abincin yake tafiya a jikin ki."

Na kuwa zunb'ura baki don idan da sunan da na tsani a kira ni da shi to wannan sunan da Yaya Saeed ya saka min ne. Ina Shirin ba shi amsa wani sassanyan k'amshin turare ya doki hancina, kafin sallamarsa ta bayyana, cikin murya mai tarin kamala da nutsuwa.

Da sauri na juya don son ganin mamallakin muryar "Wai! Subhanallah! Fatabarakallahu Ahsanul khalik'een.." shine kawai abinda na samu damar fad'i a zuciyata, don ganin tsananin kyau da kamala gami da Haiba da cikar zati na wannan bawan Allahn tamkar shi ya halicci kansa da kansa.

Ban san shi ba, ina kuma mamakin yarda ya shigo mana gida kai tsaye.

Yaya Khalil na ga ya saki murmushi ya kuma mik'e da sauri had'e da fad'in, "Hisham saukar yaushe?"

Wani k'ayataccen murmushi ya saki, da ya sake k'awata fuskarsa amma madadin in ga kyawunsa, sai naga duk wani kyansa da nake gani yana dushewa ya koma muni. Tun daga lokacin da Na ji an ambace shi da Hisham na san shine wanda jiya Umma take bani labarin dawowarsa. Da sauri na d'au kwanon abincina na shige d'aki don kada ma ace na gaisheshi, Bana son sake ganin fuskarsa da ta rikid'e ta koma min tamkar ta bak'in kumurci. Bana marabtar duk wani zuri'a ko jinin danginmu musamman d'iyoyin gidan Baba Hamza da basa daraja da martaba iyaye na. Abin haushi da saka takaici su Yaya Khalil na ji suna ta murnar dawowar ta sa da rawar jiki da shi.

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now