32

131 11 1
                                    

Zumuncin Zamani.

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

____________

Ganin kamar bai yi Maraba da kusantar da ta yi masa ba, ya sa ta koma can wata kujera gefe guda ta zauna ta nutsu sosai ta yi nisa cikin buk'atuwa da sha'awarsa fal a ranta, ga shi ba shi da lafiya, duk da Har a lokacin wata mu'amala ta aure bata tab'a shiga tsakaninsu ba.

Shigowar Mahmud ce ta farkar da ita daga tunanin da ta lula, ta zubawa Mahmud 'din ido shai'dan yana tunzira zuciyarta da wasu irin tunaninnika ayyana mata Mahmud 'din yake a zuciyarta a matsayin mutumin da zai yaye mata damuwarta. Sam a k'ira da fasali ba shi da banbanci da Hisham sai ma yarinta da ya fi Hisham 'din.

Bai lura da ita ba balle ya ga idanun data kafa masa sai dai a jikinsa idanun nata ya yi tasiri don ya ji ana kallonsa. Ya k'arasa wajen Hisham 'din yana fa'din "Yaya, bari ni na k'arasa gida tunda na ga Madam ta kasa ta tsare ga shi dare Ya yi."

Da sauri Hisham Ya ware idanunsa a kansa murya a cunkushe da b'acin ran uzzira masa da Fareeda ta yi ta kada ta tsare ta hana shi kiran Saudat ya ce "Ban gane ka tafi ba? Dama ba kwana za ka yi ba?" Da baki Mahmud 'din ya nuna masa Fareeda ha'de da fa'din "Ai na ga Big Aunty zata kwana" girgiza kai Hisham Ya yi ya na kai dubansa gareta "Ki kimtsa Mahmud zai ajiyeki a gida, shi sai ya dawo ya kwana anan 'din"

Itama idanun ta dallara masa "Ya za'a yi na tafi na bar ka Dear?" "Kin tab'a ganin mace ta yi jinyar namiji in dai yana da mai kula da shi? Ki tashi Ya kai ki gida sai ki dawo da sassafe."

Ya fa'da cikin dakakkiyar murya

Fareeda ta mik'e tana zumb'ura baki. Mahmud dubanta kawai yake yana murmushi a zuciyarsa yake ayyana "Tabbas Y. Hisham ya more da kyakykyawar mace, ina ma ni ne." "Wuce ka kaita." Ya juyo muryar Hisham 'din da ta farkar da shi daga wancan bahagon tunanin na k'iyasta kamanni da surar Fareeda a matsayin matarsa.

Suna fita Hisham Ya runtse idanunsa yana sakin ajiyar zuciya sai ji ya yi kamar an Zare masa k'aya, yanzu ne zai samu damar kiran Saudatunsa. Duk da baya son kiranta ya tayar mata da hankali Amma ya zama dole don zuciya da ruhinsa Saudatun kawai suke son gani.

Suna shiga motar suka samu bak'uncin shiru kowa da abinda ya ke kaikawo a zuciyarsa Fareeda kam a yanzu Shai'dan Ya Riga ya rinjayeta ji take tamkar ta afka jikin Mahmud ta rungumeshi tsabar yarda take jin sha'awarsa. Shi 'din ganin kamar Ya harbo jirginta kawai sai ya kasheta da kallo ido k'asa-k'asa ya ce "Ya dai Madam?" Wani irin ras ta ji tsigar jikinta ta tashi sosai jin yarda Mahmud ya kashe murya Ya ranga'da mata sunan Madam tuni wutar sha'awarta ta sake ruruwa itama ta zuba masa ido tana jingina bayanta jikin kujera da da dama data buk'aci Mahmud 'din ya kusanceta a lokacin.
Mahmud Ya saki murmushi tabbas yanayin kallon da take aika masa ya tabbatar da hasashen da zuciyarsa take masa ga wani turarenta da yake sake angizashi zuwa ga muradin zuciyarsa, da k'yar ya yi controlling kansa ya ja motar bayan ya kunna wani irin cool music.

Idanunta a lumshe suke ta ji Mahmud 'din ya ja burki hakan yasa ta bu'de ido tana sauke kallonta a kansa. Cikin murmushin da yake yaudarar y'an mata da shi ya ce "Bari na samowa Big Madam Ice cream
Ko?" Fareeda jiki a kasalance ta sakar masa murmushi ita ma ta ce "Kada ka je ka kwaso min tarkace let me follow you." Suka shige wajen Ice cream 'din yarda suke tafe suna gugar jikin juna idan ka gansu sai ka zata mata da mijinta ne.

__________

Sau kusan uku wayar Saudan tana ringing har ta mutu bata 'd'auka ba, ya kai dubansa kan agogon wayar da sauri Ya ware ido tabbas yarda ya san Sauda da saurin barci ya san tuni ta yi nisa a barci. Amma bai hak'ura ba ya cigaba da danna mata kira. A cikin barci ta dinga jin k'arar wayar da sauri ta bu'de idanunta ta janyo wayar ta mik'e zaune da sauri ganin Hisham ne akan wayar, don da tunaninsa ta kwanta da shi kuma ta yini cur ganin wuni guda bai kirata ba abinda bai tab'a yi ba. Cikin muryar barci ta masa sallamar. Muryar da ya ji ta tsarga masa har cikin k'arshen zuciyarsa. Ya saki ajiyar zuciya don sosai yake son muryar Saudatunsa shi yasa a koda yaushe muryar take sanya masa kasala don haka bai fiya amsa wayarta a gaban kowa ba don ko ya ya ya ji muryar tata sai ya lumshe idanunsa. Ya ji tamkar Ya fasa wayar ya rungumota jikinsa.

Zumuncin ZamaniOnde as histórias ganham vida. Descobre agora