chapter 5

84 6 0
                                    

YAR AREWA(T/N/G)
5⃣
Tunda ya zagi ubanta bata sake cewa komaiba har suka isa adamawa,
Zuciyarta wani zafi kawai take mata dan ko amakaranta inkaji fadan ta to anzagi ubanta ne,amma babu komai zata biyasa bashin da ya cimata,

Tundaga kofar Shiga babban gidan sarautar zakasan cewa anyi manyan baki ,
Cire damuwar shuraym jasmine tayi akanta ta nemo duk wani farin ciki tasaka a cikin zuciyarta tana mai cike da daukin ganin dada da ardo,
Motarsu na tsayawa kamar rige rige suke ita da twins suka kwasa da gudu sukayi hanyar da zata sadaka da cikin gidan,
Dada !!
Dada!!
Suka hau kwada mata kira,
Tanajiyu sautin yan jikokinnata ta fito daga cikin store din da take bawa masu aikinta umarnin su jera abinci tace yan jikokin dada cikin harshen ta na hausa wanda bai goge ba,
Kokarin dane ta suke abuh da ya shigo yace kai kai kar ku karya mun dada mana ,
Murmushi tayi cikide da alkunya irin na fulani tace barsu nan insun tafi kafun na kuma ganinsu zan jima ,koma zan sake saka su idanunne ko rai zai halinsa Allah kadai ya sani,
cikin shagwaba jasmine tace kai dada bazaki mutu ba  sai kin hau tukina na jirgin sama na kaiki shan ice cream a London,
Dariya sukayi suka zazzauna a katon falon da yasha zanen fulani na gargajiya ,
Gaisawa sukayi cikin farin ciki wanda baya boyuwa,
Addua dada tayiwa shuraym da fatan Alheri .
Daga nan bata ja ba dan ita ba kaka bace mai wasan jika saboda magana ma wani lokacin wuya takanmata ,
Wasu sukance saboda ita din yar gidan mulkice dan mahaifinta shine sarkin babbar rigar da aka auro ta duk da bata kai tasu ardo ba amma babbace kuma da sarautar tasu irin ta fulani"

Waini dada ina angonane,?
Jasmine wadda take ta fama kallan ta inda ardo zai fito ta tambaya dan taga alamun babu mai tambaya,
Abuh ne ya bata amsa da yananan shigowa jasmine kwantar da hankalinki a chan haraba yayi aike,
Wani banzan kallo shuraym ya bata wanda ita kadai ta gani dan haka ta murguda masa baki,
Dauke kansa yayi dan har ga Allah yanajin zafin rashin kunyar da take masa musamman idan ya kalleta yaga duka sa'ar kannesa ne abida da akeela sannan ko hauka suke bazasu taba yi masa rashin kunya ba kamar yarda take masa and yafi danganta hakan da rashin samun isashen coaching na rayuwa dan kawai ta rasa mahaifiyarta and baya tunanin wannan shi zaisaka a kyaleta tana yima na gaba da ita rashin kunya,

Sallamar ardo ita ta katse masa tunaninsa ,
Hade rai yayi dan yasan yanzu zai fada masa sunan tsokanarsa gaban wannan yarinyar and tabbas ta kuskura ta kirasa da sunan sai ya zubar mata hakoranta,
Kamar kuwa yarda yayi tsammani yana zama yace fuadu gyara nan zamanka nagano tuwo a madara,
Lokacin da yana yaro zuwansa na farko adamawa da dan wayansa kadan aka kawo musu fura da nono da zumudinsa yaje zai sha amma yana saka ludan cikin kwarya yaji ya dauko gayan dawo ya kalli dada yace dada mai ya kawo tuwo a madara,
Tundaga nan ardo yakafa tsokanarsa,

Bata rai yayi ,sandan da ardo ke dan dogarawa ya daga yace kai fuadu gyara na zunguru dan banza mai sudadden gemu,
Tsintar kansa yayi da saka dariya yace kai ardo nikam ina wuni bamu gaisaba,
Cikeda kaunar iyalin nasa yace aa fa nan fa daya ku matsalar azauna hira da ku baku iya yaranku ba tunda iyayen ku sun koya muku yaran yahudu sunki koyardaku harshen ku idan shi dannan (abuh)baya zama ai ita innanku tana zama ko,

Mama
Cewan shuraym ".
Kara zungurosa ardo yayi yace kajimun dan kusu  ar mene wani mama"
Gyaran murya jasmine tayi tace ardo ko na tashi na komane tunda kazo hamma shuraym kawai Ka yiwa magana and kamar bakaganni ba bakaga abida da akeelah ba gwanda hamma fuadu kace ya matsa zaka zunguri tuwo cikin madara,
Dariya gurin ya dauka banda shuraym wanda ya saki baki yana kallanta da mamaki ,
Alamu ardo yayi ma jasmine da su twins yace kuzo kuji dumin kakanku ,
DA gudu mimi ta rigasu tana dariya,
Sai bayan sun gama wasanninsu ne sanann ya saurari Abuh da su fatosh dake faman gaisar dashi tuntuni,.

Kowa yasan masaukarsa dan haka after angama gaisawa da hirar yaushe gamu kowa ya wuce masauki inda mazan suka wuce masallacin gidan danyin sallah,.
Nan sauran yan uwa dake cikin sashe daban daban na masarautar suka fara zuwa kawo gaisuwa da kawo mutsa baki da kuma taya shuraym murna .
Babbane gidan da ya kunshi duk wani dan uwa na ardo ,zaka iya kiranta da modernize riga  dan gurin gwanin shaawa yake
,yayan ardo da dada biyu daga mahaifiyar jasmine sai abuh sai kuma fatosh da suka rika ,duk da haka basu jin kadaici saboda yayan yanuwa da yawa nan gurin suke al'amuransu na rayuwa ,.

YAR AREWA(THE NORTHERN GIRL)PaidWhere stories live. Discover now