chapter 2

119 7 0
                                    

YAR AREWA (T/N/G)
2⃣

Abincine gabanta amma deep down wani tunanin take,
A tsanake fatosh take kallan yarda take ta jujuya abincin gabanta da spoon din,
Shafa gefen fuskarta tayi tace"
Jasmine kina yar karamarki tunanin me kikeyi haka,mene yake damunki tell me,
Batareda ta bar abunda take da spoon din ba tace aunt fatosh wai babu kyaune mace tace tana san ta zama pilot ,
Teacher dinmu yau a school ta tambayemu abunda muke san zama in the future and I said female pilot shine fa suke ta mun dariya shine na tambayi teacher din babu kyaune and she told me that wai akwai female pilots amma mostly ba yan arewa bane finding yar arewa is rare she said alot of things amma ni i don't get her and she said being in south doesn't make me one
Wai i should always know where I come from and wai nayi ma daddy magana ya zabamun wani abunda nake san zama idan na girma and aunt kinsan ever since daddy took me to cockpit da zamuje Sweden nagan yarda uncle haris yake nuna yanasan abunda yake naji nima inasan zama haka and insha Allahu i will surprise you all,

dan dariya fatosh tayi zuciyarta fal haushin wannan malama ta su jasmine,
Spoon din ta karba ta fara bata abincin a baki cikin kwantar da hankali irin na manya ga yaransu tace "
Jasmine you're your father's daughter and nasan duk abunda kika saka gaba zaki yi nasara akansa so forget about that your so call teacher's words kece zaki zama first female pilot a cikin dalibanta ,
Tashi tayi daga cin abincin tana rawar murna tana cewa,
Welcome on board ,this is captain jasmine Bilal speaking and I have some information about our flight ....tana kokarin sake cewa wani abu taji tai gware da mutum wanda babu wata wata ya hankadeta,da sauri fatosh ta taso ta kamata tace haba Bala idan kuma ta fadi taji ciwo fa,
Gudun karyayi mata rashin mutunci ta kullacesa ta hanasa bukatarsa idan yazo nema gurinta yasa ya matsa shima ga jasmine wadda ke ta faman zazzare idanu dan Allah ya zuba mata balai tsoran uncle Bala,
Hannunsa yasa akan na fatosh daidai inda ta rike jasmine yadan shafa yace sorry sweet jasmine uncle ya tsorata ne,
Ture hannunsa fatosh tayi dan tayi tunanin ko bai kula hannunta ya taba ba,
Kallansa jasmine tayi tace uncle sweet jasmine fa kace mun and ni ban taba jin kafadamun haka ba kullum ka ganni sai kayita harara na musamman idan kana hira da mummy, kullum sai inacewa maybe namaka rashinji ban sani ba rike kunnuwanta tayi tace im sorry uncle"

Bayasan yarinyar ko kadan sannan surutunta yana daya daga cikin abunda yasa yake kaffa kaffa da ita dan akwaita da dauke abu da ganewa amma dole idan yanasan ya samu kan fatosh to dole ya nuna yana san jasmine dan bakaramun sha'awanta yake ba duk da kullum a suturce take amma hakan baya taba boye halittunta wadanda yake kwadayi kamar yayi me,duk yawan barikinsa baitaba ganin macen da yake san dandana dadinta kamar masifa ba irin fatosh and yasan daga ganinta no nonsense ce amma babu abunda zai hana ya sharbeta,
Ledan dake hannunsa ya daga yana murmushi yace jasmine uncle bought you chocolates"
Kamar bazata karba ba amma sai ta mika hannunta ta karba tace uncle wannan ne first abunka daka taba bani,thank you ".
Murmushin yake yayi a ransa yace shegiya mai yagagge baki amma a zahiri kuma sai cewa yayi im sorry honey bana duty na a matsayina na uncle dinki and i was busy with work amma daga yanzu muna mission din da zan zama favorite uncle dinki"
Yatsanta guda daya ta mike masa,
Kalla yayi alamun bai gane mai take nufi ba ,
Dafa hannunta tayi a goshi tace ooppzzz aunt fatosh uncle baisan pinky promise ba,
Jawo hannunsa tayi ta fito da pinky finger dinsa ta hada da nata tace and uncle duk wanda ya karya alkawari zai zama monkey"
Shafa gefen fuskarsa yayi cikeda kosawa dan idan jasmine tafara bata gajiya amma dan biya ma kansa bukatarsa zai jure,
Rungumeta yayi yana shafa bayanta a hankali,_
Itadai fatosh yar kallo ta zama sannan taki tafiya sabida wannan sabuwar halayyar bala tana tantama akanta"
Sai wani mayen kallo yake bata ,dauke idanunta tayi a kansa sannan ta juya tabar gurin ,tana tafiya ya dan ture jasmine ya tashi ya fita dannemarwa kansa wadda zata kashe masa wuta saboda ganin fatosh kawai ya tada masa tsumi,
Da dan mamakin abunda yayi jasmine tabi hanyar da yafita da kallo,daga kafadarta tayi ta dauki ledan tana ta murna tashiga tana kiran fatosh ,
Kwace ledan fatosh tayi tace Jasmine too much chocolate is not good for you Kawo na aje miki cikin chocolates dinki kidai sha na hannunki,
Batayi mata musu ba ta mika mata ledan tana cewa i will take two to school Zan bawa frnd dina amad daya nasha daya jiya shima raba mana chocolate dinsa yayi he's my best friend,.
Cire kayanta tayi tace aunt fatosh kizo ki cuda mun bayana wanka zanyi,
DA gudu ta nufi hanyan bathroom din hannu fatosh tasa ta janyota takada mata kai,
Washe mata hakora tayi sannan tayi adduan shiga bandaki dan tasan abunda riketan da tayi yake nufi,kafar hagu ta shiga dashi kamar yarda fatosh ta koya mata,
Shafa mata mai tayi a baya sanann ta barta ta karasa dan jasmine indai iyayine ta nan gurin ta iya,
Gyara mata kanta tayi tamata two braid dan shikadai yake zama akanta sabida santsi,
Kanta ta dora kan cinyar ta tace aunt im bored here yaushe zamuje abuja im missing  su abida da akilah,and little mimi,da hamma fuad"
Amma I don't miss hamma SHURAYM har yanzu ina tuna dukan da yayi mana nida abida dan kawai mun shigar masa daki munyi wasa da perfs dinsa as teddy and I told him fa aunt abunda yasa mukayi wasan dasu saboda shi bashida teddy a dakinsa shinefa ya zane mu and he even call me wai spoilt blonde brat ,I don't like him.

Murmushi fatosh tayi tace to kema jasmine in banda abunku mai yasa kuje masa daki bayan saida abida ta fada miki bayasan ana taba masa abunsa amma kikace mata babu abuna zaiyyi muku ,i remembered everything,
Pouting lips tayi tace shikenan dama aunt fatosh ai nasan kinfi sanshi tunda ranan ma bayansa kika goya amma mama tayi masa fada sosai ai tace kar yasake duka na .
And God I miss mama da Abu ,
Abu kullum sai ya bani cookies, naso na dade a chan amma daddy yace school amma aunt yaushe zamu sake zuwa,

I don't know about you amma kinga ni Hamma abubakar yakirani ya sanar dani zasuje OHIO graduation din Shuraym ya  gama karatun pilot dinsa a nan ohio state university US so zasuje chan and nikuma zanje abuja kinga its shuraym not  fuad so baikamata ace kinje ba tunda baki sansa nidai zan tafi naje i cant afford to miss wannan babban abu da yasamu shuraym i talked to your daddy ma da nace tare zamuje and har ya yarda amma yanzu tunda kinga you dont like hamma shuraym ai sai ki cinye midterm break dinki keda mummynki tunda daddy ma yana lagos,

Tashi tayi daga kwancen da take tace haba aunt fatosh ai da kafun nace miki i don't like him kince mun pilot ne yanzu da ko karya nayi nace i like him amma yanzu ma na janye abunda nace Allah i like him dan Allah kije dani kinji aunt dina mai kirki mai san jasmine din daddy please....

Dariyanta ta hadiye ta kara bata serious face tace ina ai aikin gama ya gama kinriga kin fada so kinga dai na tafi ni kadai ooo i cant wait to see lovely twins abida and akila and little mimi ga fuad ga shuraym come on yarinya an barki baya I will make your favorite cookies na aje miki a gurin da na saba aje miki xan deba miki kayanki na mayar part din mummy dinki kinga sai ki zauna a chan kafun na dawo, bakida matsala altine mai mata aiki zatana dauko miki kayan da zakisa sai tazo tana kwana dake ma ,
Kuka ta fashe dashi tace aunt please ,Allah inasan hamma shuraym sosai sosai ko naji rashin sansa zai dameni zan hanasa bazan sake fada ba dan Allah kije dani ,
I don't like this house idan baki nan babu daddy ,
Daga mummy sai ni sai altine sai su soldiers din chan da suka cika mana gida dan Allah aunt i promise to be a good girl,
ganin da gaske kukan take yasa fatosh cewa to naji zakije gobe zamu wuce abuja daddy yace  akwai helicopter da zai tashi yaje abuja a airforce base gobe and he will send someone da zai dauke mu,
Tashi tayi tana rawar murna tana waka zataje taga su abida,.

******************
Doctor Abubakar saudaki babban yayan sultanane wanda suka fito ciki daya yataka babbar rawa wajen auren sultana da bilal saboda yarda bilal ya kwanta masa arai kuma irin soyayyar da suke ma juna ta tabbatar masa yaruwarsa batayi zaben tumin dare ba wajen zabensa a matsayin miji ,
Yaso auren fatosh amma sam takiya dan nauyinsa take so sosai ,
Dole ya hakura ammafa da santa acikin ransa har gobe,
Matarsa daya ziyada yar aminin mahaifinsa wadda ita kanta tasan soyayyar da mijin nata yakewa fatosh,
Takanyi kishi wani lokacin saboda yazama dole amma gudun karta shiga hurumin ALLAH yasa ta sassautawa ranta kuma a kullum take addua Allah yazaba abunda yafi Alheri,
Ziyada macece mai kunya da kawaici da tsoran Allah shiyasa a koda yaushe Alhaji Abubakar yake jin soyayyarta da ganin girmanta sosai sosai,
Yaransu biyar ,
Fuad  mai shekara 30 ne babba wanda ya bawa shuraym shekara 2 dagasu kuma Allah bai sake basu haihuwa ba sai da suka dau shekara goma sha shida sannan suka haifi twins Abida da akila sa'anin jasmine sai autarsu little mimi daganan kuma basu sake samun haihuwa ba,.
Zuwan jasmine da fatosh daya gidan dan ba wani san zuwa gidan fatosh take ba amma ganin yarda mahaifun su shuraym ya matsa yasa dole sukaje sukayi sati sannan suka dawo,
Sosai jasmine ta ji dadin gidan musamman yarda fuad yake fita dasu shakatawa sannan yarda ta samu abokan wasa su abida .

Washe gari karfe bakwai suka daga Abuja.

Share please.
Chu chu jay✍️

YAR AREWA(THE NORTHERN GIRL)PaidWhere stories live. Discover now