chapter 4

75 7 0
                                    

YAR AREWA (T/N/G)
4⃣
Wani mamakine ya saukar masa lokacin da ta kai hannunta kan cikinsa ,just the liver "
Hannunta ya cire ya kama kunnenta da karfi wanda sai da tayi ihu "
Shush yasa yatsansa kan lips dinsa yace keep quite kafun na karkaryaki na balla banza,
Ni sa'an wasankine ko kinga na miki kama da hamma fuad da kika raina ,
Hawaye take dan rikon yayi mata zafi amma bata fasa cewa "eh mana hamma shuraym kayi kama da hamma fuad tunda abuh da mama ne suka haife ku kaga ai dole zakuyi kama".
Rike kugunsa yayi ,mamakin shegen bakinta da bai bartaba yake ,
Kara Rike kunnen yayi sosai yace au bazakiyi mun shiru ba ko,
Wato ke yar karama dake amma har kinsan wani abu ajikin namiji ya burgekiko,
To ko baniba ko wani abune kikagani jikin hamma kikace ya burgeki sai na kusa karki shegiya mai idanun mayu get out now ,
Sakin kunneta yayi ya sake bata rai ko ya razanata ganin ta tsaya tana kallansane yasa yace bazaki wuce ba sai na saka belt na zane ki and ki kara shiga sabgata kisha mamaki dan sai na karya miki hannuwa get out,.
Tuna Dukan da ya taba musu yasa ta juya ta fara tafiya ,saida ta kai kofar dakin sannan ta juyo taga ita yake kallo ransa a bace ,
Kafarta daya tasa a wajen dakin sannan tace ,ai hamma idannunka sunfi kama da na mayu kamar wani mai jin bacci and hannuna da kakesan ka balla duk bakin cikinka sai na tuka jirgi kuma tare da kai ,
DA gudu ta fita lokacin da ta kai aya,
Karo taci da fuad wanda ya tarota yana cewa a'a honey lapia ina teddy din naki,
Saita kanta tayi daga hakin da take tace ban ganta ba then ta kara diba a guje dan tasan muddin tashiga hannun shuraym sai tasha dan uban duka"

sakalo shuraym yayi lokacin da ta fara masa rashin kunya har ta kwasa da gudu,
Kwafa yayi ,tabbas zai gyarawa wannnan spoilt Blonde brat dinnan kai indai tasake shigowa shirginsa sai ta gane bata da wayau dan sai ya zane ta blue black and wannan fitsarar da tayi masa ma sai tasan tayi,
Yanajin sallaman fuad bai kulasaba dan a ganinsa wasa da yake mata ne yasa take ganin shima zata iya rainashi.
Daukar teddy din fuad yayi yace mai kayiwa jasmine ne ,
Batareda ya kallesa ba yace mai nayi mata ko mai tayi mun Allah sai na karya yarinyar mutane tunda bata da tarbiya,
Kallansa fuad yayi yace kaikuwa komene tayi maka ai yarinyace kuma marainiya karinga kai zuciyar ka nesa,
Bai kuma cemasa komai ba dan kulasa ma is pointless dan tana marainiya sai akace ta ringa rashin mutunci ga manya wallahi sai ya gyarata,
Fita yayi a dakin batareda ya amsa tambayar da fuad yayi masa na mai yake masa a daki ba,
...
Drivers uku ne suka zo dan kaisu airport,
Tunda ta hango motar da hamma fuad ya shiga tatafi da gudu itama zata shiga amma sai taga su abida a ciki,
Kamar zatayi kuka ganin already ma motar da abuh da mama da little mimi suke ta fita saura guda daya wadda fatosh ke ciki and tasan definitely ita shuryam zai shiga ,

Fine girl kona fito ki shiga nan din,
Kada kai tayi tace a'a hamma kuje zanshiga na aunt fatosh,
Bamusu  motansu ta daga saura nasu da suke jiran shuraym,.
Cikin kufta milk ya fito kansa babu kula sai gashinsa da ya sha gyara wanda bashida yawannan na hauka ,tundaga nesa idan ka kalla zakaga shekin da yake yi,
Agogo yake daurawa a hannunsa, wani mugun faduwa gabanta yayi ,
DA gudu ta bude gidan baya ta shige kusa da fatosh ta zauna,
Kallanta fatosh tayi tace hala baki da gaskiya,
Gyara beret din dake kanta tayi gefe tace A'a kawai kusa dake nakesan zama,

gaban motan ya Shiga yana mai fadin bismillah kamar ance ya kalli ciki mirror,
Ya hangota ta wani hade rai ta sa janbaki ja ga tawani yi side parking na blonde hair dinta ta sakosa gefe ta dora beret a side ,
Drivern na kokari tada mota yace ya
Tsaya ,bude gidan baya yayi ya fincikota,
Yafara tafiya ,
Kamar zatayi kuka haka ta fara tafiyan dan a tunaninta bazataje adamawanba,
Itadai fatosh binsu tai da kallo dama tasan za'a rina babu mamaki wani abu tayi masa,
A falo ya chake ta ,
Dagudu mai aikinsu baba hadi tace lapia kuma shuraym ,
Lapia baba babu komai jin haka yasa tace to ta koma tana waigensun,
Kuka jasmine take sosai ,
Kallanta yayi da kyau gown dinma dake jikinta da kadan ta wuce gwiwa,
Jeki cire shegun kayannan kisa masu tsayi sannan wannan yar iskar beret din da kika kifa kamar kafuran France kije maza maza kisa hijab dan banasan ganin shegen blonde hair dinan naki idan kuma ba haka ba zaa barki gidannan daga ke sai baba hadi da masu gadi wallahi kinji na rantse,

Kuka sosai tasa tace wallahi ni hamma banida hijabi ko daya kumani wallahi nayi kyau,
bai ce mata komai ba illa zuba mata ido da yayi yanaso yaga gudun ruwanta ,
Ganinfa za'a iya kin zuwa da ita adamawa ne yasa ta nufi dakinsu ta bude akwatinta ta dauko duguwar rigarta baka tasaka dagaske batada hijab din kamar yarda ta fada dan haka ta janyo dankwalinta mai v ta yafo akai ta daure a wuya ta fita,
Kallo daya yayi mata yace wato bazaki saka hijab dinba ko,
Dawani sudden tsoransa tace wallahi tallahi hamma banida hijab ko guda daya wallahi,
Ganin gaske gaske take yasa yace naji abun kunya kina yar musulmai waike kin fito daga garin kafurai ko,to goge wannan shegen janbakin dake bakinki ko na miki shegen bugu,
Kallansa tayi shekeke dan itafa jitake ta kashe da jan bakinnan ,
Amma dai hamma bani kadai nasaka janbakinnan ba and its a symbol of classic lady,
Juyawa yayi zai fita da sauri ta riko hannunsa tace Allah hamma zan goge kayi hakuri,
Hannu tasa ta goge janbakin tana mai cikeda jin haushinsa tabi bayansa tana matsar kwalla,
Tundaga nesa fatosh da ta gansu ta fahimci abunda yasa ya ja jasmine din,

Har sukaje airport bata sake cewa komai ba dan wani irin haushin shuraym takeji sosai,
Fine girl naga kinfi dazu kyau cewar fuad,
Wani kuka da take rikewa ne ya kufce mata,
Cikeda kulawa abuh yace yarinyana mai ya faru mai aka miki,
Kallan shuraym tayi taga yawani hade rai dan haka tace kawai ina missing baba hadine dana tuna ita kadai muka bari agida badan inasan ganin ardo da dada ba ai dana zauna da ita amma yanzu dai mutafi ,
Dariya sukayi banda shuraym wanda baiga abun dariya a haukanta ba,
40 minutes suka kara a airport din jirginsu ya iso airport din,
Ticket dinta fatosh ta bata seat5b a first class,
Wane Kusa dani hamma fuad kaine,
Kada kai yayi yace aikuwa dai keda hamma shuraym ne,
Saida gabanta ya fadi ganin yayi gaba and itafa  tsakani da Allah seat din kusa da window take so amma koda ta hau jirgin shine zaune a gun ,zama tayi akusa da shi tanamai jin ba dadi,
Hamma shuraym ,
Shiru bai kulataba ganin kamar baijitabane yasa ta sa hannunta tayi tapping masa lap dinsa,
Cire headphones din dake kunnesa yayi ya sauke idanunsa akanta aransa yana adduan lokacin komawanta garinsu yayi yayi ta tafi dan in aka cigaba da haka zai iya mata illa dan mugun duka zaiyyi mata,
Kasa tayi da muryarta kamar bataso na kusa da ita suji mai zatace tace "hammana dan Allah ka bai gurinka mana na zauna saboda kaga nifa indai zan hau jirgi to a seat din window nake zama kabani seat dinka dan Allah na zauna sai ka dawo nawa it won't cause you anything and inda dai zakaje a seat din window nanne zakaje a nawa seat din i just wanna see the view,
And yawwa nace idan zaka tashi din kafun ka zauna ka kaini cockpit mana nasan tunda captain ne kai yanzu maybe kasan wani, na dai kosa na fara shiga cockpit din jirgi kaina tsaye nima,
Maybe idan anyi sacking dinka time din nazama mai taimaka maka adawo da kai sabida i will make a great captain.

You must be very stupid ,
One idan kika sake mun magana saina fasa miki baki,
Two"
Idan har sai kin kalli view ne zaki rayu to ki mutu.
Three.one more pimp from you saina cillaki ta window dan ubanki.

Yarda yace dan ubankin ya shigeta sosai and it was unexpectedly dan haka tace ubana fa kace hamma daddy fa kenan,
Sai wii ta fara hawaye an zagar mata dadddy,
Tsaki yayi ya maida headphones dinsa cikeda kosawa yaje inda zasu ya rabu da wannan illmannered yarinyan ...
Wai ayi sacking dinsa ,
Wanann yarinayn bata da tarbiyya da kunya at all.

Chuchujay✍️

YAR AREWA(THE NORTHERN GIRL)PaidWhere stories live. Discover now