chapter 3

83 9 2
                                    

YAR AREWA (T/N/G)
3⃣

Suna sauka a airport fatosh ta kira fuad wanda already yana airport din ta sanar masa sun sauka,tun kafun ta kashe wayan taga jasmine ta kwasa da gudu tana faman washe baki ,kallan direction din da tayi ta kalla taga fuad ne tsaye ya buda mata hannu yana ta faman mata fara'a fadawa jikinsa tayi tana ihun hammana ,tsaf ya dagata sama yana fadin honey ,
Kin sauka tayi daga jikinsa ,
Gaishar da fatosh yayi yana maida jasmine hannunsa ,
DA faraarta ta amsa tana cewa fuad kabiye katuwar budurwannan kadauketa a hannu,shafa gefen fuskarta yayi yace ai babu komai aunt fatosh ai katuwar budurwar ta hamma fuad ce so babu komai idan hamma fuad ya dauketa ko fine girl dita,
Kada kai tayi tana kara fadada murmushinta wanda yake bayyana dimples dinta mai kyau,
Gaban mota ya bude yasaka ta fatosh ta shiga baya tana girgiza kai tana murmushi,
Tukin motar ya fara yana cema fatosh aunt da abuh yace mun zakuzo nayi tunanin fa zakuje Ohio din nima dai surgery nayi da safen nan shi yasa bansamu zuwa ba amma kowa da kowa sukaje chan din amma kwana biyu zasuyi,
Ai dama kam ku surgeons ai baku shiryawa surgery duk lokacin da ya kama sai anyi ne ba daman tafiya kam musamman surgeon kamar kai wanda yasan mai yake "cewar fatosh,
Duk hirar da suke yi idanun jasmine yana kan adam apple dinsa yarda yake kaiwa da dawowa,

"Hamma fuad ka kara kyau wallahi ,kamun kyau sosai yau dinnan i like you,
and I want to be your wife .
Maganar jasmine ta karade kunnuwasu lokaci guda .
Sakin baki fatosh tayi tace jasmine "
Juyowa tayi ta kalleta tace menene aunt last time nace i don't like hamma shuraym kina fada yanzu kuma i said I like hamma fuad still zakiyi scolding dina and I mean it I want to marry Hamma fuad He's kind and handsome unlike hamma shuraym ,
Fatosh zata sake magana fuad wanda maganar jasmine din tayi masa dadi har zuciya yace oh aunt please ki rabu da matana haka,
Murmushi yayi mata mai kyau ya shafa cheeks dinta yace kar ki damu yar kanwata matar hamma fuad ,
DA murnarta ta kalli fatosh tace kingani aunt fatosh kar ki shiga tsakanina da hamma fuad he also like me,
Ita dai fatosh kunyar abunda jasmine take ne fal ranta,
In ma banda yaro da abunsa sai nan gaba idan ta tuna itama ya bata kunya,
Haka yayi ta tsokanar jasmine yana janta da hira ita kuma tanata sakar baki tana basu labarai iri iri"

A kwana biyu da sukayi a gidan jasmine ta kara shiga ran fuad dan a ranar da yangida ma zasu dawo tare da ita ya tafi babban asibitinsa na FSADAUKI HOSPITAL "
Koda suka dawo fatosh suka tarar a part din da abuh yayi domin yanuwansa,
Tana zaune tana yanke kumba taji an daneta ,
Kada kai tayi tace Jasmine kina kallan nail cutter ne a hannuna amma kika dane ni haka,
A tare suka juyo gabanta harda akila wadda ke tsaye bayan abida da ta dane fatosh suka ce aunt ina jasmine,
Aje abun yanke farcen tayi tace ashe yaranane ,
Fadawa jikinta sukayi suna gaisheta cikeda murna,
Kara tambayarta abida tayi Jasmine"
Tashi tayi tana cewa zillaziya ai tabi fuad asibiti amma yakirani yace suna hanya yanzu, kuzo muje na gaisa da mutan gidan,
A tare suka nufi part din hajiya ziyada,
A falo ta tarar da ita tana mitan yarda su akila suka aje akwatinansu a gun,
Tanajin sallamar fatosh ta aje kayan ta juya da fara'arta tace kai fatosh maimakon ki bari nazo da kaina na gaishe ki wallahi yanzu nake shirin zuwa din fitowana kenan nazo naga ashe ko kayansu nan basu daukeba,
Zama fatosh tayi tana cewa aikuwa dai yarana suna daukin ganina ke kuwa ai an kwana biyu ,
Zama itama tayi suka gaisa cikin mutunci ,suna dan taba hirane abuh ya shigo tareda shuraym,
"Fatosh" sannunku da zuwa mun barku gida kwana biyu ku kadai ko'

cikeda girmamawa da kunya tace "aikuwa hamma babu komai mun sameku lapia?
Alhamdulilah yabata amsa yana zama kusa da matarshi,
Kasan kujerar da fatosh take handsome shuraym ya zauna yana gaisheta kansa kasa,
Dariya irin ta manya Abuh yayi yace kai kam banga yaushe zaka daina jin kunyar fatosh ba kodai surukuntaka zakuyi ,
Kara kasa yayi da kai yana murmushi ita kuma tace nima dai hamma narasa wannan kunya tawa da matukin jirgi yake yi haka ,to
Ina tayaka murna yau cikin family din ardo mua'alim sadauki mun samu babban matukin jirgi wannan abun farin cikine Allah ubangiji yasaka maka hannu ka hau lapia ka sauka lapia,Allah ya kwabe dukkan wani tsautsayi dake cikin aikin,.

Amin suka amsa baki daya"

Sauran yar kanwarka jasmine itama dai burinta kenan ni tun tana bani dariya ma na hakura nace Allah ya taimaka ,.

A babbar magana aikuwa indai tanaso zata iya and ba discouraging dita yakamata anayi ba arinka bata karfin gwiwa ,kajifa shuraym yar kanwar taka, sai a bata guide in lokaci yayi ko mamansu? "
Cikin jin dadi hajiya ziyada tace aikuwa dai abuh ni yar tawa ma tana inane fatosh"

Wallahi tabi fuad asibiti and dazu da yakirani yace mun suna hanya"

Tashi shuraym yayi dan ya kosa da jin wannan fitinanniyar yarinyar in banda rawar kai uban me zataje yi gurin aikin fuad ,kodayake shi ya fita,
Abuh Bari naje nadan watsa ruwa,
Kada kai abuh yayi yace yakamata ,kaje yau zamuje family dinner and jibi zamuje adamawa wannan karan, ardo yace an masa laipi a gama karatun fuad baaje chan ba sai daga baya kaga kuwa dole wannan karan aje kasan halin ardo.
Aikuwa dai yanzu zai tashi hankalin kowa fatosh ta fada tana murmushi"

Fita shuraym yayi aransa bayasan zuwa adamawan nan amma yasan halin wannan kinibabban tsohon yanzu zai tashi hankalin jama'a,
Yana shiga dakinsa ya fara rage kayan jikinsa ,
Chocolate skin dinsane ya bayyana ,
Wasu abs dinsa masu daukan hankali suka bayyana,
Towel ya jawo ya daura a kugunsa sannan ya kara kwalkwale gemunsa wanda yake sol baka ganin digon gashi ko kadan sannan yafada wanka,
Shuraym saurayine mai kyau da kwarjini ,
Bazaka kirasa fari ba kuma baza kace masa baki ba duk gidan shine mai wannan kalar fatar sabanin sauran duk fararene irin na fulani,
Idanusa irin gajiyayyunan ne da ake kira sexy eyes sai hancinsa bamai yawan tsayi ba,
Lips dinsa full lips ne sai yalwar dark gira ,abu dayane yake hadasa da mutane wato miskilancinsa wanda mutane dayawa suke kira da girman kai,shi mutum ne ba mai tsoma hancinsa cikin alamuran mutane ba wanda hakan ya dauko ne gurin mahaifiyar abuh kakarsa kenan,
Amma ardo kuwa gidan radio sai dai nashi surutun da fasaha a cikinsa dan duk mai sauraransa zai gane hakan sannan shi mutum ne mai yawan barkwanci".
***.
Koda fuad suka iso gida da zumudi jasmine tayi hanyar gida dan ba domin kar tayi guduba tasa su Abuh suce tama yaya fuad yarinya ba da gudu zatasa dan ranar fatosh na kallan wani indian film taga same scene na budurwan da tashiga da gudu ta tarar da in laws dinta wanda hakan yasa aka fasa auren so idan ta duba tanasan zama matar hamma fuad which makes su abuh in laws dinta dan haka da nutsuwa ta shiga gidan,
Kasa rike kanta tayi da tayi arba da su abida da akila sai little mimi dake zaune tana shan cornflakes,
Ihunsu suka gama duk bata kulada su abuh ba saida yace yarinyan abu hala bakiga abu da mama ba ,
A nutse ta gaishesu tana sim sim da kai,.

DA daddare suka fita baki dayansu dinner a lè ricoo babban fancy restaurant na wane DA wane,
KO inda jasmine take shuraym bai kallaba itama tunda ta kallesa sau daya taga bai kalli inda takeba saita sharesa ta cigaba da hira dasu akeela amma tasa a ranta zataje yabata labarin yarda zaka zama pilot daga baya cos yarda yake wani shan kamshi kawai birgeta yake God she cant wait to be a pilot ,
sai goma suka koma gida dan haka kowa ya wuce dakinsa ya kwanta da zummar washe gari zasuwuce Adamawa,
Dan tsabar zumudi tun da Jasmine da twins suka tashi sallar asuba basu komaba , suna sallah sukayi wanka ,
Har gari ya waye basu komaba suna hirar school ,
Kowa ya fito dan karyawa amma babu shuraym,
Abuh ne yace wai ina captain din mune ko har yanzu habit din rashin breakfast da wuri yana nan,
Aikuwa Abuh yana nan fa cewan fuad"

Aje cup jasmine tayi tace hamma fuad ina  pink teddy na na barsa motanka,
Dafe goshi yayi yace kash namanta ban dauko miki ba saida na koma zan dauko file naganta a mota amma na kai miki daki na yana kan bed dina je ki dauko tanan na miki combing hair dinta"
Dariya sukayi baki daya jin karshen maganar fuad,

Kaitsaye part dinsu fuad ta tafi and idan bata manta ba dakin farko shine nasa na biyun kuma bata mantawa nanne tasha dan banzan duka gun shuraym ,
Kai tsaye ta murda handle din tasakai ta shiga,
A zaune ta tarar da teddy din ,karasawa tayi tana murnar ganin teddy dinnata daitace favorite teddy din da daddy yabata as birthday gift personally dakansa,
Daukan teddy dintayi tayi kissing nata akan hanci,
Juyawar da zatayi shikuma yana fitowa daga bathroom dagashi sai three quarter baki,
Kallansa tayi from head to toe Saannan takara maida idanunta kan cikinsa inda packs dinsa suke,
Sakin teddy din tayi tace God is great" abs  "
Karasawa tayi inda yake tasa hannnu ta taba abs din tace Hamma abs omg irin abs din Can na early bird dana gani mummy na kalla i love abs..

Chu chu jay✍️

YAR AREWA(THE NORTHERN GIRL)PaidWhere stories live. Discover now