52

162 18 6
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

*(52)*
Yagana na tsaye na sababi Zulai ta faɗo parlon da sauri, tambayarta ta ke lapia amma ko sauraronta bata yi ba, salati kawai ta ke zabgawa tana kambaba zancen da ba shikenan ba. Zulai ta juya ga su Basma da ke zaune kan kujera hankulansu na kan tv su na kallo, ta kira sunan Sadiya, ta juyo a sanda ta ke kai mango baki tana sha. "wannan ai shashashanci ne Sadiya, kuna jin Yagana na salati ba ku tashi kuga meke faruwa da ita ba". kamar Sadiya ba zata ce komai ba can ta nisa sannan tace. "Inna ki yiwa Allah ki ƙyale wannan rikitacciyar tsohuwar". lokacin Yagana ta juyo tace da Sadiyan. "wannan kuma da wadda ke tsaye kusa da ni kike ba ni ba". Sadiya ta ƙara kaiwa wuya amma bata ce mata komai ba. Zulai ta maida hankalinta ga Yagana da ke faɗin,"ki kalle min nan fa Uwar Amadu, wai yaron nan Kabiru daga yi masa halacci nace ya shiga su ci abinci da matarsa shikenan sai ya tafi aikata abunda ba haka mu kai da shi ba". Zulai tace,"me ya faru Yagana?". Yagana tayi guntun tsaki sannan tace,"kema Zulai wataran dai akwai ki da duhun kai...matsa ki ban wuri nan kiga na shiga na fito da shi". sai a yanzu Zulai ta fuskaci inda maganar Yagana ta dosa, dan haka ta dakatar da ita daga shiga ɗakin tana cewa,"yi haƙuri Yagana". "nayi haƙuri kamar ya Uwar Amadu...ba ki lura da ta'asa ake aikawa ba akan gadona ba ne". "bai zama lallai hakan ba Yagana". "ke kinji uban ihun da yarinyar nan ta kurma kuwa da kike faɗar wai ba farketa yay ba...ta ina za ki sa ni, haka fa yaron can Lamiɗo yay mana da bikinsa, daga shiga ɗaki a barsa ya keɓe da matarsa sai fito mana yay kayan jikinsa duk sun ɓaci da dilkar da ake shafa mata, to yanzu tsakani da Allah ki faɗa min a wanne irin yanayi Kabiru zai fito, kai kai ni Rakiya Manniru ina ganin abinda ya isheni bai ishi Allah na ba....akan gadona, kan gadona fa akai kwanciyar aure, wannan ɗiban alhaki da me yay kama". tayi zancen tana neman kujera ta zauna haɗe da rafka tagumi. Sadiya taja dogon tsaki tace,"wallah Yagana kayan haushinki da yawa yake...ta ya mutumin da baifi minti biyar da shiga ɗaki ba za ki ce ya farke matarsa?, sai kace wanda zai yi fyaɗe ko kuma wanda aka aura masa wacce ba ya so...dan Allah ki rage zuzuta abu". Yagana dai bata ce ma ta kanzil ba tayi kunnen uwar shegu da ita.
ni kuwa tunda Ya Kabir ya sakar min baki daga matsar da yay masa nake aikin matsar hawaye, naja hancina da ya cika da majina ina ƙara kumbura da irin tunanin sharrin da zan ƙala masa wurin Daddy a raba wannan auren. yasa hannu ya gyarani akan cinyarsa da nake a zaune, zaman da yay min ta dole dan kawai zai yi forcing ɗina naci abinci. ya kawo spoon bakina wanda ya ɗebo eba da ya sha miyan egusi busashshen kifi. "oya haa". na kasa yi masa garda saboda yanda naga ya ɓata rai, irin ɓacin ran da tun tasowarmu tare ban taɓa gani a fuskarsa ba, haka ya dinƙa feeding nawa har sai da ya tabbatar da cikina ya cika kafin ya ƙyaleni.
kuma abunda nake ta tsoro tun shigowarsa shi ya faru, idonsa ya ƙyalla kan wedding card gift ɗin da ke aje gefen pillow ɗin da na ɓoye. a ɗazu da ina sallar isha'i Ya Ahmad ya shigo, lokacin tayarwata kenan dan haka bai iya zaman jiran na idar ba ya sunkuya har ƙasa ya aje min card ɗin sannan ya juya ya fita, ya fita ya barni da bugun zuciyar da har yanzu bai tsaya ba, kuma harga Allah a lokacin ko da ace nayi sallama ne ba zan iya ɗaga kai na dube shi ba balle na iya yi masa magana, dan ban san da me zance masa ba.
"wancan card ɗin fa?". tambayar Ya Kabir ta katse min gajeran tunanin da nake, ƙirjina ya fara yin fat-fat, ban san me aka rubuta ajikin card ɗin ba, dan tunda na ɗauko aje shi kawai nayi da zummar idan zan kwanta zan karanta, abu ɗaya kawai da nake tunani nasan ba zai wuce marriage wish ba. ban san me zance masa dan haka nayi tsilli tsilli da idanuwa bakina a gimtse. hannunsa na zagayowa kan cikina ya ƙara tambayata, da irin sautin da ayanzu na gagara yin shiru na amsa masa da. "Card ne". "ehh ai nasan card ɗin ne...na mene shi ne abunda na ke tambaya". na haɗiye wani guntun yawu sannan nace. "nima ban sa ni ba". na amsa mishi a ɗarɗarce saboda yanda yake tambayar cike da tuhuma, cikin kausashshiyar muryarsa yace,"tashi ki ɗauko min". nayi ƙumm na kasa tashi, a tsawace ya ƙara cewa,"nace ki tashi ki ɗauko min ko". muryana a ƙasa nace,"to ai ka matse ƙafan nawa". sai a yanzu ma ya tuna da cewar ƙafafuna na tsakanin cinyarsa ne da ya maƙalesu, ya ware ƙafar na miƙe kamar munafuka naje na ɗauko, abunda ya ban mamaki ina miƙa masa kallo ɗaya yaywa card ɗin sannan ya ɗago ya dubeni fuska babu annuri yace,"me ya kawo Ahmad wurinki?". sai nayi kaman ban gane me yake nufi ba. "wai ba za ki bar min shiru ba idan ina tambayarki". "to ai kai ne da wata negative tambaya, me zai kawo Ya Ahmad ɗakin nan bayan yasan ni matar wani ce". a harzuƙe cikin tsananin ɓacin rai yace,"zan ɗaukeki da mari wallah, ni za ki rainawa hankali...ƙamshin turarensa da naji shigowata naki ne? ko kuma wannan hand writing ɗin naki ne?...kin faɗa uban me ya kawo shi wurinki ko sai na miƙe kinga ainihin tsayina tukunna". jikina na shaking nace,"wallah ni ban san me yazo yi ba, kawai ya shigo ya aje min wannan ya fita amma Allah ka yarda da ni ko kallonsa ban ba". ya galla min wani banzan kallo kamin yasa hannu ya keta card ɗin, sai da yayi gutsi gutsi da shi tukunna yay watsi da su gefe sai wani irin huci yake. sannan ya miƙe tsaye ya tsaya a tsakiyar kaina yana cewa,"daga yau ko wuta Ahmad ya aje kikai gigin ɗauketa gudun karta ƙona ki Maryam abin da zan miki sai kin ƙwammaci mutuwa ki kai...stupid kawai". yay maganar kamar zai rufeni da duka sannan ya bar ɗakin fuuuu kawa guguwa. ya fita ina jiyo Yagana na cewa da shi,"Ta faru ta ƙare, da gasken dai lissafin daga ɗakina zai soma...ai shikenan Kabiru kanka ka yiwa". abinda yasa ta faɗa masa haka ganin yana gyara zaman belt ɗin da ke jikinsa ne, dan da kamar zai cire belt ɗin ne ya dukeni sai kuma yay saurin ficewa.
na miƙe ƙafafuna a sanyaye na shiga toilet ɗin Yagana na wanko fuskata na dawo na kwanta ko cire kayan jikina banyi ba, bacci yay ƙaura daga idona tunda na kwanta, tunaninsa da tunanin abunda yay min kawai na ke, sai ƙwafa nake saki a raina. haka har Yagana ta shigo ɗakin, ina jinta sanda ta kunna fitila ta kashe tana faɗin,"ni Rakiya Allah yasa bai jiwa ƴar mutane ciwo ba...dan yanda naga ya fito fuskar nan kamar hadarin da ya haɗe a gabas nasan bata daɗin rai akai ba, ni dai Kabiru bai kyautan ba, dan da ya san amana na karɓa ba zai aikata hakan ba". ta hayo gadon tana taɓa jikina, cikin fushi na bige hannun nata. ta hau surutanta har taga ji kuma ta dawo tana yabona da yabon Ya Kabir, har da kukanta na zata rabu da shi gobe, wai tasan yanda yay auren nan in ya tafi sai ranar da ta ganshi...ina kallonta tana haɗa wasu kayansa da ta ke faɗin ta wanke masa tasa an goge, tana haɗawa kuma tana goge hawaye, duk sai naji ta bani tausayi, na sauko na ɗora kaina saman cinyarta, nan ta shiga yi min kalar nata nasihar da faɗan duk akan zamantakewar aure.

****ɓangaren Kabir kuwa yana fita direct ya zagaya ta ƙofar baya, inda ɗakinsu Nawwara yake, dama ƙofa biyu ce, ko ka shiga ta kitchen ɗin Yagana ko kabi ta baya wajen flowers ɗin gidan. da farko da ya shiga ɗakin bai lura da kowa ba dan ko sallama bai yi ba bare a amsa yasan da wani a ɗakin, sai Iya ce da ta kula da shi ta yunƙura ta miƙe daga kwancen da ta ke tana gaishe shi. ya shafi bayan wuyansa ya amsa sannan ya tambayeta ina Nawwara. tace da shi ta shiga wanka ne da yake yau ta wuni da zazzaɓi sai yanzu taji daɗin jikinta. sai ya juya ya fice bayan yace da ita,"iya idan ta fito kice ta sameni a ɗakina". ta amsa mishi da "to" tana ƙara yi masa Allah sanya alkhairi dan jiya gaba ɗaya ma bata ganshi a gidan ba.
bai yi minti goma sha biyar da shiga ɗakinsa ba yaji knocking ƙofa. ya ƙarasa saka button na rigarsa sannan ya bata izinin shigowa ɗakin. ta sanyo siraran ƙafafunta ciki bakinta ɗauke da sallama kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta. "Ya Kabir gani". ba tare da ya dubeta ba yace,"na ganki, idan kin gaji da tsayuwar kya iya hawa kaina ki tsaya". daga yanda yay maganar tasan ransa babu daɗi, dan da sauri ta ɗago ta dube shi, kamin nan ta durƙushe a wurin tana fuskantarsa. "ɗauki wannan abincin ki cinye". ta buɗi baki zata yi magana ya dakatar da ita da cewa,"bana son musu". saboda haka ba dan taso ba ta shiga cin abincin, bata wani ci da yawa ba tace da shi ta ƙoshi. sannan ya ƙara cewa da ita,"ɓalli wannan maganin kisha". ta kalli inda wani ƙaramin box yake ta ɗauki maganin da ya mata nuni da shi ta ɓalla tasha, ya taso yace ta miƙe yay mata allura, lokaci guda ta shiga matse hawayen da ke shirin sakko mata, tana cewa da shi. "Ya Kabir na warke wallah". bai bi ta kanta ba ya janyota jikinsa ya tsira ma ta allurar a sanda ta ke ruƙunƙume shi tana sakin ɗan ƙaramin kuka. sanin cewar ba iya lailayawa zatayi ba ya lailaya mata sosai kan muryarsa ta fito a sanyaye yana cewa. "kin gama haɗa kayan naki?". ta ɗaga masa kai alamar ehhh. ya sauke numfashi sannan yace,"ɗazu naje wurin Baba". sai tayi saurin zamewa daga jikinsa tana ɗago kai da ido ta kalle shi. shima ya kalli ƙwayar idonta da ta ciko da hawaye tukunna yace,"ba na son kuka". ya faɗa yana saka hannu ya goge ma ta su da suka sami damar sakkowa.
"munyi magamar Kabirun da kika ce an ba ki, yace sun neme shi tunda jimawa kuma an tabbatar musu da ya rasu, basu faɗa miki ba ne kawai...ashe almajirin Ummanki ne da yay musu halacci, kuma shi ya nuna yana biɗar aurenki tun kina tsumma...na faɗawa Baba cewar zan tafi da ke can ƙasar da nake zaune za ki ci gaba da karatunki acan...na basu haƙuri na ƙurewar lokaci da aka samu wurin sanar da su, amma nayi musu alƙawarin ko shekara ba za kiyi ba zan kawo ki kona sa akawoki ki gaida su...hakan yayi miki?". ta ɗaga kai tana cewa,"na gode da kulawanka gareni". sai taji yasa yatsunsa ya ɗago haɓarta yana cewa. "idan waɗan nan ƙafafun ba su daina rawa ba idan suka ganni next time ɓallasu zanyi, kin san dai ba zasu yi wuyar ɓallewa ba yanda suke kamar sillan karan nan". bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. "kin dai gama shirya komai ko?". "ehh na gama". "kar ki haɗa da tsaffin kayanki, na saya maki wasu su na wurin tailor sai zamu wuce zamu tsaya a karɓa". "tom na gode, Allah ya ƙara arziƙi". "amin amin..kije ki kwanta Allah ya ƙara sauƙi...amma ki tabbata ban fito ina cewa Nawwara fito ba, ko kuma ki fito kina ce min kinyi mantuwa". "insha'Allahu". daga haka tayi masa sallama ta fita yana bin bayan da kallo, zuciyarsa na lissafa masa wani abu da yake ganin da wuya ya yiwu...amma yana roƙon Allah yasa hakan ta kasance.

*Plsss Comment and vote*.

SIRRIN ƁOYE CompleteWhere stories live. Discover now