43

189 20 5
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._

*(43)*
*4Months Letter.*
*Qatar University, Doha.*
"Maryam Mukhtar Afafa". sautin kiran sunan nawa ya fito ta cikin hall ɗin daga can sama, daga bakin Shamsiyya Sani, sanin cewar kiran nata bana arziƙi bane yasa ban tsaya sauraronta ba, naci gaba da tafiya abina, tafiyar da ka kalla yanda nake yinta zaka san nayi matuƙar gajiya.
a hankali na ke saukowa daga steps ɗin bakin hall ɗin namu, hannuna na dama riƙe da matsakaiciyar jaka kasancewar yau ban lodo handouts ba. kamin na kai ga ƙarasa sauka daga step na ƙarshe na zare space glass ɗin da ke kewaye da rabin fuskata, sannan na zura hannun haguna cikin aljihun pink abayar da ke jikina wadda su Shamsiyya su kai ta santinta su na faɗin rigar ta dace da ƙirar jikina.
a bakin hall na tsaya ina jiran fitowar Shamsiyya da Nusaiba amma shiru shiru ba su fito ba, naja ƙaramin tsoki na takaici sannan naci gaba da takuna cikin natsuwa har san da na taka kan titin cikin makaranta, yanda nake ta faman ɓata fuska zaka ce ko banda lafiya ne, haka ina ji wayata na ringing amma naƙi ɗagawa duk da na san mutumin da kiran nasa ke shigowa cikin wayar me muhimmanci ne a gare ni, kamar yanda na banbanta ringing ɗinsa da na saura.
"Ya Ahmad". angona wanda za'a ɗaura min aure da shi nan da sati biyu masu zuwa. tafiyar da nayi akan titin gaba ɗayar bai fi taku 8 ba naja na tsaya, tsayawar tawa tai daidai da tsayawar motar da ta zo ɗaukana a gabana.
a cikin yaren larabcin da a yanzu ya maye harshena nace da driver,"me yasa kayi late yau?". "kiyi haƙuri ranki ya daɗe, na kai Alhassan library ne, bai kammala da wuri ba ne shi yasa, kuma na yita kiran wayanki ba ki ɗaga ba". "yana ina?". na tambaye shi a sa'ilin da nake duban cikin motar ban ganshi ba. "yanzu zai ƙaraso ya tsaya da abokansa ne su na gaisawa, hangoki da yay ne yace na ƙaraso na ɗauke ki...ga ma shinan naga ya taho". ya ƙarashe zancen yana min nuni da direction ɗin da Alhassan ke tahowa wanda ke gab da iskomu.
"menene? ba ki da lafiya? wani abun aka maki?". tambayoyin da Alhassan ke jera min kenan ya ƙaraso yana ɗora hannunsa saman goshina, yana mai tambayar cike da nuna damuwa da kulawa. na kwaɓe fuska ina karayar da kai nace,"na gaji ne". "to sannu". ya faɗa yana amsar jakar hannuna, sannan driver ya buɗe mana motar muka shiga, ko da shigarmu ban iya zama ba sai kwantawa da nayi na ɗora kaina saman cinyarsa.
"Mami ta tafi?". na tambayeshi a amon muryata na fitowa a hankali. "har ta shirya sai kuma tace ta fasa wai ba yanzu ba". lokaci guda naji wani abu ya tsarga min a zuciyata, wani abu da ya haddasa jin daɗi a ƙasan ruhina. ko kaɗan bana son nesanta da ita, shi yasa ko da na taho karatu wata huɗun nan da nayi babu ita kusa da ni sai nake jina tamkar ina rayuwa ne a cikin kurkuku, irin kurkukun nan da ke da duhun ɗaki da kuma ganiyar azabtar da me laifi.
driver ya tsayar da motar a rumfar wajen da aka tanada dan ajiye motoci, motocin da ake fita da Ammi kaɗai a cikinsu, sai ni da na zama ƴar gidan yanzu, ya fito yazo ya buɗe mana ƙofa, kamin na zuro siraran ƙafafuwana da suke ɗauke da gajiya waje, Alhassan ya kama hannun mu kai cikin gida. sanin cewar a irin wannan lokacin Ammi na tare da Abbi ne, yasa bamu biya ta parlon da ta ke zama ba. muka wuce kai tsaye zuwa ciki inda sauran ɗakunan ɓangarenta su ke wanda acikinsu ne aka fitar min da babban ɗaki guda aka bani tun zuwana karatu ƙasar, dan lokacin da Ummi tayi aure acan saudiya wurinta na koma da zama, sai ma lokacin da za'a saka ranar biki ne naje can abuja inda Mami take na zauna na tsawon sati biyu daga abuja kuma na wuto Qatar, ko su Yagana banjewa sallama ba a lokacin.
"Subhanallah, me ya faru da ita?". muka jiyo muryar Ammi da bamu tsammaci gani ba tana tambayar, na kalleta da gajiyayyun idanuwana ina ƙara kwaɓe fuska nace,"Ammi yau na gaji ne". sai ta miƙa jakar da ke hannunta wa Kuyangar da ke bayanta, sannan tayi saurin tahowa gareni ta riƙoni zuwa jikinta. Alhassan kuma ya wuce ɗakina kai min jakata, akan cushion ɗin parlon muka zauna Ammi ta shiga warware min vail ɗin da ke kewaye da fuskata tana yi min sannu.
ta kwantar da kaina bisa kafaɗarta tana jera min wata sannun, sannun da bata da adadi tun daga lokacin da ta riƙoni. cushion ɗin da muke zaune na fuskantar steps ɗin da su ke cikin parlon, ta nan na jiyo takun tafiyar takalmi ƙwaf-ƙwaf na sakkowa daga upstairs ɗin, kamin wucewar sakanni biyu kuma naga ɓulluwar Mamina, tana sanye ne da butter milk ɗin abaya wadda tasha stones a jikinta, ta kuma matuƙar amsar kyawun nata, ta ƙarasa saukowa tana sauya hannu na riƙe wayar da ke kare a kunnenta zuwa ɗayan hannun da ke riƙe da ƴar ƙaramar jakarta haka ta ƙaraso wajen cushion, ta cikin wayar da ke kare a kunnen nata ta ke faɗin.
"a'a i just want to stay more for a while". tayi shiru kamin ta ƙara magana,"oak hakan ma Yayi Your Excellency. muyi waya letter". daga haka ta katse wayan a yayinda ta ke zama acikin ɗaya daga cushions din. "sannu da hutawa Ammi". "yauwa". lokaci guda idona ya cika da tarin ruwan hawayen da basu kai ga sakkowa ba, muryana na rawa nace da ita,"Mami sannu da gida". "yauwa sannu". ta faɗa ba tare d ta nuna halin in kula a gareni ba, wanda hakan ke damuna sosai, kuma da dukkan alamu bata gane ina cutuwa da wannan shariyar tata ba, haka ko time ɗin da na zauna a abuja zaman da mu kai da ita tamkar wani zaman kishiyoyin da basa jituwa ko kuma zaman sirikan da, ƙwaƙwƙwarar magana bama yi da ita, sai dai na bita da ido, nayi tunani kala daban daban ko wani laifin na mata amma na gagara gano komai, kuma taƙi bani damar da zan zauna da ita naji laifina na bata haƙuri.
nasa hannu na mayar da hawayen da ke neman sakko min, kamin muryarta ta ƙara fito min da faɗin,"Daddynku na gaidaki, wai bai sameki a waya ba". tayi maganar idonta na kan wayar da ta ke shafawa. "mun yi lectures da yawa ne yau shi ne nasata a silent". bata ƙara cewa komai ba sai Ammi da ke cewa,"ina ga ki kira doctor ya duba Maryam, ban yarda da yanayinta na yau ba, kanta ma naji da zafi". nayi saurin ce da Ammi,"Ammi lafiya fa nake wallah, kawai stress ɗin yau ne". "eh duk da haka dai yazo ya ba ki wani maganin kisha...tashi kije kiyi wanka ki ɗan huta kamin ya ƙaraso".
Alhassan da ya ƙaraso wajen yana zama kusa da Mami ya ɗora hannunsa a bayan wuyana ya dafa ni ya kalleni yana cewa,"zama ki rabu da wannan son jikinne, kwana nawa ya rage". na turo baki gaba ina hararsa. sai yasa hannu ya ɗago fuskar Mami yana ce mata,"kalla yanda ƴarki ke hararata, to ki faɗa mata na rigata shaƙar iskar duniya, ta kiyayeni kafin taji ajikinta". Mami ta murmusa kuncinta ba tare da ta ce masa komai ba ta maida kanta kan wayar. Ammi tace da shi,"shegen son girma kaman gyaute...kai yanzuma aka ce ka daketa sai ka taɓata?". ina siririyar dariya nace,"rabu da shi Ammi, ai yanzu ko Bro Almustapha ba zai ɗaga hannu akaina ba, kasan kenan kuwa na girmi gaban dukanka". sai ya jijjiga kai bai ce komai ba, sannan ya sumbaci Mami a kumatunta ya miƙe tsaye yasa hannu a cikin aljihun wandon suite ɗin da ke jikinsa, ya dubi Ammi yana ce mata,"mijinki ne fa yace na kira masa ke, kiyi sauri sauri kije fita zamu yi". Ammi ta kai masa hannu ya kauce yana dariya. "kai ni wai yaushe ma zaka koma inda kafi wayo ne, na gaji da ganinka ina faɗa maka". yana nufar hanyar fita ya nuna ni da baki yace,"sai anyi bikin wannan ƴar zan koma, nima na gaji da ganinta saboda tana shigar min cikin al'amura".
ko da na shiga wanka na jima acikin bathtub cikin ruwan zafi kafin na fito, dan sai da na tabbatar ruwan zafin ya ratsa ilahirin jikina ta yanda gajiyar zata yi saurin sakata, ina tunawa da karatun test ɗin da nake da ita gobe.
na shirya cikin wata riga armless na zauna a dining ɗin da yake acikin ɗakin nawa na shiga zuba abinci. kuma fara cina kenan wayar Sweety ta shigo cikin tawa, na daɗa kallon sunan Ya Ahmad ɗin da ke yawo akan wayar fuskana ɗauke da tarin murmushi na jin daɗi, ban ɗaga ba sai da kiran yazo gab da yankewa tukunna.
ajiyar zuciyarsa na fara juyowa a kunnena kafin kiran sunana ya fito daga bakinsa. "me kyauna". laɓɓana suka tale da kyakykyawan murmushi na amsa da cewar,"na'am Yaya nah". murnushinsa mai sauti ya fito yana cewa,"me kyauna yau nayi kewanki da yawa, duk kinsa na shiga damuwa da rashin jinki". cikin sigar lallashi da ban haƙuri nace da shi,"sorry Yaya Nah, wallah yau munyi busy ne da yawa a school, baka kalla ba ma duk na gaji, jikina sai ciwo yake min". na faɗa ina shagwaɓe murya da fuska kaman ina gabansa ne. muryarsa ta fito cikin tausaya min da faɗin,"ayyah sannu Me Kyau nah, sannu kinji, ina ma ace munyi aure da na kawar maki da dukkan gajiyan da ke tare da ke...kinci abinci?". na kaɗa kai kaman yana ganina ba tare da na amsa da baki ba, kuma shi ma kaman yaga hakan sai yace,"to please ki samu kici abinci sai ki kwanta ki huta, kiyi bacci mai yawa please". nace da shi,"tom Swty". "albishirinki". nayi saurin amsawa da,"goro". "tomorrow by now insha'Allah ina tare da ke, zanzo na ganki me kyau nah, na gaji da rashinki a kusa da ni, wannan 2weeks ɗin da ya rage ji nake kamar shekara biyu ce nan gaba". na doka wani tsallen murna da jin daɗi ina faɗin,"Allah ya kaimu goben, Allah ya kawo min kai lafiya...Allah nima Yaya kewanka na ke sosai, wataran har sai naji kaman nayi kuka". duk da ba kallonsa nake ba a lokacin amma nasan ya kaɗa kai kafin yace,"a'a kar ki kuka plss, kinga hawayenki masu tsada ne, bana so ake zubar min da su anyhow, duk da cewan akaina ne za'ayi". na gyaɗa kai kawai, da haka muka ci gaba da hiranmu ta masoya, haka mu kai ta hiran ina cin abinci har naci da yawa ba tare da na sani ba, gaba ɗaya shauƙin sonsa daɗa tsarga min yake yi, Ya Ahmad ɗina bai yarda da na ƙoshi ba sai da muka yi vedio call ya kalleni sosai sannan yace na haska masa cikina tukunna ya gyaɗa kai yace na yarda, tun da ga cikin nan ya zama ƙato kaman nasa, saura bacci kuma, shi ma kar a tashi sai na tashi me kyau da kaina.
a cikin baccin da na kwashi mintuna ashirin ina yi na jiyo daddaɗan ƙamshin turaren Mamina ya karaɗe min cikin hanci da cikin kaina, na buɗe murfin idona a hankali ina dubanta, tana tsaye bakin dressing mirrow ɗina tana maƙala sarƙata a wuyanta, sai nayi murmushi kamin na tashi zaune na dubeta ta cikin madubin da ƙwayar idonta ke kallona ta cikinsa. nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsuna nace,"Ummi ce ta saya min". murmushinta me ƙarfin sauti ya fito kafin tace,"na sa ni ƴar gidan Mami, aro za'a bani please". sai na ɗago kaina ina dubanta ta cikin madubin kamar yanda ta ke dubana nace,"duk yawan sarƙoƙinki sai kin ɓige ata aro Mamin Alhassan, wannan fa me ƙaramin kuɗi ce ba dai-dai da sawarki ba ce". ƙwayar idonta ƙyam akaina, talewar da leɓenta yay da murmushi tun ɗazu har yanzu tace,"na sa ni ƴar gidan Ummi, yau ɗin banjin saka nawan ne, na aro na keso, na aron ma wannan, ko ba za'a bani bane?". na ɗauke idona daga ƙwayar idonta na kaishi ƙasa sannan nace,"kar ki taɓa min abina, ki aje min ban ba ki izini ba". ba kallonta nake ba, amma ina jin san da ta zare sarƙan daga wuyan nata ta buɗe akwatunta ta saka, sannan tace,"kiyi haƙuri na taɓa maki kaya ba tare da neman izininki ba, ba zan ƙara ba insha'Allahu". na ɗago fuskata da tayi shaɓe-shaɓe da hawaye cikin ƙanƙanin lokaci, na kalla har ta kai bakin ƙofa zata buɗe ta fice daga ɗakin, sai na maida kaina ƙasa nasa tafukan hannuna na rufe fuskata, kuka ya kuma ƙwace min.
sai naji tausassun hannunta akan nawan su na ƙoƙarin buɗe fuskar da na rufe, daga nan kuma ta janyoni jikinta gaba ɗaya ta rungumeni tsam wanda har ina iya jiyo bugun zuciyar da ke harbawa a ƙirjinta, a hankali ta ke shafa gyararriyar sumar kaina da ta sha gyara, bata hanani kukan da nake ba har sai da na gaji dan kaina na tsaya, na tsayar da kukan a sa'ilin da na shiga mata magana cikin shashsheƙar kuka.
"Mamina...". ban iya cewa komai ba wani sabon kukan ya kuma zuwar min. sai naji ta sauke ajiyar zuciya a hankali kamin ta fara magana. "na sani Maryam, Na san dalilin hawayenki. ba ki min laifin komai ba, Maryam kunyarki nake ji shi ne dalilin da ya sa nake kasa sakewa da ke". na ɗago kaina daga jikinta ina dubanta nace,"Mami wacce iriyar macuciyar kunya ce wannan da za ki bari ta kassarar da ƴarki? Mami ba zan yarda da wannan furucin naki ba, saboda haka kar ki yaudareni da batun cewar wai kunyata kike ji shi yasa kike yakice kanki daga gareni, ba don mu biyun da kika haifa duk ta dattin hanya kika samar damu ba, da sai na ce ba kya ƙaunata ne saboda kin haifeni a shegiya, amma tsakani da Allah meye banbancina da Alhassan da ni ba za ki iya bani soyayyarki da kulawarki ba?, ko kuma dan shi ya taso a cikin gata da daula ne, ni kuma na rayu cikin karkara, na rayu a ƙazantaccen wurin da kike ganin ba za ki iya tarayya dani ba, to bari kiji, wallahi summa tallahi ƙauyen bichi ya fiye min wannan daular masarautar taku sau dubu miliyan, ina ƙaunar bichi fiye da wannan ƙasar taku, nafi ganin kyanta akan wannan wajen da rashin rayuwata acikinsa ya hanani samun soyayyar uwata...ba komai Mami, na gode da iya amsawar ma da ki kai na cewar kin haifeni, Allah sarki Gwaggona, Allah ya jiƙanki da rahma ya haskaka ƙabarinki, na tabbata ko babu soyayyar wata uwa a gareni a duniyar nan, tunawa da iyaka tata da na samu ma kaɗai ta isheni nayi farin ciki muddin rayuwata, ballantana ina da Ummi, wacce ta sadaukar da jin daɗin rayuwarta dan ganin na rayu, ta hana kanta jin daɗi da walwalar duniya duk saboda kada na shiga damuwa ko da na sakan ɗaya".
sai kawai ita ma naga ta shiga zubar da hawaye daga idonta, kuma ta ke hankalina ya kai ƙololuwar tashi, hakan yasa na tsayar da maganganuna, na shiga kaɗa mata kaina da sauri ina kama fuskarta ina goge hawayen, sai ta kuma rungumeni muka shiga kukan tare, kukan da bana komai bane sai na huce takaicin da zuciyoyinmu ke ciki.
"ki yafe min Maryam". muryan Mamin ta fito a hankali, a hankalin da ya haifar da tsargawar jin wani tsananin tausayi da jinƙai na mahaifiyata. "ni ba ki min komai ba Mami, dan haka ki daina neman yafiyata, ni ce dai zan nemi yafiyarki, na kuma roƙeki da Allah nima ki sammin soyayyarki da kulawarki, ko da ace bai kai kwatankwacin yanda kike nunawa Alhassan ba". "Maryam kenan, ba ki san cewar nafi ƙaunarki akansa ba. ba za ki gane bane, you are still a baby, shi yasa gaba ɗaya kika kasa fahimtata, Maryam ina kunyarki ne idan na tuna ta irin hanyar da na samar da ke, amma kiyi haƙuri ki yafe min, nima bana jin daɗin yanda na ke mu'amalantarki, kuma daga yau na daina, insha'Allahu, zan nuna miki dukkan so da ƙauna da kulawa muddin rayuwata, ƙila ma har kice Mami wannan soyayyar ta fara isata, domin za ki dinga ganinki ne kamar jaririyar da ke shan nono...kin yafe min ɗin?".
ban san lokacin da wani murmushi ya suɓuce min ba, na kaɗa mata kai, sai ta ɗago da fuskata sama ta sumbace ni a goshina da kumatuna, kamin ta furta,"ina sonki Maryam, ina tsananin sonki". nima nace da ita,"nima ina sonki Mamina". ta kamo hannuna ta riƙe acikin nata, sannan murya a hankali tace,"idan kina cikin fushi ki daina magana kinji, ki dinga bari sai kin sauko, dan na lura ba kya iya controlling harshenki a duk san da kike cikin yanayi na ɓacin rai, kinga aure za ki yi, idan ni na ɗauka ba lallai mijin rufin asirinki ya ɗauka ba". sai na kaɗa kai nace,"zan kula insha'Allah". "yauwa Allah yay maki albarka".
shiru ya gimla a tsakaninmu na wasu ƴan sakanni, kafin tayi min tambayar da na iya amsa mata da ƙyar saboda kunya. "ba muyi maganar da Umminki ba, ai na Ahmad ɗin yace za ku zauna?, lagos ɗin ko kuma a kano?". "Lagos ɗin yace, idan ya sami hutu kuma sai muke zuwa kano". "hakanma yayi, to ya batun tsarin gidan ya faɗa miki?". na ƙara yin ƙasa da kaina cike da kunya nace,"ehh hoton yana wayata". "to sai ki turawa Daddynki, ɗazu yace yanata kiran wayarki zai tambayeki. duk da Umminki tace ita zata yi sayayyar komai. kin san Mai Martaba ya baku gida ma anan?". nayi saurin ɗago da kaina ina kallonta, kafin na girgiza kai nace,"a'a Mami". "ɗazu ya bawa Yayanki Almustapha key ɗin gidan, yace ya bawa Ahmad ɗin idan sun haɗu". na shafa gefen fuskata a hankali kamin nace,"Allah sarki Abi an gode Allah saka da alkhairi, Mami ki masa godiya". ta ɗan harareni da wasa kan tace,"tun da ni ce bakinki ko". sai kuma ta ƙara cewa,"me za kiyi yanzu?". na ɗaga kaina sama na kalla agogo sannan na sauke nace mata,"mu na da test har uku gobe, zan duba littafaina". ta gyaɗa kai,"to yayi, ai karatu da yawa. bari na ƙyaleki idan kin gama sai ki sameni a ɗakina, dama saboda ke na fasa komawa gida, dan haka daga yau har zuwa ranar da Umminki zata miƙa ki ɗakinki lokacina gaba ɗaya naki ne". murmushi kawai nake yi, na sakko akan gadon na dakatar da ita taga fitar da za tayi. "Mami ba ki sa sarƙar ba". da murmushin da bai bar fuskarta ba tace,"yanzun kuma za'a ara min kenan?". nasa hannu a fuskata cike da kunya sannan na kamo hannunta ta tsaya a gaban madubin, na ɗaura mata sarƙar sannan na ɗora haɓata saman kafaɗarta muna kallon juna ta cikin madubin, muna sakarwa juna ƙayataccen murmushi, tare da haskawar tsantsar soyayyar da muke yiwa juna a cikin ƙwayar idonmu. "kin yi kyau Mamina, kin haska sarƙar".
Alhassan ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya tsaya daga bakin ƙofar yana kallonmu cike da burgewa, ba mu juya gareshi ba, shi ma kuma bai yi magana ba sai da ya gama kallon namu sannan yace,"gwara dai ma kiyi auren ki tafi ki ƙyalemin Uwa". baki kawai na murguɗa masa bance komai ba, ya ƙwalo min biron da ke hannunsa na kauce ya sauka akan wuyan Mami, Mami tace da shi,"ya maka kyau Alhassan". "yi haƙuri Mami". tace,"ai ba wani abu bane, indai ƙwalowa mutum abu ne kar ka daina kaci gaba, zanyi maganinka wataran tun da kai baka san alkunya ba". yay dariya yana cewa,"yi haƙuri Hajiya Mami". "ka dai ci gaba kaji, garin jifan mutum da abu ka jefa ka sami Ubana, to nima kuwa da izinin Allah zan rama akan ubanka Major, ko da yake Allah ba azzalumin bawansa bane gashi yau da kanka ka rama min akaina, amma duk da haka ka sani sai dai idan ban sami abin jifa ba, sai na jefi goshin Major da shi yayi ƙwalele". ya rufe bakinsa yana dariya yana faɗin,"wa yaga goshin Dad yayi tsini". ta girgiza kai tana faɗin,"Allah ya gyara min kai, yanzu ya akai?". sai ya dubeni yana faɗin,"wai ke me ya sami wayarki?". nace,"me ka gani hala?". "Dad ne yace yanata kiranki tun ɗazu a kashe". sai na sa hannu na rufe baki na nufi wayar ina faɗin,"laaa wallah na manta na kashe sim ɗin, Na Yaya ne kawai a kunne". yaja tsaki kamin ya taɓe baki ya haɗa da faɗin,"to dai yace ki kira Ya Ahmad ɗin ki faɗa masa ya kawo masa result ɗin genotype ɗinsa". ban san dalili ba haka kawai naji allon ƙirjina ya girgiza, na ɗago na dube shi da sauyin yanayin da fuskata ya samu nace,"me za'ai da shi?". yace,"ki kira Dad ɗin ki tambaye shi tun da bani nake nema ba". daga haka yasa kai ya fita a ɗakin. Mami kuma tace,"dama tuntuni ba'ai wannan gwajin ba?". nayi shiru ban iya cewa komai ba, dan yanda naji jikina yay sanyi a lokaci ɗaya. sai ta fita tana faɗin,"to ki kira shi da sauri ki sanar masa kin san halin Daddynki sarai ba ya son delay". na ɗauke idona daga bayan ficewarta, na haɗiye wani abu a maƙogorona da ban san mene shi ba, kamin na iya neman wuri na zauna.
nasa finger print na buɗe wayar, kuma ta ke fuskata ta washe da annuri sakamakon cin karo da saƙon Ya Ahmad da nayi, wani taraddadi dann ji yana neman mazauni acikin zuciyata ya washe, na shiga karanta text ɗin nasa da haskawar hoton fuskarsa acikin idona.
_"I am in you and you in me, mutual in divine love. Saying it a thousand times won’t be enough to express my feelings towards you, but I’m going to keep saying it nevertheless- I love you! I will keep loving you till the end of my days, no matter what lays ahead of us Cutie nah, waiting and eager of the day, wannan ranar, a wannan daren da Ummi zata damƙa hannunki a nawa tace Diman Da'iman Ahmad..."._
sai na rungume wayar a saman ƙirjina na kifa kan gadon, na haɗe murfayen idona waje guda na lumshe, sannan naja leɓena na ƙasa na shigar da shi cikin bakina ina tsotsa da tarin murmushin da ya ƙi barin fuskata, ji nake ajikina tamkar Yaya nah na rungume ba wayar da ke ɗauke da saƙonsa ba. kuma ta ke hoton wannan ranar ya shiga haska min acikin idona, wannan daren ranar da Ya Ahmad ya buɗe min zuciyarsa, ya tona min sirrin da ke shimfiɗe a cikinta a game dani da soyayyata.
wannan daren da ya sameni da Al'ameen a parlo muna hira, saurayina da ya min proving soyayyansa a computer school ɗin da na shiga kafin na baro bichi, kuma a wannan daren ne zuwansa na farko gida da izinin Baba da Yagana, amma zuwan Ya Ahmad ya wurin ya tarwatsa zaman fahimtar junan da muke shirin yi ni da Al'ameen.
a gaban Yagana, gaban Ya Kabir, gaban Basma da Inna Zulai, gaban Ya Aminu da Baba, gaban Ummina, gaban kusan kowa na gidan. ya jawoni daga kan kujerar da na ke zaune gefen Al'ameen, ya tsayar da duga-dugaina a gabansa, dab da shi sosai, ya kama dukkan hannayena biyu ya ɗora saman ƙirjinsa, saitin zuciyarsa, wani abu da ya haifar da tasirin da na ji kamar zanyi fiffike na tashi sama.
wannan lokacin da nake a dab da gabansa, hannayena saman ƙirjinsa, sai nake jin zuciyata a lokacin kamar fayau ta ke babu komai acikinta, na kasa haɗa ido da kowa na kuma kasa kallon gefen da kowa yake, sai haɗiyar wani yawu nake a maƙogarona da ke wucewa da ƙyar, kafin daga bisani naji ƙafafuna na neman gaza ci gaba da ɗaukata, dalilin wannan harufa biyar da Ya Ahmad ya furta min.
_"Maryam za ki Aure ni?."_

*Plss Comment,Share&Vote.*

SIRRIN ƁOYE CompleteDove le storie prendono vita. Scoprilo ora