48

142 19 0
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

*(48)*
"menene?". tambayar tasa ta fito daga bakinsa kai tsaye zuwa cikin kunnuwanta, kuma yanayin yanda yay maganar ɗumin iskar bakinsa na fita ta sauka a wuyanta ya ƙara haifar mata da kasala. ta buɗe lumsassun idanunta ta zubesu akan hannunta da har yanzu ke kan ƙirjinsa riƙe da gaban rigarsa, wata uwar kunya ta lulluɓeta har tana neman nutsar da ita acikin ƙasa, yayin da bugun zuciyarta ya ƙaru wanda tana da yaƙinin yana iya jin sautinta dum-dum!. a hankali ta shiga ɗauke hannun nata akansa, shi kuwa yana lure da yanda hannayenta ke rawa kamar ana girgizasu. ya fahimta a tsorace ta ke, tsoron da shi kuma ba ya so yake ganinsa a tare da ita. sai kawai shima ya saketa ya matsa baya da ita yana kallon yanda hatta ƙafafuwanta rawa suke, hakan yasa yace da ita,"zauna". yanayin muryar tasa da ta fito fayau tasa tayi saurin ɗago kai ta dube shi, a lokacin har ya zauna kan kujera yana tattara wasu takardu da ke gabansa.
ta silale ƙafafuwanta zuwa ƙasa ta durƙushe akan carpet ɗin, har yanzu hannunta bai bar rawa ba, kuma tambayar da ya jefo mata ne yasa gaba ɗayanta girgiza a lokaci ɗaya. "kinyi wanka?". sai ta shiga girgiza masa kanta da ke ƙasa ba tare data amsa masa da baki ba. kuma a wannan karon da ya ƙara jefa mata tambayar taji yanda amon muryarsa ya sauya daga na ɗazu. "me yasa to ba kiyi ba?". tayi shiru ta kasa cewa komai, sai taji ya ƙara cewa. "daga wannan lokacin har zuwa gobe kar wadda ta ƙara sa ki aiki acikin gidan nan kika yi, kinji na faɗa maki, kuma duk yaron da naga kin ƙara goyawa abunda zanwa goyon yaron kaɗai zai sa ki shiga hankalinki...". sai tayi yunƙurin katse maganarsa da cewan,"ai...". bai bari ta ƙarasa ba shima ya tari numfashinta,"ai me? ke baiwar kowa ce?, ko su suka ɗauko ki aikin?". yanda yake maganar cikin ɗagawa sai ya tsoratata, bata san san da bakinta ya buɗe da ce masa,"a'a Ya Kabir duk ba haka bane". muryartata ta fito a karkarye. kallonta kawai yake yi kamin yaja tsaki ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihun wando. sai da ya zo saitinta sannan yace,"minti goma na ba ki kiyi wanka ki shirya". ta miƙe da azama zata bar ɗakin ƙwayar idanunsu ta gauraya, ya wurga mata wani wawan kallo da ya tsaida tafiyarta yace,"ina nufin ki shiga wannan toilet ɗin kiyi wanka". ta haɗiye wani guntun yawu sannan tace,"zan ɗauko kayana ne, kuma Innah zata nemeni zamu yi yankan albasa".
kai tsaye bakinsa ya fito da furucin,"ba zaki yi ba. ko ɗazu da nace kar ki ƙara aikin komai kunnenki a toshe yake?". tace,"a'a". bai ce komai ba ya juya zai fice yaji tana binsa a baya, bai tsaya daga tafiyar ba taji yace,"kar ki ja na sauke dukan fushina akanki...ina nufin kiyi wanka anan, ga kaya can a leda ki saka su, idan kin gama ki sameni a parlo". abin da yace kenan ya fice gaba ɗaya daga ɗakin cikin taku biyu. tabi bayansa da kallo tana haɗiye wani ƙullutun abu da bata san ko menene ba, wucewar sakanni uku ta ɗaga ƙafarta da take tunanin ta maƙale a wurin ta ƙarasa ta rufe ƙofar ɗakin, sannan ta juyo ta nufi inda toilet ɗin nasa yake ta buɗe ta shiga, bata da natsuwa sam, hakan yasa ta gaggauta yin wankan ta fito, ƙamshin shower gel ɗin da tayi wankan da shi ya baɗe ɗakin, hatta ita kanta lumshe ido take tana zuƙar ƙamshin saboda daɗinsa.
a ƙasa ta tsuguna ta jira har ruwan jikinta ya gama tsanewa gaba ɗaya, ta miƙe kenan sai gani tayi ƙofar ɗakin ta buɗe a lokaci guda, kuma ƙofar ta gaya mata wane tun kafin taga ƙafafuwansa da suka shigo a yanzu, ba tare da ta shirya ba sai jinta tayi a tsaye akan ƙafafunta duk a rikice, ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi.
sam bai lura da ita ba sai da yaje ya kwashi takardunsa ya dawo zai fita tukunna ya lura da ita a tsaye sai ƙudundune jiki ta ke yi, kallo ɗaya yaywa gashin da ya kwanto saman goshinta ya san zai iya cewa jikinta yaga ruwa, amma yanayinta sam bai yi kama da na wadda tayi wanka ba. dan yanda ya fita ya barta da kayan jikinta haka ya dawo ya sameta da kayan jikinta. kallon hannayenta da ke aikin rawa yake yana jin kamar ya kamo su ya riƙe acikin nasa har sai sun tsaya, to amma hakan da zai yi dai-dai yake da ƙara rikita yanayin tsoron da yake gani tare da ita, ƙwaƙwalwarsa na gaya masa cewa bayan ihun da yake ganin bakinta zai iya yi wannan siraran ƙafafun nata har kwasa da gudu ma za suyi su fita su bar ɗakin. kawai sai ya kaɗa kansa yace da ita,"har yanzu ba ki yi wankan ba?". kamar jira ta ke yay maganar da sauri kuma cikin saurin murya tace,"nayi tun ɗazu ma na fito, kayan da zan saka ne ban san inda suke ba". abin da tace ɗin ya fito tare da tsayawarsa a gabanta, wannan dunƙulallan abun da ke maƙogwaronta yaƙi wucewa a san da tayi ƙoƙarin kora shi da yawu. a yanzu da take jin saukar numfashinsa a jikinta ji take kamar zai ɗaga hannu ya duketa ne. dan haka bakinta yay saurin furta,"kayi haƙuri yanzu zan shirya". "why are you afraid of me?". bata iya kallonsa ba kuma bata iya ba shi amsa ba, alhalin taji me yace ɗin. "wannan wankan da ki kai sunansa wankan ƙazanta". ya miƙa hannunsa yana haska mata agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa yana ci gaba da cewa,"ko da saɓi ɗaya ki kaiwa jikinki bai ci ace kin fito a minti biyu ba balle har ki ƙara da cewar tun ɗazu kika fito". sai yasa hannu ya ɗago haɓarta,"ki nutsu Nawwara babu abin da zanyi miki, ba zan cutar da ke ba, ni ba mugu bane...kawai ina so ne naga kema kin zama kamar kowa ba yanda kowa ke son ganinki kina kai komon aiki ba...ki koma ki sake wannan wankan, akwai towel aciki ki ɗaura shi kar ki mayar da kayan jikinki dan wata dauɗar ce zata kuma hawa jikinki...idan ma ba za ki iya ɗaura nawa ba to akwai sabo daga ɗayar hanger ɗin yana nan ki saka shi". sai ya saki haɓar tata yay mata nuni da bakin gadonsa,"kayan da za kisa su na cikin waccan ledar, dan Allah Nawwara kar ki ɓata lokaci, jiranki nake yi, kuma nima jirana ake". sai tayi masa knooding kanta kawai, ya juya ya fita sannan ta koma toilet ɗin ta sake yin wani wankan, sai dai bata sako sabon towel ɗin ba kaman yanda yace, nasan ta saka ba tare da tasan me yasa zuciyarta ta sauya ra'ayi ba a san da zata saka sabon.
atamfa ce sky blue da kwalliyar flowers dark blue acikin ledar da ta buɗe, anyi ɗinki jiki da dark blue ɗin net less, daga atamfar har ɗinki sun bugu, tana iya tuna inda ta taɓa ganin irin atamfar da kuma kuɗinta da taji an ambata, ranar da su Ummi suka je store su kai sayayya, acikin kayan taga atamfar har Ummi tace ta bawa Sadiya ita a gudunmawar bikinta, atamfar na da tsada dan dubu ashirin taji Ummi na cewa Yagana ta siyo, har Yagana ke cewa ana almubazzaranci dai da kuɗi, ta ke ta mitar mene zai sa a sayo atamfa har ta wannan kuɗin, a sayo ta ƙasa da hakan ma sauran kuɗin kuma ai sadaƙa da su tunda an lissafa dole sai an kashe su.
sai ta ke ganin kamar zata yi kuskuren saka kayanne, wata ƙila yayi mantuwar nuna ma ta su ne, amma wannan kayan sunfi ƙarfinta, sun girmi matsayinta, ba ta kai ba, bata isa ta saka sutturar da ta kai waɗannan kuɗin ba, abunda ta sani shi ne kuɗin suttirarta ba ya wuce sama da dubu ɗaya da ɗari biyar, atamfa leda kenan ita ma kuma sai sallah ne Baba ke siya musu, amma yawancin kayanta kwance ne suke samu a ba su. saboda haka sai ta zaro mayafin ciki ta yafa shi akanta, duk da cewar ba wani babba bane amma yazo mata har kusan cikinta, ta ɗauki kayan ta riƙe ta nufi ƙofa ta fita, daga bakin ƙofar ta tsaya kanta a ƙasa, sannan ta buɗe baki, ta ɗan ɗaga muryarta yanda zai jiyota tace,"wanne ne kayan?". idonsa ya ɗauke daga kan tvn da ke manne a bango, ya juyo zuwa inda yaji sautin muryarta da tambayartata, idonsa ya fara sauka akan ƙafafunta da suka bayyana ta ƙasan towel ɗin, kafin ya maida ganin nasa ga kayan da take nuna masa. "ehh su ne". yana faɗin hakan ta juya ta koma, kayan kaman an auna da jikinta, dai-dai ita ciff.
tunaninta bana yadda zata fita gare shi a cikin kayan ba ne, ta yanda zata fita ta dinga ratsawa ta cikin mutanen gida su na ganinta. saboda haka sai ta yafa mayafin a kafaɗa, shi kuma ɗankwalin ta ɗora shi a saman kanta ta rufe fuskarta da shi, sannan ta fita daga ɗakin.
abun da ya bashi tabbacin fitowarta ƙamshin man da ta shafa, dan haka ya ɗago yana kallonta a inda ta ke tsaye daga bakin kujerar da ke kusa da shi. kamin ta silale ta duƙa ƙasa, wannan hannayen naci gaba da rawa kamar yanda suke yi tun a ɗazu, ba dukan fuskarta ya gani ba amma yasan tayi kyau, gefen leɓensa ya tale da murmushi sannan yace da ita. "ga abinci can kije ki zuba". "zan ci idan na koma ɗaki". shi ɗin kawai ta gani a gabanta san da tayi shiru da maganar, kafin tayi wani yunƙuri taji ya sunkoyo ya kamo hannunta guda ya ɗagota, sannan ya jata suka fara tafiya zuwa inda dining ɗinsa yake daga can baki-bakin ƙofar shigowa, Allah ya sani a wannan halin da take ciki babu abin da ta ke so tayi irin ta kurma ihu ta ambaci ta shiga tara, dan halin da yake sata aciki tun daga ɗazu zuwa yanzu yafi gaban ta shiga uku, ta lura ya kasa fahimtar cewar yana neman ya zautar da yanayinta musamman a yanzu da ya ƙara sa ɗaya hannunsa ya kamo ɗayan nata ta bayansa, ya damƙe a nasa hannun, kuma abin da ta fahimta so yake ya dakatar da duka hannayen nata daga rawar da suke yi.
"haka na cewa telan ɗinkin na ƴar siririya ne, siririyar fa irin firit ɗin nan, dan ƙafafunta yawo suke acikin zani duk san da tasa kaya, kaman yanda hannunta yake yawo acikin duk hannun rigar da tasa, tsayinta kuma gaba ɗaya a ƙasan ƙirjina yake saman cikina kenan. amma kar ka yi awon daidai da yanda ƙaƙafunta da hannunta zasu yi yawo a kayan, kayi daidai da yanda kayan zasu zauna ajikinta". abin da yake ce mata kenan lokacin da suka ƙaraso bakin dining ɗin, yace taja kujera ta zauna sannan ta zuba musu abincin. ta zuba abincin amma ta kasa ci sai tunanin maganar awon ɗinkin ta ke acikin kanta. "na bada awon dai-dai ko?". taji ya tambaya lokacin da ya kai spoon bakinsa, sai ta ɗago kanta a yanzu ta kalle shi sau ɗaya sannan ta maida kanta ƙasa. "ba ki ban amsa ba". "Ya Kabir amsar me?". "surutun da na gama yi miki a yanzu indai bai bi iska ba to akansa nake magana, in kuma yabi iska kici abincinki kawai". haka kawai maganar tasa yasa murmushi suɓucewa a fuskarta kafin tace da shi. "Ya Kabir to ai ban san wace siririyar ba". sai kawai taga shima yay murmushi yace,"ki ƙaddara a matsayin kece, kuma a cikin ɗinkin awon yanda aka bada". bata san lokacin da ta fara cin abinci ba tun daga lokacin nan da ya ce in maganarsa bata bi ta iska ba, dan haka a yanzu da ta haɗiye abincin da ke bakinta cikin jin kunya sai tace da shi,"ehh yayi daidai amma ni nafi waccan tsayi". so yake ta sake taci abincin dalilin da ya sa yake janta da zancen kenan. dan haka ya ƙara cewa,"kenan idan naki ne anyi kuskuren ba da awon kenan?, in aka kawo maki tsayinsu za su yi maki kaɗan?". kawai sai yaji tace,"aini Ya Kabir na taddoka a kafaɗa ita kuma kaga a cikinka kace". ya gyaɗa kansa har sau biyu san da ya kai kofin lemu bakinsa, bai sake cewa da ita komai ba sai da ya lura ta gama cin abincin tukunna ya miƙe yace ta tashi. "zan kwashe kwanukan...". wani kallo da yay mata shi ya dakatar da sauran furucinta, hakan yasa ta tura kujerar baya ta isko zuwa inda yake ta tsaya, kuma tsayuwarta kenan taji ya janyota ta tsaya ajikinsa. "banbance min wannan tsayuwar da maganarki ta ɗazu". a hankali ta buɗe idonta da ke rumtse, kafin ta kelleta gaba ɗayanta akan cikinsa. kuma maganarsa sai ta katse tunaninta jin yana cewa,"kin ƙara faɗa min kin kerewa kafaɗata ko sai na kai ki asibitin wanke ido". "na kere maka". ta faɗa a sanyaye tana murmushi, shi kuma yana sakinta a hankali ta bar jikin nasa, kafin yayi gaba ya barta a baya, san da ta ƙaraso bakin motar tasa har ta buɗe zata shiga baya cikin ɗagin murya yace da ita,"drivernki ne ni?". da sauri ta maida murfin motar ta rufe ta dawo gaba ta shiga, ta tsorata sosai da shi ɗin da yanda yay mata maganar, dan bata mantawa da kwanaki can kafin Yaya Maryam ta bar gidan ta taɓa yi masa irin hakan, kuma ƙiris ya rage ya kaiwa fuskarta mari tayi saurin kauce ma sa, shi yasa ko a yanzu da yace ma ta shi drivernta ne ta fuskanci me yake nufi.
da gudu yaja motar ya bar harabar gidan, mai gadi ya buɗe masa gate, ko gaisawa bai tsaya yi da mai gadin ba kamar yanda suka saba da shi a duk lokacin fitarsa, tun da ya hau titi magana bata shiga tsakaninsa da ita ba har suka baro bichi ya shigo kano, kuma har zuwa san da yay parking motar tasa a bakin *S. FARI BEAUTY PALACE, COURT ROAD*.
maganar da zata iya tunawa kawai ta shiga tsakaninsu awa ɗaya da suka ɗauka su na tafiya akan titi yace da ita,"kina jin yunwa?". kuma a wannan lokacin da yay tambayar girgiza masa kai kawai tayi alaman a'a, bai ɗauki a'a ɗin tata a yarda ba sai da ya tsaya a wani restaurant yay takeaway tukunna suka ci gaba da tafiya.
a yanzu da suke bakin wurin da ta lura wajen gyaran gashi da jiki da ƙunshi ne, waya taga ya ɗauko ya kira wata lamba kuma babu jimawa wata bayerabiyar budurwa ta fito, bata san maganar da su kai da ita ba tunda cikin harshen turanci ne, kafin budurwar ta juya ta koma ciki shi kuma ya juyo gareta yace da ita. "idan an gama ki kirani da wannan wayar". ya faɗa yana miƙa mata ƙaramar wayar da ke hannunsa, ta ɗago ido ta kalle shi kafin tasa hannu biyu ta amsa. sannan ya ƙara miƙo mata card ɗin da taji Ya Maryam na kiransa da ATM ya bata yace,"6915". sai da ya maimaita mata lambobin sau biyu kan ya ɗora mata da cewar,"lambobin sirrin banki ne. idan kika bari wani ya gani za ki ja a yasheni gaba ɗaya, kuma aka yasheni ke aka yashe".
"a dawo lafiya". shi ne furucin da tayi tasa ƙafa ta fita daga motar, ta rufo ƙofar taji ya kira sunanta,"Nawwara". hakan yasa ta dakata daga tafiyar ta leƙo ta glass ɗin tana amsawa,"na'am Ya Kabir". "ayi miki mai kyau, haka za ki ce da su, na faɗawa incharge ɗin wurin amma ki ƙara faɗa musu". tace,"to Ya Kabir, na gode". ta faɗa tana juyawa ta nufi inda ƙofar shagon ta ke, bai bar wurin ba sai da ya tabbatar da shigarta wurin har ya ƙara kiran matar ya tambayeta ta shigo tace masa ehh sannan ya baɗe wurin da ƙura.

*8:30pm.*
*more event center.*
daga irin yanda kake ganin zuƙa-zuƙan motocin da ke cike da harabar events ɗin har zuwa waje zaka san ehh fa lallai bikin na manya ne masu lokacinsu. sojoji da ƴan jarida zagaye da wurin, da yawa nada ga cikin hall ɗin zaune yayinda wasu kuma yanzu ne motocinsu ke parking wanda yawancinsu dangin amarya ne, alagaitar da ake busawa na shaida bikin na masu sarauta ne.
a wannan lokacinne jiniya ta ƙaraɗe ko'ina, a cikin wurin har daga can waje kan titi sakamakon motar Mahaifin amarya da ke shigowa. a yayin da motar amarya ke shigowa daga baya, Major ya fito daga cikin motar cikin dakakkiyar shaddar magic milk colour me cijawa, sannan matarsa Aaliya ma ta fito cikin wani haɗaɗɗan less ɗinta ita ma milk colour, ta zagayo inda mijinta yake suka jera suka nufa cikin hall ɗin sojoji uku na take masu baya. sai bayan shigarsu sannan Almustapha, Imam, Joseph da Alhassan wato yayyan amarya su ma suka fito cikin shaddarsu irinta mahaifinsu da su kai anko gaba ɗayansu, suma sannu a hankali suka rankaya zuwa cikin hall ɗin.

SIRRIN ƁOYE CompleteМесто, где живут истории. Откройте их для себя