47

175 22 10
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

_haba! Kabiro ba Kabir ba😝duk kun damemu da wani Kabir sai kace gwal🤨 yana fama da wani ƙaton kansa anan, mu muka ce yay dakon soyayyartata ko mu muka ce yay nauyin baki😏....#teamAhmad whre are guyz kuzo mu raƙashe a filin dinner💃💃Maryam da Ahmad za su tabbata abu guda, our dream has come true💃💃..._
*the whole page is dedicated to Ahmad's team.*

*(47)*
"me Kyauna kina irin zumuɗin da nake yi ne?". na juya ƙwayar idona sama kamin na dawo na saukesu kan hannuna ina kallon ƙunshin da yayta santinsu ajiya, muryata tayi ƙasa kafin ta fito a sirance nace da shi,"me ka gani Yaya?". daga inda yake naji saukar sautin murmushinsa, kuma na tabbatar kamin murmushin nasa sai da ya shafo kansa da ya sha haɗaɗɗan aski. "i heard that emotions in your voice, so tell me wanne irin shirin tarba kika min a daren gobe?". ban iya bawa Yaya amsa ba nayi saurin saka tafukan hannuna na rufe fuskata saboda kunya kaman ina gabansa. daga inda Ahmad yake ya saki wani ƙayataccen murmushi sannan yace,"hmm in dai wannan kunyar ce daga gobe dai ne zan cire ta". ban dai ce komai ɗin ba ya ɗora da,"ɗazun da safe before i hurt you who made you sad that you cried?". tambayar ta ɗauke nishaɗin da nake ciki na turɓune fuska, murya a kumbure nace da shi,"ba Jawad ba ne". na faɗa ina aikin harare kaman Jawad ɗin na gabana.
"me Kyauna wai Jawad sa'anki ne? please ban sanki da raina na gaba da ke ba wannan ba halin Autar Mami bane, ki bar kiransa da Jawad kai tsaye kinji...me yay maki?". "ni to ina ruwana da shi, ai shi ne yake fara takalata dan haka ba zan ce masa Yaya ba Jawad sunansa". nayi maganar har ina dukan ƙafa kaman ƙanƙanuwan yarinya. "bar ni da shi zan faɗa masa kar ya ƙara taɓa min Matata, her tears are very expensive ya daina zama silar zubarsu, if not kuma zan mance mu inlaws ne na rama maki ko Swty nah?". nayi murmushin da ya bayyanar da fararan haƙorana nace,"ai Yaya ko za kai inlaw da kowa kar ka yi da wannan, kirkinsa ragagge ne. ɗazun fa breakfast ena ya cinye kuma ya kama gashina yaja min da ƙarfi kawai dan nayi magana". kuma a inda Ahmad ɗin ke zaune sai ya ɓata rai,"ki faɗa masa ke matar aure ce, kar ya ƙara taɓa maki gashi mijinki ba ya son wannan wasan cousins ɗin kinji ni ko...ko after aurenmu ban yarda idan kinje gida kun haɗu da wani ba ki biye masa da wannan shashancin banzan, ni i don't take such kind of things as a joke, kin jini ko?". nayi saurin ɗaga masa kai,"naji Yaya and i will keep it insha'Allah". sai kuma naji voice ɗinsa yayi low a sanda yake cewa,"me kyauna ko dai Jawad bai haƙura da ke ba ne?, karfa ya zamana nayi shuka na gama ban ruwa someone else kuma yazo yaci amfanin gonar". maganar tasa ta haska min hoton abin da ya faru jiya a masarautar bichi da muka je. mahaifiyar Jawad Hajjah Nashwa, ana zazzaune a turakar Bella take cewa,"ni fa har yanzu banga ta inda Maryam ta dace da auren wani bare ba, shi yasa har da ya rage saura kwana biyu ɗaurin aurenta ni da ɗana bamu cire rai da ita ba". Anty Zaina tace,"hmm ai duk mai martaba ne da rashin yin dogon nazari har ya yanke wannan hukuncin, har ma da su Akilan ai. wai su na duba irin halaccin da mutanen su kayi masu, ina wani batun tuna halacci for God sake a inda ake son yarinya ta tsira da mutuncinta...duk wannan rawar jikin da suka ga yaron nayi akanta wallah wataran sai sunyi dakacan ina ma ba su ba shi ita ba. domin wuyarta ta ɓata masa rai zai fanshe ta hanyar tuna mata wacece ita, wallahi wataran sai ya tuna mata da wannan tabon da yake manne ajikinta, amma tsakani da Allah idan ɗan'uwanta ta aura fa, akwai wanda zai fishi ganin ƙimarta da mutuncinta ne?, aiko wani yaji ya goranta ma ta sai iyaka inda ƙarfinsa ya ƙare". kuma maganartata sai ta zama kamar ta fito da allura ne ta ɗinke bakunan kowa, dan babu wanda ya sake wata maganar. ni kuwa a wannan lokacin banda hawaye babu abinda nake, dakacen inama ba'a haifeni ba nake, fata nake dama ace mutuwa tazo ta ɗaukeni a yanzu ba sai anjima ba, tun da maganar auren nan ta kama babu abin da nake facing sai ƙalubalen da ya shafi maganar asalina, hatta a dangin su Ya Ahmad ɗin ma akwai wadda tace min,"Maryam ki bar ganin zuri'arku kuna da dukiya da sarauta, kuma kema naji ance mahaifiyarki da mahaifinki sun mallaka maki kadarori da dukiyar da za'a iya saka ki a sahun farko na masu kuɗin ƙasarku, to ki sani da waɗannan kaɗai ba ki isa kifi Amadu ba, dan na lura kun siye mana shi ne da kuɗi ko kuma barazanar Yayanki zai iya korarshi daga aiki, banda haka babu ta inda kika dace da shi domin shi yafi ki da abu ɗayan da zai shafe duk wani abu da kuke gadara da shi, Maryam Ahmad ya fiki tsarkakken asali ki tuna da wannan, da tsarkakken asalinsa kaɗai duniya ma zata fi ganin nasa girma da komai ɗin da kuke tutiya da shi".
a lokacin da Umma Sahura take faɗa min waɗannan maganganun ji nayi kaman naje na sami Ummi nace mata na fasa wannan auren, to amma kuma sai na tuna farin cikin Ummina, ko ba komai ina so na sakawa Ummina da irin sadaukar da farin cikinta da tayi akan ganin na rayu. na kai hannu na toshe kunnena da ke min amsa kuwar wasu ƙananun maganganu da naji a san da nasa ƙafata zan shiga ɗakin su Jamila naji ƴan'uwan Inna Zulai nayi, hawaye ne kawai ke sauko min, kuma a lokacin kawai sai zuciyata da ni kaina muka tsinci kanmu a matuƙar son ganin Ya Kabir, a wannan yanayin da nake ciki wanda kaina ke daf da tarwatsewa babu hannun wanda nake so na jini, babu kusa da wanda nake so na jini sai Ya Kabir. to me yasa shima nake nemansa a wannan lokacin?, idan na gansa me zai yi min da zai wanke baƙin cikin da nake ciki?. ko kuma dan na sami labarin cewar wata a dangin su Baba ta shegantani yasa ƙafarsa yay fatali da ita ya tattaketa?, na tambayi kaina yafi sau cikin masaki dalilin da yasa Kabir zai yiwa wadda ta ke ƙanwace wurin mahaifinsa haka? ya manta girman mace ne?, ban ankare ba kawai naji ƙafafuna na ɗauka na su na tafiyar dani zuwa sashensa, sai da na ɗora ƙafata akan steps na entrance shiga parlonsa sannan tunanina ya ankar da ni inda nake neman kai kaina, wurin Kabir, wannan Kabir ɗin da a duniyarsa ta yanzu babu wadda yaƙi jini sama da ni, kar fa na manta ya tsaneni, shi da kansa ya furta min na rabu da shi, kenan da nazo nan ƙara na kawo masa ko me?, after all nasan da cewan a yanzu shi yafi kowa ƙyamatata, illegitimate ta ɓata kyakykyawar alaƙar da ke tsakaninmu, shin na manta ne da cewar na yiwa kaina alƙawarin ko a lahira ni da Kabir?, to ayanzu da nazo wurinsa dan huce takaici ai babu abin da zan samu face wani baƙin cikin da ya fi wanda kowa ke sani aciki, dan na tabbata Kabir zai iya wankeni da muggan kalamai akan ciwon shegantani da su Mami su kai. "Yaya kin manta Ya Kabir ɗin ba ya nan". maganar da Basma tayi kenan a bayana, ba tare da na bari ta fuskanci halin da nake ciki ba na bar wurin da sassarfa, na fita daga gidan na hau motar haya na nufi airpot, wanda sai bayan naje can ɗin tukunna na kira Ummi nake faɗa mata.
tabbas zuciyata ta karanta min yafi sau adadin lissafi cewar Maryam ba za ki taɓa auren soyayya ba, balle har ki zama cikin farin ciki, saboda wannan ciwon har abada ba zai bar zuciyarki ba, dan haka asirinki alaikum ki auri Jawad kawai, shi ne wanda ko da ya goranta maki kansa ya gorantawa. bana son Jawad dan haka me yasa zan aure shi?, ai har gwara ma wannan mutumin da Ummi ta ban labari, shi naji ɗarsuwar sonsa a raina, kuma shi ko da ya walaƙantani rantsuwar Allah ce zata ci shi, tun da ya rantsewa Ummi da Allah zai tsaya min, zai gusar da dattin baƙin cikin shegiya daga zuciyata, haka zai goge tabon ciwon shegiya da ke tare da ni, duk da nasan cewar wannan soki burutsin soyayya ne kawai, amma shima ba zai so samawa Ƴaƴansa uwa marar asali ba.
"zuwa yaushe za ku taho?". maganar Ya Ahmad ta katse dukkan tunanina, cikin sanyin muryata nace da shi,"Daddy ake jira ya dawo, mu mun gama shiryawa". "a jirgi ɗaya za ku taho?". na ɗaga kai da faɗin,"ehh". "to ki kula min da kanki kinji". na amsa da,"insha'Allah, kaima ka kula min da kanka". daga haka wayar tamu ta ƙare. wayar da ban iya saukewa ba daga kunnena ba kenan, haka kawai hoton Jawad ke haskawa acikin kaina da idanuwana. san da Mai Martaba(kakansu Mami) yace na ba shi zoben azurfar hannuna, na maƙe kafaɗa nace da shi,"a'a wannan ba naka ba ne". da ya tambayeni na wane sai na kalla Jawad da ke hakimce akan kujerar Mai martaban, fuskarsa da tsananin damuwa, kallonmu kawai yake ba tare da ya saki fuskarsa ba, ina murmushi nace da Me Martaba,"wannan zoben daga hannuna sai hannun My Jawad". nayi maganar da sigar zolaya, furucin nawa ya haifar da tasirin tsoro a gareni, dan cikin sauri ya waro ƙwayar idonsa da suka ƙanƙance ya saukesu akaina, kamin ƙiftwar idona sai tsintar Jawad nayi agabana, ya damƙo hannuna yana matsawa yace,"dan Allah Maryam ƙara faɗa". na cuno baki nace da shi,"me?". ya rumtse ido ya juyar da kai sannan ya dawo da kallonsa kaina yace,"sunan da kika faɗawa Me Martaba kamin ya fita". na karyar da kai na ɗan harare shi sannan nace,"au wai My Jawad?". sai kawai naga ya ɗaga kansa sama ya cije leɓensa na ƙasa yana wani irin smiling, sannan ya sauke kan nasa yana cewa,"ashe duk pretending kike dama kina sona?". na kanne ido nace da shi,"kawai dan nace My Jawad sai ka fassara shi da abinda yake zuciyarka. to dama ai dole na so ka tunda kai ɗan'uwana ne, kuma dan nace My Jawad har wani abune dama?". "Jawad ɗinki fa kika ce". na sake cewa,"to a matsayinka na Yayana kai ba nawa bane...kaga tsaya! na fahimci dai jingina kalmar My ga sunan mutum ta ƙunshi tarin ma'anonin da yawa, dan haka zan kiyaye gaba". kuma irin kallon da yake min acikin ƙwayar idanuwansa yasa sauran maganata ta maƙale a maƙogwarona, cikin wani irin mood mai wuyar a fassara shi. sai kawai nayi ƙasa da kaina na taka zan wuce ta kusa da shi sai naji ya riƙo hannuna ya dawo dani gabansa, cikin wata iriyar murya da ban taɓa jinsa da ita ba yace,"ina sonki Maryam, wallahi ina sonki, kuma burina ki zama abokiyar rayuwata na har abada, Maryam Jawad mai ƙaunarki ne, ya fara sonki tun a ranar da ya fara ɗora idanunsa akanki cikin wannan tsiwar rashin kunyar ta ki, kawai nayi shiru ne a lokacin saboda kinyi yarinta da yawa, kin min ƙanƙanta, idan nace zanyi soyayya da ke za ki dinƙa cin karo da abubuwan da suka fi ƙarfin kanki, please Baby doll kice ni za ki aura ba wancan Ahmad ɗin ba da bai ko iya soyayyar ba, kizo gareni na nuna maki soyayya da...". ban bari ya ƙarasa ba kawai na ture shi daga matsoni jikinsa da yay na fice daga turakar mai martaban, ina jiyo shi yana fitar da wani makirin murmushi mai ƙarfin sauti. kuma ban ƙara ganinsa ba sai yau da safe a dining, wai saukarsa kenan daga ƙasar moroco ya biyo ta nan saboda yasan idan ya wuce ethiopia ba lallai ya sami damar zuwa bikin ba, shi ne ya shigo a yunwace yana zuwa ya afkawa abincina da muke ci a plate ɗaya ni da Bro Almustapha. na kama ƙunƙuni ya fizgoni gabansa ya damƙe gashina wai bari ya yanke gashin da wani gaja can ya gani ya liƙewa, ai yasan komai, Ahmad ba sona yake ba haskena da gashina yake so, Bro Almustapha ya ƙwaceni na bishi da harara ina murguɗa masa baki nace,"oho dai ba zan dai ce ina sonka ba".
nasa hannu na share hawayen da ke sauko min cikin azama, tunawa da maganar Mami da nayi a ranar da ta tsuguna min tana roƙona da girman Allah kar na kuma zubar da hawaye akan asalina, in har da gaske ne na yafe mata to karna ƙara kuka akan yanda aka haifeni, kuma na ɗaukar mata wannan alƙawarin. don haka na bar tunanin koma na zuro ƙafafuna ƙasa daga kan gadon, dai-dai shigowar Shamsiyya da suka fita tun a ɗazu, tayi turus daga inda take tana cewa,"kambu wai sai yanzu ku ka gama wayar?". ban amsata ba, nayi ma ta harar wasa ina ɗaura towel ajikina. ta taɓe baki tana cewa,"in yayi haƙuri dai gobe za'a kai masa...kuma ke Allah kiyi sauri ki shirya dan ga Daddy can ya dawo, naga ma har driver ya fita kai kaya airpot". na nufi hanyar toilet ina cewa da ita,"dan Allah ki ɗauko min underwear a ɗakin Mami". "to". sai kuma ta ƙara cewa,"dama ba ki taho da allon saukarki da certificate ba?". (da yake cikin wata ukun da nayi a qatar bayan larabcin da na koya har da alqur'ani muka sauke). "Mantawa nayi Shamsiyya, kaina duk ya cunkushe amma zan kira Alhassan in zasu taho ya ɗauko min". "to wannan gift ɗin da Madam Deborah ta ba ki na haɗa da shi acikin wannan ƙaramar trolly ɗin ko da za ki nema. tunda nasan kai tsaye gidanki za'a kai kayan, kuma zan iya mantawa ban maki bayanin inda na saka maki wasu abubuwan ba". "to Shamsiyya sannu da ƙoƙari. kiyi sauri kema ki shirya kar Anty Samiha ta haɗa faɗan har da ke...ina Aisha Tayo?". tana saka wasu kaya cikin trolly ɗinta tace,"to ai kayan fa su Anty Iftihal ne suka tafi dasu, Aisha ta bisu. dagani sai ke sai Mami da Ummi muka rage. dan Daddy ma naga kaman tafiyarmu ba tare ba". na buɗe ƙofar toilet ɗin ina cewa,"ƙila ko sai ya jira su Uncle Lucas sun zo, wannan bataliyar christian ɗin ba son zuwansu nake ba...ke nifa gaba ɗaya mantawa na ke daga zuri'ar arna na fito". na faɗa da sigar mita da jin haushi, na bar Shamsiyya da dariya tana faɗin,"kuma kin san Ummi tace rigar da Granny Chioma ta ba ki za ki saka a dinner ba". nako ce,"tabɗijam Allah tsaren dasa kayan arna wallah, ko mai zasu ce sai dai su faɗa". daga haka na faɗa toilet na barta da ƙyalƙyala ƴar iskar dariyarta mai cin rai.

SIRRIN ƁOYE CompleteWhere stories live. Discover now