32

166 26 8
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

_Shafin Gaba Ɗaya Sadaukarwa Ne Ga Masu Sharing Wannan Book Ɗin, Alkhairin Allah ya isa gareku._

*32)*
dukkan wata ma'ana ta tashin hankalin ta gaba fitowa ajikina, a yau ɗaya rayuwata ta sauya, tabbas idan aka tambayeni tarihin rayuwata da wannan shafin zan fara, ta kansa zan soma. yanayin da nake ciki da ni da wanda aka tsamo daga cikin teku bamu da maraba a wajen jiƙewa illa shi ruwa ne ya jiƙa shi, ni kuma zufa ce ta jiƙani sharkaf. tun da na daki kaina da bango naji zafin a jikina na tabbatar da abun da kunnuwana suka ji ba'a mafarki bane, zahiri ne. na koma kamar wadda aka sassaƙa aka dasa a ƙofar ɗakin Baba, babu motsi sai numfashin da shi ma na ke zuƙo shi da ƙyar, idanuna sun kaɗa sunyi jajur. murfayen idanuna su ka haɗe su ka rufe su na fatan daga haka shikenan ba za su ƙara buɗewa ba su gansu a wannan duniyar ba.
hoton rayuwata gaba ɗaya ya shiga haskawa cikin idona, yayin da agefe ɗaya maganar Kulu ke ci gaba da shiga cikin kunnuwana.
"Malam in har dai wannan Sojan da ƙasa ke ji da shi ne Major Tosin Afafa to wallah ba zan maka ƙarya ba shi ne mahaifinta, Malam shi ya yaudareni da cewar zai musulunta bayan ya gama dasa soyayyarsa a zuciyata at long last yazo ya yaudareni yaci amanata yay min ciki, a gabansa na haifesu, akan idonsa, da shi aka karɓi haihuwarsu, amma saboda zalunci bayan zuwansu duniya yace ba zai iya karɓarsu ba. shi ne har ya ɗaukesu wai zai kai gidan marayu suyi rayuwarsu a can gudun kar sunansa ya ɓaci, jin hakan yasa na ƙanƙame Hussaina da ke hannuna dan Hassan na hannunsa a lokacin, nace idan ya rabani da namijin ba zai rabani da macen ba, ba zai yiwu duka su tashi a tutar kafirci ba, bai bi ta kaina ba, balle ya tausayawa halin da nake ciki yasa ƙafa ya wuce ya barni. shi ne har ku ka zo ku ka sameni a  wannan asibitin, Malam Hauwa ba shi ne sunana ba Akila shi ne asalin sunana, ni ba ƴar nigeria bace ƴar ƙasar Qatar ce, mahaifina shi ne sarkin ƙasar.
yanzu ban san ya zanyi ba, ban san da wani irin kalami zan faɗawa Hussaina ta yarda cewar bada son raina na haifesu ta wannan hanyar ba".
kukan da ya ci ƙarfinta yay dai-dai da ɗaukewar wuta a zuciyata, sai kuma wasu hawaye na daban masu zafi suka shiga sauko min, kukan da ke riƙe a bakina ya suɓuce, bakina kawai naji yana furta,"Ya Allah kabi min hakkina akan Akila da Tosin, ba zan taɓa yafe musu ba, dan sun cutar da ni...Allah ka ɗauki raina na huta da rayuwa ma gaba ɗaya, karka bari na ƙara kwana a duniyar nan dan zan iya ɗaukar...". maganar ta katse daga bakina dalilin toshe min baki da Ya Kabiru yay, wanda ban san da zuwansa ba sai ganinsa nayi tsugune a gabana.
"me yay zafi haka?, Mairo rashin uwa ai ba hauka bane. dan kawai kin rasa mahaifiyarki sai hankalinki ya nemi ya gushe, har ta kai kina furta kalaman da za su fidda ke a addininki, haba karki raunana imaninki mana. ƴaƴa dubu nawa ne suka rasa mahaifiyarsu, ni ma fa kaina bani da mahafiyar nan a raye...". sai yay shiru a san da Baba da Kulu suka fito daga ɗakin, jikinsu a sanyaye, ta gefen idon na ke kallonsu. ya miƙe tsaye daga gabana, ni kuma Baba ya kira sunana,"Mairo". ban amsa ba sai jan hanci da nayi. "Mairo tashi muje daga ɗakin Gwaggonki". nace da shi,"Baba ka kirani da sunana na ainihi mana. domin Mairo ta mutu, Mairo ta mutu tun daƙiƙu kaɗan da suka shuɗe, yanzu Hussaina ce a gabanka".
har yanzu fuskarsa na nuna bayyananniyar ɗumbin damuwa yace,"Mairo bata mutu ba, da Mairo da Hussaina duk ɗaya ne". "a'a Baba ba ɗaya bane, Mairo da ubanta, ba shegiya bace. Hussaina kuwa bata da uba, ƴar gaba da fatiha ce, shegiya ce, sai da akayi zina sannan aka sameta". kowa yay shiru ya kasa cewa komai, illa sheƙar kukana da na Kulu ko kuma nace Akila ke tashi. na buɗe murfayen idanuwana sosai na kalleta, kallon da zan iya kiransa da na dole, domin ko kaɗan bana ƙaunar sakata a cikin iɗanuwana saboda na tsaneta. kuka ta ke sosai ba don ta tsoshe bakinta da ɗan kwali ba babu abin da zai hana sautinsa fita. na rufe ido na buɗe sannan na lashi leɓena na ƙasa, zuwa wannan lokacin kam idanuwana sun bushe, zuciyata ta ƙeƙashe, nayi gutun murmushi me cike da tarin ma'anoni da yawa sannan na buɗi baki na kira sunanta."Akila". yanayin yanda sautin muryata ta fito kaɗai ya isa ya shaida maka ba kiran kirki bane, sunanta kawai na kira, amma kamar har da Baba da Ya Kabiru na kira, domin duk idanuwansu suka sauke shi a kaina, sai ta ɗago da sauri ta dubeni, nace da ita,"ki nemi wuri ki zauna yanda za ki yi kukan da kyau, yanzu ba komai kike ba hawayenki ɗaya yake da dariya a wurina. ki bari in hukuncin abin da kika aikata ya biyo baya sai kiyi me dalili, dan wallahi tallahi Akila sai na ɗau fansar rayuwata akanki". Ya Kabiru ya ɗaga min murya da cewar,"ke kina hauka ne". maganarsa ta fito a dai-dai lokacin da ƴan gidanmu su ka fara sallamar shigowa ɗaya bayan ɗaya, ban dubi kowa ba, ban kuma bi ta kan kowa ba dan duk bata tasu nake ba. na buɗi baki zan kuma magana Ya Kabiru ya sake buga min tsawa,"karki ƙara cewa komai a wurin nan, ki wuce ki tafi ɗaki...". nima nai saurin dakatar da sauran maganarsa ta hanyar ɗaga masa hannu da cewar,"dakata Kabiru, magana ake ta rayuwata da kuma asalina, so don't interfere". sai kuma na juyo a fusace na fuskance shi ina nuna masa yatsa,"idan kuma kaƙi ji, to ina me tabbatar maka da hukuncin kisan da nake ƙoƙarinyi zai dawo kanka, dan a yanzu zuciyata na azalzalata ne na kasheta, idan har ita bata ji tausayina ba ta biyewa son zuciyarta ta aikata zina sannan ta haifeni, to nima ba zanji tausayinta ba dan na ɗauki kowanne irin makami na daɓa ma ta a ƙahoton zuciya ta shura". muryar Baba ta fita da kalmar,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil". kalamai biyun da yake ta maimaitawa kenan a bakinsa, yayin da a gefe guda Inna Amarya da Inna Zulai ke aikin tambayar me ke faruwa. nasa hannu na ture Inna Amarya daga gabana na ƙarasa gaban Akila na tsaya, da yatsa ɗaya na ɗago fuskarta da ke duƙe tana kwaranyar hawaye. "wallah kin cuceni, kuma Allah ya isa tsakanina da ke, dan kin nakasta rayuwata, me nayi miki da har kika zaɓi ki haifeni ta wannan ƙazantacciyar hanyar?". na ƙarasa faɗa ina damƙar ƙirjinta,"wallahi tallahi ba zan taɓa yafe miki ba, sai na saka ki kuka fiye da wanda zanyi, sai na sakaki baƙinciki fiye da wanda kika saka ni a cikinsa, sai na zama ni ce ajalinki dan baƙin cikin abinda zan aiwatar ne zai sa zuciyarki ta kumbura ta fashe. a cikin daƙiƙa biyu da kunnuwana suka gama jin asalin labarin rayuwata daga gareki, a rabin daƙiƙa ƙwaƙwalwata ta gama lissafi da tsarin yanda zan ɗauki fansata akanki da Major, kuma a rabin minti zuciyarta ta zartar hukuncin kisa akanku, to amma cikin shigar sabuwar daƙiƙa lissafi da tsarin komai ya sauya, naga kasheku ba shi ne mafita ba, idan na kasheku ba shi ne zai sa na sami sauƙin zafi da raɗaɗin da ku ka dasa a zuciyata ba, ba shi zai hanani jin baƙin cikin rayuwata ba. in sakaku kuka fiye da yanda kuka sani shi ne kaɗai zai sa na sami ƴar salama daga ƙuncin da ku ka jefani aciki, a ƙalla ko ba komai za ku ƙarasa rayuwarku cikin dawwamammen baƙin ciki. Akila za ki ce na faɗa miki, ki aje hakan a ɓangaren tunaninki... wallahi ba za kiyi danasanin samar da ni ta hanyar fasiƙancin da ki kai ba sai na ɗauki mataki akanku tukunna, zan je na sami shi abokin dadiron naki, zan tabbatar masa da cewar ni ƴarsa ce da ya haifa a waje yay watsi da rayuwarta saboda yana so ya tsira da mutuncinsa, bayan yaji wannan zan tilasta masa na tursasa shi ya kwanta da ni ya aikata irin abin da ya aikata da ke, zai mu'amalantu da ni ne yana kuka yayin da nawa hawayen suke a ƙyafe. da zarar buƙatata ta biya zan wuce na nemi ɗan'una na shaida masa ni wace ɗinsa, na kamo hannunsa na kawo shi har gabanki, shi ma ya tursasaki ya aikata the same abin da muka aikata ni da major... kukan da zanga kina yi a wannan lokacin shi ne burina, duk da na san hakan ba shi zai wanke min dattin baƙin cikin da ke zuciyata ba, amma kuma ko banza na dasa muku baƙincikin da ba zai taɓa bari ku ji daɗin rayuwa ba...in Allah ya yarda ba za ku zubar da hawayen ruwa ba hawayen jini za ku yi ta zubarwa".
ta riƙe hannuna ta ɗauke daga kan ƙirjinta, dan ni kaina ina jiyo yanda ƙirjinta ke harbawa tamkar zuciyarta zata faso waje, murya a cikin kuka tace,"ko ba komai ni mahaifiyarki ce, ki tuna wannan a mahanga ta addininki...". ban bari ta ƙarasa ba na shaƙi wuyanta lokaci ɗaya ta kama kakari,"bari na ƙarasaki tun yanzu, ke har kina da bakin da za kiyi min nasiha, ki gama jin daɗin iskancin naki sannan kizo kice za ki min nasiha, gaba ɗaya ba ki fi ƙarfin na kiraki da karu...". sauran maganata ta katse, jina da ganina suka ɗauke na wucin gadi, cikin sakannin da ba su haura ɗaya ba na haɗa hankalina da tunanina na dawo cikinsu, sannan na buɗe idanuwana tangararau suka bar ganin ƙyallin wutar da ta haska a cikinsu, duk ta dalilin azababban marukan da Ya Kabiru ya bani ta duka ɓangaren fuskata, da kuma wanda Ya Amadu ya dawo min da shi bayan ɗaukewar na Ya Kabiru, sai na gigice gaba ɗaya na rasa makama, sai dafe kuncin nawa nayi da nake jin kamar wata jijiya acikinsa na neman tsinkewa.
"Ya Amadu har sau nawa za'a dukeni ka hanani yin kuka,? mene laifina a ciki dan na kira matar da ta lalata min rayuwa da sunan karuwa, yanzu shikenan kowa zai tsananeni, kowa zai koma kirana da shegiya..kuma wallahi ba zan janye ƙudurina akanta ba ko da me za'a min, sai dai in Allah ne ya ɗau raina, kuma na faɗa ɗin Karuwa, ai idan batayi karuwancin ba zata samar da ni ta ƙazamar hanya ba". ƙaton kutufo ya kuma sauka a bakina, halshe da haƙorina suka haɗe wuri ɗaya, jini ya shiga zuba. na ɗago ido na kalli Ya Kabiru, huci yake da jajayen idanuwansa da suka sauya launi su ka rikiɗe zuwa na wata halitta a cikin halittar dabbobi. da kakkausar murya ya ke faɗa min,"billahillazi la'ila ha'illahuwa idan bakinki ya ƙara furta wata magana anan wurin sai na sa ƙafa na mitstsikeki dan ubanki, shashasha mahaukaciya....Amadu saketa". kallonsa kawai na ke da mamaki nace,"dole kace nayi shiru tun da kai igoyoyin uku na aure ne suka samar da kai, ba zaka ji irin zafin da ni nake ji ba, shi yasa ba zaka damu ba, to wallah a yau banga me hanani magantuwa ba duk faɗin duniyar nan". maganar na ke ci gaba da faɗa a san da tuni yasa ƙafa ya fyaɗeni na zube ƙasa, kan yasa hannu ya jani kamar wanda ke jan wasu kaya har zuwa zaure, ya buɗe ɗakinsu me uban duhu babu wutar nepa, ya jefani a ciki sannan yasa mukulli ya rufe.
duk kururuwar da nake akan ya buɗeni na fita ɗaukar fansa amma sam yaƙi, illa ma buɗewa da yay ya dawo ciki ya ɗaureni da igiyar shanyar da ya ciro. nabi bayansa da ido ina kallon yanda yake goge ƙwallarsa. amma ban fasa jaddada masa ba, sai dai idan bana numfashi ne kaɗai zuciyata zata ƙi aiwatar da ƙudurinta akan Akila da Tosin, insha'Allahu sai nasa sun zubar da hawaye fiye da wanda nake yi, wannan alƙawarina ne, kuma nasan wace zuciyata ba zata taɓa rissina akan hakan ba.
daga can zaure na jiyo Yagana ta shigo gidan tana faɗin,"ai wallahi tunda Adawiyya taje tace min wai Mairo tayi shaye-shaye tana ta wasu surutai marasa kan gado nasan zai yi wuya idan ba SIRRIN ƁOYE ne ya fito fili ba. oh oh na shiga uku ni Rakiya, a garin ya hakan ta faru?, wa ya sanar da ita cewar ita shegiya ce duk wannan rufa-rufar da muka dinga yi, kai munafiki bai ji daɗin halinsa ba, dole sai da aka samu wanda ya faɗawa yarinyar nan ita ƴar zina ce, to Allah ya isar ma ta, ke kuma ki bar kuka muje ɗaki...ina Mairon ta ke?".
"shegiya kuma Ƴar zina!". kalmomin suka ƙara maimaituwa a cikin kunnena, "Akila kin cuceni". na fada tare da kifa kaina akan gwiwoyina ina fashewa da matsanancin kuka. duk bidirin da ake tsakanin Yagana da Ya Kabiru akan ya fito da ni ina jinsu.

*Plss Comment&Share.*

SIRRIN ƁOYE CompleteWhere stories live. Discover now