24

168 21 2
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

_The Pages Completely Goes To duk wani makaranci littafin sirrin ɓoye, na gaisheku, ina kuma yi muku Son So fisabilillah...masu text messages da kirana a waya su na yaba min, ku sani ina jin daɗi kuma ina godiya a gareku._

*24)*
*Kano, Bichi.*
wata takwas! watanni takwas kenan rabonsu da saka Mairo a idonsu, Mairon da tun su na saka rai da dawowarta har sun haƙura sun fawwalawa Allah.
zata dawo garesu? ba zata dawo ba? tana raye ko ta mutu? Allah ne masani. anyi neman, anyi cigiyar amma shiru, sai adu'a da ba za su daina yinta ba, ba za su taɓa mantawa da ita ba, tarihinta ba zai taɓa gogewa a garesu ba, diman da'iman, ɓatanta shi ne tashin hankali na farko da suka fara cin karo da shi a rayuwa, ko mizani ba zai iya auna alhinin da suke ciki ba na game da rashinta a tare da su.
_zuciya sirrin me shi take, ko ka kasa kunnuwa ba zaka jiyo komai ba._
_shi ko SO kamar iska ya ke, ko ka tara hannuwa ba zaka taɓo komai ba._
_ni da ke kamar Laila Majnun muke, ko da mutuwa tazo ba zata ɗau ɗaya ta bar ɗaya ba._
waƙar da ke tashi kenan ta cikin ƴar ƙaramar radion da ke aje kusa da turken awakin Yagana. Yaganar da ke daga cikin turken awakin tana ba su abinci tace, "kiwa Allah ki kashe wannan radion ko kuma ki sauya tasha ki kai inda suke wa'azi, haba abu babu daɗin sauraro tun ɗazu waƙar ke hawar min kai wallahi, na miki alamar da za ki gane kinƙi, da yake ke ƙwaƙwalwar taki cunkus ce".
"A'a fa Yagana, ba zai yiwu na zo gidanki ina taimaka miki da aiki ba kuma ki hanani shaƙatawa, ina dalili...ke ba kin san sirrin da ke cikin waƙar bane da ba ki ce na kashe ba, idan na kashe ma aikin ai ba zan iya ba".
Adawiyya wacce ke zaune kan kujera tana tankaɗen garin masara ta faɗa.
"yo ni ina ruwana da sirrin da ke cikinta...da kike kallona haka har yanzu jimamin rashin Mairo ƴar albarka bai barni ba ƙarfin hali kawai nake, saboda haka ki kasheta kawai ko wallahi idan na fito nabi ta kanta tunda ba tawa bace".
Adawiyya ta kyaɓe baki ta shiga ƙunƙuni sannan ta kashe radion, domin tasan sarai Yagana zata iya fasa radion sai dai idan bata fito ba.
taja dogon tsakin takaici, yo ai ita zata iya rantsewa ma ta manta da batun wata Mairo, dan anata ɓangaren sam ɓatan Mairo bai tada hankalinta ba balle ya dameta, ai ko lokacin da suka dawo daga makaranta su ka sami labarin ɓacewarta da za'a buɗa zuciyarta za aga kaf duniya tafi kowa farinciki, murna da tsananin farin cikin da ta shiga a lokacin Allah yayi yawa da su. tun yaushe Mairon ta zame mata alaƙaƙai, ta jima da hawar mata kai tana neman hanyar da zata ɓarar da ita, cikin sauƙi sai gashi Allah ya dubeta ya dubi kukanta shi da kansa ya kawo mata ɗoki, kuma insha'Allahu tana fatan har duniya ta naɗe Mairo dai ba za'a ganta ba, ko da za'a ganta kuwa sai dai aga gawarta.
"Hmmm". tayi wani murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa, to ai ko alawar da aka ga tana siya tana rabawa yara sadaƙa da tata manufar tayi, kuma ko da Inna Amarya ta shigo ɗaki ta sameta tana aljanu duk na ƙarya ne, rawar jin daɗi take a sa'ilin kawai sai taji an ɗaga labule shi ne ta zarce da aljanun ƙaryar.
Ƙaya! ai idan anji ana batun Ƙaya ɗaya ma kenan, ai Mairo ƙaya ce a gareta, tun ranar farko da ta fara ganin Suhail taji ya mata, ya shiga zuciyarta yayi bake-bake, tana sonsa, tana sonsa da manufa ta aure. amma daga ba ya sai ta fahimci Suhail Mairo yake so, Mairo ce a zuciyarsa, ko ba'a faɗa ba ta sani, masarautar bichi ta ɗauki tallafin karatunsu ne saboda Mairo, saboda da ta sami gogewar ilimin boko ta yanda a gaba zata iya shiga cikin zuri'arsu. shi yasa tun a ranar da suka dawo daga masarautar bichi taji ta tsani Mairo, ba Uba ɗaya ba, ko da ace ciki guda suka fito to ta tsaneta, ita ce ta dace da Suhail ba Mairo ba, ko san da ta fita a sabgarta tayi hakanne dan Mairon ta fahimta amma da ike ƙwaƙwalwar kifi gareta ta kasa gane komai, har take wani kuka a gabanta tana neman afuwar abin da tayi mata, a lokacin ji take kamar ta shaƙeta ta mutu, sai taga wa Suhail ɗin zai aura, ai sai dai su duka su rasa, ta rasa me ya sami idon Suhail ɗin ma, da me Mairon ta fita da har ita ya kasa ganinta ya ƙyasa?, sai wata Mairo da yake ta rawar ƙafar ingantawa rayuwa, Mace ƙirji kamar ɗan malele, baya duk a shafe.
sau biyu tana yin mafarkin Suhail ya auri Mairo, hauka ne kawai bai kamata ba, shi yasa ta ƙudurta ɗaukan mataki, matakin da take ganin zai kai ta ga Nasara. tabbas duk duniya Uwar da ta tsuguna ta haifeka ita kaɗai ce me sonka, ita kaɗai ce me ganin ta share maka hawaye, ita kaɗaice me yin duk yanda za tai wajen ganin ta rabaka da damuwa, a yanzu ta sani, ashe a ba ya shirme take da ta biyewa su Gwaggo a ganinta su ne zuciyarsu me kyau, ashe ƴarsu Annoba zata zame mata. dalilin da yasa tayi hankali kenan ta sanar da Innarta komai.
babu kwane-kwane ta sanarwa da Mahaifiyarta matsalarta, ai dama Innar ta taɓa tambayarta dalilin da ya sa kwana biyu take ganinta kamar ba'a hayyacinta ba, amma sai tace mata babu komai, Innar kuma bata ƙara bi ta kanta ba saboda tasan dama bata faɗa mata matsalarta sai dai taje can ta faɗawa Gwaggo.
a sanda ta sanar da Innar, tayi dariya tace,"ai bari ba shegiya bace tana da ubanta, yanzu kinji uwar bari kenan". tayi narai-narai da fuska ta kamo hannun Innar, ta soma hawaye tana faɗin,"Allah Inna da gaske nake ina sonsa, kuma wallahi idan ya auri Mairo zan iya kashe kaina, dan zuciyata ba zata juri ganinsu tare ba...Inna ni ina faɗa miki ma yanzu na tsani Mairo dan ashe tuni gonata take shiga ban sani ba, wallahi da nasan hanyar da zanbi na kawar da ita Allah sai nabi". kuka take sosai a san da tayi maganar.
Innar ta tsaya tana dubanta tsawon lokaci, Adawiyya ta san wace mahaifiyarta, dole zata nema musu mafita. Innar ta saki murmushi me cike da tarin ma'anoni tace,"ke ni fa ba shashashar uwa bace da zan zuba ido Mairo ta auri jinin sarauta, nawa Ƴaƴan kuma su ƙare a auren ɗan ƙauye gidan manomi. saboda haka ki share hawayenki ki bar kuka, asiri gaskiya ne, dan haka in dai akwai boka a duniya Yaron nan sai ya bar kan Mairo ya dawo kanki, in ba haka ba kuwa to ya zo da batun auren nata sai ta aure shin na gani, ai sai dai idan bana numfashi, ko kuma ke da ita ɗin duk ku rasa. ba Mairo kaɗai ba har Uwarta wallahi sai sun shiga tsumin wahala, kamar yanda na aika Hajiya lahira to suma tasu rayuwar a tafin hannuna take, ƙiris na ke jira, kuma lokaci yayi, nayi alƙawarin ko zanyi yawo tsirara sai nasa Rayuwar Mairo ta ƙare a tangaliliya.
can dama kece mara wayon, kin nane a gindinsu kina nuna min Uwarta ita ce me ƙaunarki bani dana haifeki ba, na sha faɗa miki ba ƙaunarki suke ba amma yarinyar sai kika yi sautin mahaukaciya da ni, to ai gashi nan ta nemawa ƴartata miji me ido da kwalli ke za su barki a gidan ɗan dako. to wallahi ko da ace ba kya sonsa ba zan bari aurenta da shi ya tabbata ba". Adawiyyan ta kuma fashewa da kuka,"ni dai Inna kiyi duk yanda za ki ki tarwatsa sonta daga zuciyarsa, dan wallahi a yanda na gama fahimtarsa aurenta yake so yayi, ranar ma fa da suka kwana agidan nan ina jinsa yana cewa da Ƙaninsa yaga Matar aure a gidan nan, to na rantse miki da Allah Inna in har baki nema min mafita ba zan kashe kaina, kisa Suhail ya bar kanta ya dawo kaina". Zulai ta kuma dafa kanta, tai ƙasa da murya tana ce mata,"ke na fa ce miki ki bar zubar da hawayenki a banza a wofi, zan tabbatar miki da Suhail ke zai aura ba waccan abar kamar sillan kara ba, yanayin jikinki shi ya dace da gidan hutu, matar manya, na faɗa in dai da boka to hawayenki daga yau ya daina zuba. Suhail zai dawo sonki kuma zai aureki, sannan zan yi amfani da basirata da hikimata wajen ganin na tarwats...". bata ida abun da zata faɗa ba Amadu ya ɗaga labulen ɗakin ya shigo, hakan yasa su kai shiru aka ɗora da wani babin zancen na cewar Kanta ke ciwo, saboda Amadu ya tambayi dalilin kukan nata.
kuma da suka dawo ɗin, Innar tata ta bata labarin bayan tafiyarsu makaranta ko wata biyu ba'a shafe ba Suhail yazo da kansa har ƙofar gida yasa ai masa sallama da ita Adawiyyar, an kuma shaida masa ɓatan Mairo amma ko jaje bai shigo yaywa Uwarta ba, tun da akace masa ai kina makaranta ya koma mota ya bar unguwar.
tayi dariya ta rungumo Uwar tace,"ai yaje har makarantar ya sameni, wallahi Inna a ranar ji nayi kamar nayi hauka don daɗi, ya shaida min yana sona, kuma da zarar na kammala makaranta zai aureni...Inna ranar ban iya bacci ba, yace saboda ni fa ya baro ƙasar Ethopia a lokacin da bai shirya hakan ba, saboda yadda idanuwansa ke masa zugi da zafin son su yi tozali dani".
tunanin Adawiyya ya yanke lokacin da Maganar Yagana ta shiga kunnenta. "ke zan leƙa gidan Hajiya Fatsima, yanzu zan dawo. idan kin gama tankaɗen garin sai ki tafi da shi can gida ki bawa Aisha, kice musu Mujibu ne ya siyo gari yace ai sadaƙar kunu da shi ranar juma'a". ta amsa mata da,"to". Yaganar kuma ta fice, ita kuma ta ɗauki aniyar Garin Kunun nan sai dai ayi asararsa, so take yanda ta manta da duniyar Mairo kowa ma ya manta da ita, dan haka ba zata bari ai sadaƙar nan ba, taga nema su ke su jaza mata bala'i Allah ya amsa adu'arsu ya dawo da Mairo, bayan ta gama sawa a ranta Mairo ta tafi kenan tafiya kuma ta har abada.
a ɓangaren Gwaggo kuwa tun wannan rana da Mairo ta ɓata ta ke a kwance babu lafiya har yau, ciwon hawan jini, kullum kuma ƙara hawa yake ba ya sauka saboda yawan tunanin halin da Mairo ta ke ciki, ta rame sosai sai kace ba Gwaggo da ke da jikin diri ba, wuyan nan nata ya zama dogo, kuma tun daga wannan rana har iyau bata kuma takawa da ƙafafunta ba, ciwon da ya tsorata Malam ya kuma ɗaga hankalinsa, ciwon ƙafar tata tamkar aikin asiri, dan bata iya komai da kanta sai dai ayi mata.

SIRRIN ƁOYE CompleteWhere stories live. Discover now